Cin Hanci Da Rashawa Na Matukar Bunkasa A Aikin Gwamnati – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashawa na bunkasa a aikin gwamnati saboda son kai da siyasa da kuma rashin gaskiya.

Buhari ya bayyana hakan ne yau Juma’a lokacin bikin mika lambobin yabo kan kwarewar aiki a fadarsa da ke Abuja.

Shugaban ya bukaci ma’aikatan gwamnati da kuma mutane da ke kan madafun iko da su tabbatar da cewa sun kauracewa harkar rashawa saboda a san da su a matsayin wadanda suka kawo wa aikin gwamnati ci gaba.

Buhari ya bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan lambobin yabo kan kwarewar aiki da kuma wasu fitattun ‘yan kasar 43.

Ya ce ya kamata shugabanni a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu su san cewa an daura musu hakki ne, inda ya bukace su da yin aiki na kwarai ako da yaushe domin barin tarihi da za a ci gaba da tunawa da shi.

Ya kuma ce idan ba a karfafa hukumomin shari’a ba ta yadda za su hukunta wadanda suka ci rashawa a aikin gwamnati, to abu mai wahala ne kawo karshen rashawa a tsarin aikin gwamnati.

Labarai Makamanta