Ci Rani Kasar Waje: Sanusi Ya Shawarci Matasa

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu, ya yi kira ga matasan Najeriya da su daina barin kasar nan domin neman dama a kasashen waje, a matsayin ‘yan ci rani.

An ruwaito cewa Sanusi ya yi wannan kira ne ga matasan yayin da yake jawabi a ranar Lahadi a wani taron wasan kwaikwayo mai taken ‘A Truth in Time’ a Birnin tarayya.

Taron wanda ya naqalto rayuwa da gogewar tsohon sarkin, Ahmed Yerima, farfesa ne na fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer, ya rubuta shi, wanda Duke of Shomolu Productions ya shirya.

A cewar tsohon sarkin akwai bukatar matasa a fadin kasar nan su fara bunkasa fasaharsu a nan cikin gida ba tare da damuwa wajen fita waje ba.

Ya kuma bukaci matasa a Najeriya da su yi kokarin ganin sun yi wa shugabanni da masu rike da mukaman gwamnati jan ido wajen tabbatarwa sun yi aikin da aka daura musu.

“Gare ku matasa, kada ku ji tsoro. Wannan ita ce kasarku. Wannar ita ce makomarku. Ku rike ta. Ku yi aiki don ita. Ku gina ta. Kada ku bari kowa ya ce ku gudu saboda kuna da digiri.”

Labarai Makamanta