Dalilanmu Na Cigaba Da Kulle Jama’ar Kaduna – El Rufa’i

Jawabin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ga al’ummar Jihar Kaduna game da bitan dokar kulle Ya ku al’ummar Jihar Kaduna, 1. A madadin Gwamnatin Jihar Kaduna ina amfani da wannan dama domin in mika godiya ga al’umma na irin jajircewar da suka yi tun daga lokacin da Gwamnati ta sanya dokar kulle a ranar 26 ga watan Maris 2020. Dokar wanda aka sanya na kwana talatin sannan daga bisani aka kara wasu kwanaki talatin a ranar 26 ga watan Afrilu domin dakile yaduwar cutar Covid-19. 2. A…

Karanta...

CORONA:Duk Almajirin Da Aka Kora Yazo Zamfara – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya janye batun maida almajirai jihohin su na asali, sannan ya rusa kwamitin da ya nada domin haka. Hakan ya biyo bayan ganawa da yayi da wasu jiga-jigan malamai ne a jihar. Idan ba a manta ba Gwamna Matawalle, kamar wasu gwamnonin ya lashi takobin maida almajirai jihohin su na asali a dalilin barkewa annobar Korona. Sai dai kuma yanzu ya canja shawara, ya ce duk wanda ke son yin almajirci a jihar Zamfara, ya garzayo abin sa, gwamnati na maraba da shi. Abin da…

Karanta...

Karya Doka: Limamai Uku Sun Shiga Hannu A Jihar Kaduna

‘Yan sanda sun tsare malamai uku da suka jagoranci sallar idi da ta Juma’a a garin Zaria jihar Kaduna. Yanzu kwana hudu ke nan babu bayani game da daya daga cikin malaman wanda ke tsare a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda (CID). Biyu daga cikin malaman sun amsa tambayoyi ne kan Idin karamar salla da suka jagoranta a ranakun Asabar da Lahadi. ‘Yan sanda sun gayyaci Sheik Sani Khalifa tare da yi masa tambayoyi ne kan sallar Idi da ya yi limanci a ranar Asabar. Daga bisani…

Karanta...

Zan Garkame Duk Wanda Ya Tura Danshi Almajiranci – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ta gargadi iyayen da ke kai yaransu Almajirci da cewa za’a yi musu daurin shekaru biyu a gidan kaso. El-Rufa’i ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ya ziyarci wasu Almajirai 200 da aka kawo daga jihar Nasarawa kuma ake kula da su a kwalejin gwamnati dake Kurmin Mashi, Kaduna. Gwamnan ya kara da cewa duk Malamin Allon da ya karbi yara zai fuskanci fushin hukuma inda za’a daure shi sannan a ci shi tarar N100,000 ko N200,000 kan ko wani yaro. Saboda haka, za…

Karanta...

Pantami Bai San Darajar Mata Ba – Dabiri

Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta mayarwa da ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, martani bayan ya karyata zargin da take yi na cewa ya tura mutane da makamai su kori ma’aikatan ta daga ofishin da hukumar NCC ta basu. A wata hira da tayi da SaharaReporters, Dabiri-Erewa ta zargi ministan da aika ‘yan bindiga da su karbe ofishinta a watan Fabrairu. Sai dai ministan ya karyata wannan zargi da take yi a kanshi ta shafinsa na Twitter, inda ya ce karya take zabga…

Karanta...

Ranar Sallah: Ku Azabtar Da Duk Wanda Ya Karya Doka- El Rufa’i Ga Jami’an Tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Alhaji Umaru Muri ya yi kira ga mutane su bi dokokin da aka kafa domin kare kai daga cutar Coronavirus da ta zama annoba a fadin Duniya. CP Umaru Muri ya bayyana cewa za su yi maganin duk wanda ya saba dokar zaman gida da shiga cinkoso a jihar Kaduna a yayin da musulman Duniya ke yin bikin karamar sallah. Umaru Muri ya fitar da jawabi ta bakin jami’in da ke magana da yawun ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya na mai cewa za…

Karanta...

Sallar Idi: Kuyi Gajerun Hudubobi – Ganduje Ga Limaman Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya shawarci malaman addini a Kano da su gabatar da gajeriyar huduba yayin sallar idi. A wata takarda da sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Abba Anwar ya fitar a jiya, ya ce za a yi sallar idi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar. Amma dole ne Musulmai su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka tanadar don sallar jam’i. “Kamar yadda manyan Malamai suka shawarci limamanmu, ya kamata a yi huduba gajera a yayin sallar Idin saboda kalubalen Corona virus da muke…

Karanta...

Zamu Zama Gatan Almajirai A Kasar Nan – Gwamnonin Borno Da Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa ba za su kori duk wani almajiri da ba dan asalin jihar ba, maimakon haka za su yi gyara ne a harkar ta almajiranci, saboda su ma yara almajiran ‘ya’yansu ne. Gwamna Buni ya kara da cewa jihohin Borno da Yobe cibiyoyi ne na neman ilmin addini a tarihance, don haka gwamnatinsa ta shirya yi wa harkar almajiranci kwaskwarima. Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan, Gwamnatin jihar Borno ma na tuna cewa ba za ta kori almajirai…

Karanta...

