Rahotannin dake shigo mana daga Æ™asar Kasar Qatar na bayyana cewar Croatia ta taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Qatar inda ta hau matakin na uku bayan ta doke Maroko da ci biyu da daya. Wannan ne karo na uku da Croatia ke samu kyauta a gasar cin kofin duniya saboda a shekarar 1998 ita ce ta yi ta uku, sai kuma a 2018 ta zama ta biyu a gasar bayan Faransa ta doke taa wasan karshe. A yau Lahadi ne za a buga…
Cigaba Da KarantawaCategory: Wasanni
Wasanni
Tsohon Dan Wasan Kwallon Brazil Pele Na Kwance Rai A Hannun Allah
An kwantar da shahararren dan kwallon Brazil Pele a asibiti amma Æ´arsa ta ce baya cikin mummunan yanayi. Tashar ESPN Brasil ta bada rahoton cewa an garzaya da Pele zuwa asibitin Albert Einstein da ke birnin Sao Paulo saboda yana fama da kumburi a jikinsa. Amma diyar Pele din Kely Nascimento ta wallafa a shafinta na Instagram cewar jikin bai yi tsanani ba. A watan Satumbar 2021 ne aka yi wa Pele tiyata kuma tun daga lokacin ake yawan kwantar da shi a asibiti. ESPN Brasil ta bada rahoton cewa…
Cigaba Da KarantawaWasanni: Morocco Ta Doke Belgium A Gasar Cin Kofin Duniya
Morocco ta bai wa Belgium mamaki bayan ta doke ta 2-0 a wasa na biyu a rukuni na shida a Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci. A minti na 73 Morocco ta ci kwallon farko ta hannun Abdelhamid Sabiri, sannan Zakaria Aboukhlal ya kara na biyu daf da lokaci zai cika. Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Coutois shi ne ya yi kuren kwallon farko a bugun tazara da Sabiri ya buga masa, saura minti 17 a tashi daga wasan. A karawar Belgium wadda ba ta taba daukar kofin…
Cigaba Da KarantawaFaransa Ta Kai Zagaye Na Biyu A Gasar Cin Kofin Duniya
Tawagar Æ™wallon Æ™afa ta Faransa mai riÆ™e da Kofin Duniya ta zama ta farko da ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta lallasa Denmark 2-1. Tun a ranar Juma’a Qatar mai masaukin baÆ™i ta zama Æ™asa ta farko da aka yi waje da ita daga gasar. Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa Æ™wallayen, inda mai tsaron bayan Denmark Andreas Christensen ya ci wa Æ™asarsa É—aya. Kazalika, a É—azu an yi gumurzu tsakanin Saudiyya da Poland inda Poland É—in ta doke Saudiyya 2-0. Haka kuma an…
Cigaba Da KarantawaKuskure Ne Ba Qatar Damar Daukar Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya – Tsohon Shugaban FIFA
Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ya ce an yi kuskure da aka bai wa Qatar damar karɓar bakuncin gasar cin Kofin Duniya. Sepp Blatter wanda ya shugabanci hukumar FIFA lokacin da aka ɗauki matakin a 2010, ya bayyana cewa an yi wa hukumar matsin lamba kuma da alama kuɗi ya yi tasiri wajen yanke shawarar. Ana zargin Qatar da cin hanci da kuma cin zarafin ma’aikata a wuraren gine-gine. An kuma soki ƙasar kan yadda take tafiyar da al’amuran masu ra’ayin auren jinsi.
Cigaba Da KarantawaWasanni: Mikel Obi Ya Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa
Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa na Najeriya Mikel John Obi ya sanar da ritayarsa daga wasan kwallon kafa. Mikel Obi ya sanar da matakin ne ranar Talata a shafinsa na Instagram. Ya lashe gasar Zakarun Turai a 2012 tare da tsohuwar kungiyarsa ta Chelsea, baya ga wasu jerin kofunan da ya lashe, kuma a baya-bayan nan yana buga wa kungiyar Kuwait SC ne. Ga wani abu cikin sakon da ya wallafa a Instagram: “Akwai wani karin magana da ke cewa komai na da karshe kuma haka lamarin yake ga…
Cigaba Da KarantawaTaraba: Kotu Ta Kori Timothy Hamman Daga Jagorancin Kungiyar Taraba FA
BASHIR ADAMU, JALINGO Babban Kotun Gwamnatin Tarayya dake da zamanta a Jalingo ta kori Timothy Heman Magaji, inda ta tabbatar da Sanusi Mahmud a matsayin sahihi kuma zababben Shugaban Kungiyar Kwallon Kafan Jihar Taraba, wato Taraba FA a turance. Wakilinmu Bashir Adamu daya halarci zaman Kotun ruwaito mana cewa; Bayan daukan tsawon lokaci yana karantawa tare da nazari akan hukuncin, Mai- Shari’a, Simon Akpah Amobeda daya jagoranci Shari’an ya Umurci Timothy Magaji da nan take ya fice daga wannan Ofishin kuma kar ya sake aiyana kanshi a matsayin Shugaban Kungiyar…
Cigaba Da KarantawaManchester United Ta Doke Arsenal Da Ci 3-1 A Gasar Firimiya
