Cin Hanci Da Rashawa Na Haifar Da Koma Baya A Kasa – Imam Abdul-Ganiyyu

Dafa Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

An Bayyana Cin Hanci da Rashawa A Matsayin Babban abinda ya jefa Nigeria Halin da Take Ciki a Yanzun.

Sheikh Abdulwahid Abdulganiyyu
Limamin Juma’a na Jabi Daki Biyu dake Abuja Shine ya bayyana hakan a Hudubarsa ta Sallar Juma’a da ya Jagoranta.

Imam Abdulwahid Abdulganiyyu Yaace Cin Hanci da Rashawa Babban laifine a Cikin Addinin Musulunci inda yace Ma’ anar cin Hanci Da Rashawa shine, Cin Dukiyar Mutane ba tare da son Ransu ba.

Ya bada Misali da Yadda ake dakile Masu neman aiki A Gurabe Daban Daban koda Kuwa sun Can-Canci Gurbin Aikin indai Basu Bada cin Hanci ba.

Yace Wannan Yana Faruwane a kowanne Bangare na ma’aikatun Gwamnati da Masu Zaman kansu.

Yace wani babban abin bacin rai shine yadda Cin Hanci da Rashawa ya mamaye Bagaren Sharia ta yadda ake amfani da cin Hanci don baiwa mara gaskiya gaskiya.

Ya tabbatar da cewa yaki da cin hanci da Gwamnati keyi yayi daidai da Umarnin Addinin Musulunci na hani akan cin Hanci da Rashawa inda Allah yayi Tsinuwa akan masu bayarwa da masu karbar Rashawa.

Sannan ya tabbatar da Cin Hanci da Rashawa shine babban Karshin Bayan Tabarbarewar Dukkan Al’amura na kasa.

Ya Kuma Buga Da yadda Direbobi ke kinyin Katin Shaidar Tuki Sakamakon Karbar Nagoro da akeyi a wajensu Maimakon a Tilasta musu Bin Ka’ida.

Daga karshe yace Babbar hanyar maganin Hana Cin Hanci da Rashwa Itace Jin Tsoron Allah Da Kuma Bin Umarnin Manzon Allah SAW.

Labarai Makamanta