Birnin Gwari Ya Dace Ka Tare Ba Kano Ba – Ganduje Ga El Rufa’i

A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ranar Sallah da kansa zai je ya tare hanyar Kano dan kar kowa ya shigar masa jiha daga Kanon. Gwamnan ya bayyana hakane a yayin jawabin da yayiwa mutanen jihar tasa, kamar yadda Wakilin Jaridar Muryar ‘Yanci ya saurara. Saidai ga dukkan alama wannan magana ba tawa bangaren gwamnatin jihar Kano dadi ba inda daya daga cikin hadiman gwamna Ganduje wani ya mayar wa da gwana El-Rufai martani. Hadimin gwamnan Kano kan kafafen sada zumunta, Abubakar Aminu…

Karanta...

Za A You Idi Da Hawan Sallah A Katsina – Masari

Duk da hauhawan da cutar Corona ke yi a jihar Katsina, Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce zaa dage dokar hana zirga zirga da gwamnatin jihar Katsina ta sanyawa wasu kananan hukumomin jihar Katsina da aka samu bullar annobar cutar Corona a cikin sati mai zuwa, domin al’umma su samu damar yin hidimomin saye-sayen kayan Sallah da yin Sallah idi da Kuma hawan Sallah a jihar Katsina na al’ada. Gwamna Masari ya tabbatar da hakan a lokacin da yake wata hira ta musamman da manema labarai a…

Karanta...

Mun Shirya Tsaf Domin Maka El Rufa’i Kotu – Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama

Wakilin kungiyar Kare hakkin ‘dan Adam (Amnesty)reshen jihar kaduna, Alhaji Musa Jika ya bayyana cewa a shirye suke su maka Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad Elrufai muddin bai biya Korarrun Sakatarorin din din da sauran Ma’ikatan da aka sallama ba bisa ka’ida ba a fadin jihar kaduna. “Alhaji Musa ya bayyana hakan ne yayin zantawa da Wakilinmu inda yace babu inda Dokar ‘Kasa ta bayyana cewar wani gwamna yana da karfin ikon ragewa Ma’ikatan gwamnati da aka sallama aiki kudaden sallama aikin su (Fansho). ” Yace a binciken da…

Karanta...

Zamfara: Uwargidan Gwamna Ta Raba Kayan Tallafi

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle ta kadamar da bada tallafin kayan abincin da kudin cefane ga mata domin rage musu radadin zaman gidan karkashin shirin tallafawa mata na “Women Empowemt Program” wanda Princes Dr Rabi Shinkafi ke jagoranta. Allah ka taimaki Uwar Marayun jihar Zamfara, Ka ci gaba da dafa mata a dukkan lamurranta na alhair.i Amin.

Karanta...

Karya Doka: Mun Tatsi Milyan Daya Da Rabi Wajen Talakawan Kaduna – Dikko

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta tara Naira milyan 1.9 a cikin kwanaki biyu na makon da ya gabata daga kudaden da take cin mutanen da suka keta dokar kullen zaman gida sakamakon bullar cutar coronavirus. Kwamishiniyar Shari’a Aisha Dikko ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar. ”Ta ce akasarin masu laifin an kama su da laifin kin sanya takunkumin rufe hanci, face mask, da kuma fitowa waje ba tare da kwakkwaran dalili ba. ”Gwamnatin ta ce ga duk wanda aka samu ya fito waje babu…

Karanta...

Jigilar Almajirai : Ganduje Ya Yi Maganin El Rufa’i

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad Elrufai da wasu jihohin da ke korafin cewa ta mayar musu da almajirai masu dauke da kwayar cutar korona, tana cewa ita ma ana kawo mata almajirai masu dauke da cutar korona. Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan halin da kwamitin kar ta kwana kan annobar ke ciki. Gwamnan ya bayyana cewa mayar da almajirai jihohinsu na asali batu ne da aka yanke hukunci a kai…

Karanta...

CORONA: Buhari Da APC Sun Ci Amanar Najeriya – PDP

Jam’iyyar PDP tace shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma jam’oyyar sa marar cika alkawari ta APC gaba daya sunci amanar almajirai, da kuma sauran gajiyayyu, da talakawan Najeriya bayan sun gama amfani dasu wajen samun nasara a 2015. Jam’iyyar tace sai yanzu mutane suke kara fahimtar kudirorin APC a fili musamman babban halinsu na nuna halin ko in kula ga mutane inda suka dauke talakawan Najeriya ba a bakin komai ba musamman tun daga lokacin da annobar COVID-19 ta shigo kasar nan. PDP tace wannan halin ko in kula din…

Karanta...