Cimar Doya Ta Gagari Talaka A Jihar Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar farashin doya ya yi tashin gwauron zabo lamarin da a yanzu sayen doya ke neman gagarar talaka.

Wakilimu da ya leka babbar kasuwar ‘yan Doya dake Kaduna ya samu zantawa da wasu daga cikin Dillalan Doyar, inda suka bayyana yadda farashin ya yi mummunan tashi sama a cikin shekara guda.

Malam Bala mai Doya ɗaya ne daga cikin Dillalan Doyar dake kasuwar, ya bayyana cewar a halin yanzu kwaryar Doya wadda a baya suke saye akan farashin kudi naira dubu 40 a yanzu abin ya canza inda kwaryar Doya a yanzu take kai wa har Naira dubu 150.

Dillalan Doyar sun bayyana cewar matsalar ta samo asali ne sakamakon fitinar ‘yan bindiga waɗanda suke addabar Manoman doya da Dillalai dake shiga sayen Doya a Jihohin Neja da yankin Uduwa dake karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

“A magana ta gaskiya a yanzu doya ta fi karfin talaka, lamarin ya kai ga wani hali na Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un”.

Labarai Makamanta