Zan Bi Diddigin Kisan Da Aka Yi Wa Ɗalibin Jami’a A Kano – Pantami

Ministan harkokin sadarwa na ƙasa Sheikh Dakta Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai bi bahasin yadda wani ɗan sanda ya hallaka matashin mai suna Mus’ab Sammani a birnin Kano sakamakon wata ƴar taƙaddama da ta faru tsakanin matashin da wani mai tuƙa babur ɗin adaidaita sahu. Sheikh Pantami ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, in da ya sha alwashin zai bi kadin binciken yadda lamarin ya faru har sai gaskiya ta yi halinta. “A ƙashin kai na ni Isa Ali Pantami zan bi bahasin wannan al’amari har…

Read More

DSS Sun Ƙara Kama Soware

Jami’an tsaro na SSS sun yi wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja shigar-kutse, sun sake kama Omoyele Sowore, kwana daya bayan sun sake shi. Al’amarin ya faru yau Juma’a da safe, inda SSS suka yi kokarin shiga kotun domin su kama Sawore da karfin tsiya Da yake kuma su Sowore na da masaniyar haka, sai lauyoyin sa da abokan arziki suka ki fita da shi waje, suka yi zaman su a kotun. Sowore ya je kotu ne tare da lauyoyin sa, kwana daya bayan sakin sa da Mai Shari’a Ijeoma…

Read More

Hukumar DSS Ta Saki Soware

Hukumar tsaro na SSS ta saki mawallafin Jaridar Sahara Reporters dake tsare a hannun ta a bisa umarnin kotu. Baya ga haka kuma hukumar ta biya shi Naira 100,000 kamar yadda kotu ta umurce ta. Idan ba a manta ba Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci jami’an SSS su saki Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore cikin awoyi 24. Yayin da ta ke yanke hukunci a yau Alhamis, Ijeoma ta ce haramun ne Sowore ya kara ko da kwana daya a hannun SSS. Sannan…

Read More

Ku Saki Sowore Nan Da Awa 24 Umarnin Kotu Ga DSS

Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci jami’an SSS su saki Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore cikin awoyi 24. Yayin da ta ke yanke hukunci a yau Alhamis, Ijeoma ta ce haramun ne Sowore ya kara ko da kwana daya a hannun SSS. Sannan ta ce shi ma wanda ake tuhumar su tare, mai suna Olawale Bakare a sake shi ba tare da bata lokaci ba. Ba a nan ta tsaya ba. Mai Shari’a ta kuma umarci SSS su biya Sowore naira 100,000. An…

Read More

Rikicin ‘Yan Shi’a: Kotu Ta Bada Umarnin Cigaba Da Tsare Zakzaky

Yau ne kotun jihar Kaduna ta ci gaba da sauraron shari’ar dake gudana tsakanin Gwamnati da Zakzaky wanda ake tuhuman shi da aikata manyan laifuka, tun bayan abinda yafaru a watan Disambar 2015 tsakanin Shi’a da rundunar sojojin Najeriya. Zama na karshe da aka yi a farkon shekarar nan wanda kotu ta bada umurnin abar Zakzaky ya tafi kasar waje neman lafiya, wanda daga bisani Zakzaky ya koka akan rashin samun walwala kamar yadda ya ke samu a Najeriya, inda Madugun ‘Yan Shi’an yaki amincewa da tsarin da hukumar DSS…

Read More

Tsaro: An Bada Belin Maman Boko Haram Akan Milyan 30

Wata babban kotun jiha da ke zamanta a Maiduguri a ranar Laraba ta bayar da belin Barrista Aisha Alkali Wakili da aka fi sani da Mama Boko Haram da wasu mutane uku kan tuhumar da ake musu na damfarar kudi har naira miliyan 62. Mai shari’a Aisha Kumalia ta bayar da belin Wakil a kan kudi naira miliyan 30 tare da mutane biyu da za su tsaya mata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Alkalin ta yi gargadin cewa muddin wadanda ake zargin suka ki gurfana a kotu yayin shari’ar…

Read More

Uwargidan Buratai Ta Bada Tallafin Abinci Ga Mabukata A Kaduna

Uwargidan Shugaban Dakarun sojin Najeriya Hajiya Ummu Kulsum Buratai a madadin Shugabar Ƙungiyar Matan manyan sojoji ta Najeriya, ta bayar da gudunmawar Kayayyakin abincin na Buhunan Shinkafa da Masara da Gero da Dawa kimanin 786 ga masu karamin karfi a Kaduna. Sauran kayayyakin sun hada da Taliyar zamani garin fulawa, Garin Sabulu da man gyada da Manja da zannuwa. Da take bada tallafin ga mabukata a sassa daban daban na Kaduna, uwargidan Buratai din ta ce wannan gudummawa da suka bayar yana wani bangaren ne na aikin kungiyar Matan manyan…

Read More

Kawar Da Zakzaky Da Gardawansa Nasara Ce Ga Rundunar Soji – El Rufa’i

An yaba gami da jinjinawa rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban dakarun rundunar na kawar ‘yan ta’adda da ta’addanci a tarayyar Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ne ya yi wannan yabon lokacin da yake jawabi a matsayin shi na mai masaukin baƙi a babban taron rundunar sojin Najeriya da ke gudana a Kaduna a yau din nan. El Rufa’i ya cigaba da cewar, bai yiyuwa ayi magana akan nasarar rundunar sojin Najeriya ba tare da an ambato kokarin da rundunar ta yi…

