Cin Amanar Ƙasa: Ka Yi Gaggawar Hukunta Duk Waɗanda Suka Aikata- PDP Ga Buhari

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa maganar shugaba Buhari ta tabbatar da abinda ta dade tana fada cewa akwai barayin dukiyar talakawa a Jam’iyar APC.

Ta kuma kara da cewa gwamnati na baiwa wadannan barayi kariya ta yadda ba a iya hukunta su.

Saidai PDP ta ce tana kira ga shugaban kasar da ya yi himma wajen hukunta wadannan maciya amanar.

Sakataren watsa labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce a baya PDP ta samar da hukumomin yaki da rashawa da cin hanci kuma ta hukunta wadanda aka kama da laifi.

Labarai Makamanta