Nazari: Dalilan Da Suka Haifar Da Mace-Mace A Kano – El Bash

Akwai Matsalar Tsanantar Talauci A Tsakanin Al’umma, Sannan Jama’a Su Na Fama Da Rashin Lafiya Da Rashin Samun Damar Zuwa Ganin Likita, Haka Zalika Hankalin Likitoci Da Gwamnati Ya Karkata Kan Yaƙi Da (CORONAVIRUS). -Akwai Buƙatar Gwamnati Ta Ƙara Ƙoƙari Ƙan Ƙoƙarin Da Ta Ke Yi, Ta Samar Da Motocin Jigilar Marasa Lafiya Ta Kuma Yafewa Marasa Lafiya Kuɗin Neman Lafiyar A Dukkan Asibitoci Mallakinta. Yau Asabar, 25 Ga Watan Afril, 2020. A wannan hali da ake ciki al’ummar Jihar Kano da ma ƙasa gabaɗaya su na cikin zullumi da…

Karanta...

Bauchi: Hadarin Mota Ya Lashe Rayukan Mata Biyar

Hadarin Mota A Hanyar Bauchi Ya Halaka Mata Biyar Da Yaro Daya Yadda hadarin yammacin jiya Asabar 04/ April/2020 ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida, mata biyar da karamin yaro tsakanin garin Zalau da Gumau dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi. Abdulkareem direba Zalau (Hogan) wanda yake a asibiti yanzu haka tare da wasu da suka jikkata. Hadarin ya yi muni matuka domin har da kananan yara wani ya sami karaya a kafada wani a kafa. Allah ya yi musu rahama ya sa aljnna ta zama makoma ya kyautata…

Karanta...

Mune Matsalar Kannywood – Adam Zango

Shahararren jarumin masana’antar Kannywood kuma mawaki, Adam Zango, ya bayyana silar rikicin da ke addabar masana’antar Kannywood. Ya zargi yaranshi da kuma yaran jarumi Ali Nuhu da rura wutar rikicin da taki ci taki cinyewa a masana’antar ta Kannywood. A wata tattaunawar da jarumin ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, ya bayyana irin rikicin da yaransa tare da yaran jarumi Ali Nuhu ke haifarwa a masana’antar Kannywood. Inda kuma ya kara da cewa babu shakka hakan laifin jarumi Ali Nuhu ne. Kamar yadda jarumin ya ce, da…

Karanta...

Saura Kiris Najeriya Ta Fara Fitar Da Shinkafa Waje – Dangote

Kamfanin Dangote na Duniya, ya yi alkawari cewa labarin Najeriya zai tashi daga matsayin kasa mai shigo da shinkafa zuwa kasar da ke fita da shinkafa zuwa kasashen Duniya kwanan nan. Kamar yadda Daily Nigerian ta yi rahoto, Dangote ya sha alwashin ganin Najeriya ta daina dogara da kasashen ketare wajen abincin ta. Kamfanin ya bayyana wannan ne ta bakin Kunt Ulvmoen. Mista Kunt Ulvmoen, wanda shi ne babban Darektan Kamfanin ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da aka yi da ‘yan kasuwa a ranar musamman da…

Karanta...

Bambancin Almajirai Da Mabarata – Al-Mansour Hussein

Ga dukkan alamu kaso mafi yawa na al’ummar mu, basa banbance kalmar almajiri da kuma mabarata, wadannan kalmomi guda biyu kalmomi ne mabanbanta da juna, sai dai sukan hadu a wasu bangarori duba da yadda muke kallon su a zamanin mu. Kalmar almajiri asalinta daga kalmar larabci ce ma’ana Almuhajirالمهاجر (The immigrant), sahihiyar ma’anarta mu a wajan mu shine wanda ya bar gida zuwa wani gari ko tsangaya neman karatun Alqur’ani, sannan kuma daga cikin bukatun wanda ya je neman karatun alqur’ani ba wai ya haddace ne kadai ba, yana…

Karanta...

Yadda Yari Ya Talauta Zamfarawa Da Bashi

Tsohon gwamnan jahar Abdulaziz Yari Abubakar ya bar bashin bashin N251, 951,849,482.50 ga sabuwar Gwamnatin, Gwamna Mohammed Bello Matawallen-Maradun. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin karbar mulki, Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad. Lokacin da kwamitinsa ya ke ganawa da manema Labarai a fadar Gwamnatin jahar Zamfara Da ke Gusau. Shugaban kwamitin ya bayyana cewa gwamnati Mai Ci a yanzu ta kafa wannan kwamitin ne. Domin gano iya adadin basukka Da gwamnatin Da ta shude ta Bari, Kafin Mika ragamar mulki ga wannan Gwamnatin. Wannan rahoton na biyar rahoton…

Karanta...