Read More

Katsina: Matashi Ya Hallaka Ɗan Sanda Da Al-Makashi

An gurfanar da wani matashi mai suna Yusuf Lawal, dan shekaru 22, a gaban babbar kotun Majestare ta Katsina, bisa zarginsa da hallaka kofurar din dan sanda mai suna Musa Isiyaku har lahira da almakashi, a yayin da dan sandan ya je kamo shi. Kofurar Musa Isyaku mai shekaru 30, dan sanda ne dake aiki a carji ofis din yan sanda na cikin garin Malunfashi, ya gamu da ajalin nasa a ranar 5, 2019, a No 22 Layin Yanbori kwatas cikin garin Malumfashi, Majiyarmu ta Punch ta rawaito cewa Yusuf…

Read More

Tsaro: Buhari Ya Bayar Da Umarnin Ɗaukar ‘Yan Sanda 400,000

Ma’aikatar kula da harkokin da suka shafi rundunar ‘yan sanda ta ce ta samu umarnin gaggawa daga fadar shugaban kasa a kan ta dauki sabbin ‘yan sanda 400,000 domin magance karancin da jami’an tsaro keda shi. Da yake sanar da hakan ranar Litinin, shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar, Odutayo Oluseyi, ya bayyana cewa tuni ministan ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda ya kafa kwamitin mutane 13 domin fitar da tsarin yadda za a dauki karin sabbin jami’an. Umarnin fadar shugaban kasar ya kawo karshen tababar da ake yi…

Read More

Dakarun Soji Sun Yi Nasarar Ceto Mutane 20 Daga Boko Haram

Ƙungiyar ta’adda ta Boko Haram ta Ƙaddamar da hari akan Garin Babban Gida Hedikwatar Karamar Hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe a Makon da ya gabata. A cikin sanarwar da Daraktan yada labarai na rundunar sojin Kasar Aminu Iliyasu ya fitar ya bayyana cewar, ‘yan ta’addan sun kai hari a yankin wanda ke zaune lafiya a wani yunkurin su na mayar da hannun agogo baya ga rundunar soji, da kuma jefa tsoro a zukatan jama’ar garin. ‘Yan Boko Haram din sun sace Kayayyakin abincin jama’ar garin da kuma kama wasu…

Read More

Kogi: ‘Yan Fashi A Shigar ‘Yan Bautar Kasa Sun Budewa ‘Yan Kwallon Kafa Wuta

Kungiyar kwallon kafa ta ifeanyi Ubah ta tabbatar da cewa an kaiwa motar kungiyar su hari a hanyar su ta zuwa jihar kano daga kogi.kungiyar ta taso ne domin zuwa garin kano inda zasu fafata da jigawa golden stars a wasa na 6 da ake fafatawa a gasar primiyar Najeriya. ” Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar jumm’a a daidai kabba junction dake lokoja babban birnin jihar kogi inda wasu ‘yan ta’adda sanye da kayan masu yiwa kasa hidima (NYSC) suka far wa motar kungiyar inda…

Read More

Garkuwa Da Mutane: Majalisa Ta Amince Da Hukunci Mai Tsanani

A karshe dai Majalisar Dattawan kasar nan ta yi wa dokokin laifuffuka garambawul inda ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane a Najeriya. Kamar yadda mu ka samu labari, Majalisar ta kawo kudirin daurin rai ne ga masu sace jama’a, domin maye gurbin dokar da ake amfani da ita a halin yanzu wanda ta yanke daurin shekaru 10. Sanata Oluremi Tinubu mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa ta gabatar da wannan kudiri. Wannan kudiri idan ya zama doka…

Read More

An Fafata Tsakanin ‘Yan Shi’a Da Jami’an Tsaro A Abuja

Wata yarinyar ‘yar Makarantar Sakandare ta rasa rayuwarta a ranar Laraba yayin da rikici ya barke tsakanin ‘yan kungiyar Shi’a da suke gudanar da zanga-zanga a kasuwar Wuse, birnin tarayya Abuja da jami’an tsaro. Yarinyar, dalibar Government Secondary School, Wuse ta gamu da ajalinta ne yayinda take komawa gida daga makaranta. Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa wani jami’in dan sanda mai suna, Geoffrey A. Rafah, ne ya harbi yarinyar bisa kure amma ba’a tabbatar da wannan ikirarin ba. Hakazalika, ‘yan Sanda sun garkame ‘yan jarida biyu dake…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Abuja

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun yi awon gaba da Sarkin garin Rubochi da ke karkashin karamar hukumar Kuje ta Abuja. An dai ce ‘yan bindigar sun je gidan Etsu Mohammed Ibrahim Pada ne da misalin karfe biyu na daren Talata, inda suka yi amfani da bindiga wajen fitar da basaraken daga dakin sa sannan suka yi awon gaba da shi. Wata ‘ya ga Sarkin na Rubochi ta shaida wa mana cewa “ba a samu rasa rai ba amma kuma ‘ya’yan sarkin guda biyu sun…

Read More