Wata babbar kotun birnin tarayya, Abuja ta bayar da umarnin aike wa da dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris da wasu mutane uku zuwa gidan yari na Kuje bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.5.
Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Olusegun Akindele, Mohammed Usman da Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.
Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da su a gaban kuliya, bisa tuhume-tuhume 14 da ake zargi da karkatar da Naira biliyan 109.5.
Mai shari’a O. Adeyemi Ajayi ta bayar da umarnin ne bayan gabatar da dukkan lauyoyin da ke cikin shari’ar.
Ta kuma bada umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da aka neman beli.
Ta ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin sauraren roƙon neman beli.
You must log in to post a comment.