Chadi: Ɗan Marigayi Idriss Deby Ya Zama Sabon Shugaban Kasa

An naɗa Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙo a kasar Chadi.

Matakin ya biyo bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby a yau Talata sakamakon raunukan da ya ji a kusa da kan iyakar Chadi da Libya inda ‘yan tawaye ke bore.

Shugaban na riko na da shekaru 37 a duniya kuma Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi.

A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi “ya ja numfashinsa na ƙarshe a yayin da yake kare martabar ƙasar a fagen daga”.

Janar Mahamat Idriss Deby Itno

Majalisar ƙoli ta soji za ta jagoranci ƙasar har na tsawon wata 18 karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby

Mista Déby ya ɗare mulkin ƙasar ne tun a shekarar 1990.

A ƙarshen mako ne ya je fagen daga don kai wa dakarun da ke yaƙi da ƴan tawaye ziyara a kusa da kan iyakar Libiya.

Deby ya rasu ne yayin da yake kan hanyar lashe zaɓe wa’adi na shida sakamakon zaɓen da aka gudanar ranar 11 ga watan Afrilu.

Labarai Makamanta