Manchester United ta doke Arsenal da ci 3-1 a wasan mako na shida a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford. United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Anthony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax. Tun a minti na 12 da fara tamaula Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen keta tun farko. Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da…
Cigaba Da KarantawaCin Zarafin Dan Kallo: ‘Yan Sanda Sun GargaÉ—i Ronaldo
‘Yan sanda sun ja kunnen Cristiano Ronaldo, bisa wani faifan bidiyon da ya nuna dan kwallon ya wafce wayar dan kallo ya buga da kasa. ‘Yan Sandan Merseyside sun ce sun yi wa dan wasan mai shekara 37 tambayoyi, sun kuma gargadeshi kan laifin da ya shafi cin zarafi da lalata dukiya. Jami’an tsaron sun tabbatar da faruwar lamarin sun kuma damu da halayar a karawar da United ta yi da Everton ranar 9 ga watan Afirilu. Hukumar kwallon kafa ta Ingila itama ta ce za ta gudanar da nata…
Cigaba Da KarantawaWasanni: Salah Ya Sabunta Kwantiragi Da Liverpool
Mohamed Salah ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Liverpool kaka uku. Saura kaka daya kwantiragin dan wasan mai shekara 30 dan kwallon tawagar Masar ya kare a Anfield, daga baya aka kama rade-rade kan makomarsa a Liverpool. Salah ya ci kwallo 156 a wasa 256 da ya yi wa Liverpool a kaka biyar da ya yi a Anfield, tun bayan da ya koma kungiyar daga Roma. An fahimci cewar sabuwar yarjejejeniyar da Salah ya kulla ya zama dan kwallon da zai ke karbar albashi mafi…
Cigaba Da KarantawaWasanni: An Kori Shugaban Kano Pillars A Firimiyar Najeriya
Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take. Hukumar ta fitar da wani jawabi a karshen mako da ya shafi dakatar da shugaban da wasu karin hukunce-hukunce. An tuhumi Kano Pillars da karya doka ta gudanar da wasannin Firimiya a lokacin da ta buga karawa da Dakkada ranar 23 ga watan Yunin 2022. A wasan ne shugaban hukumar Pillars, Suraj Yahaya ya ci zarafin mataimakin alkalin wasa Daramola Olalekan. An kuma ci tarar Kano Pillars da laifin…
Cigaba Da KarantawaSalah Ya Zama Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya
Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah da ‘yar kwallon Chelsea, Sam Kerr sun lashe kyautar fitattun ‘yan wasa ta bana ta PFA. ‘Yan wasan biyun sun lashe kyautar takalmin zinare a kakar da aka kammala a gasar Premier ta 2021-22 da kuma gasar mata ta Super League. Dan wasan Manchester City, Phil Foden, mai shekara 22 shi ne gwarzon matashi da ‘yan wasan suka zaba a bana, karo biyu a jere kenan. Lauren Hemp, mai shekara 21, wadda take taka leda a City, ita ce mace matashiya da aka zaba ba…
Cigaba Da KarantawaGwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Tsoffin ‘Yan Wasan Super Eagles Gidaje
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ya gabatar da takardun gidaje ga tsoffin Æ´an wasan Æ™wallon kafa na Super Eagles da gwamnatin tarayya ta yi masu alÆ™awali. Hotunan da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta wallafa a Twitter sun nuna lokacin da Æ´an wasan ke karbar takardun gidajen hannun Fashola a ranar Juma’a. An ba tawagar Super Eagles da suka buga wa Æ™asar wasa a 1994 gidajen ne bayan shekara 28 da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta yi masu alÆ™awali lokacin da Æ´an wasan suka lashe kofin Afirka a…
Cigaba Da KarantawaRikicin Ukraine: Mamallakin Chelsea Na Shirin Cefanar Da Kungiyar
Mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich ya tabbatar da cewa zai sayar da kulob din. Abramovich ya sanar da hakan ne a shafin intanet na Chelsea FC cewa matakin sayar da kungiyar ” yana da wahala gare shi, kuma ”yana jin radadin rabuwa dashi.” Dama wani biloniya dan kasar Switzerland ya fada wa manema labarai cewa an taya masa kungiyar. A makon da ya gabata ne Abramovich ya mika ragamar tafiyar da kungiyar hannun gidauniyar amintattun kungiyar biyo bayan kutsawa Ukraine da Rasha ta yi. Sai dai kuma…
Cigaba Da KarantawaWasanni: An Bai Wa Everton Hakurin Buga Fenariti
Kungiyar alkalan wasan kwallon kafa ta Ingila ta bai wa Everton hakuri saboda hana ta bugun fenareti a wasanta da Manchester City. Shugaban kungiyar Mike Riley ya kira kocin kungiyar Frank Lampard ta waya, ya fada masa cewa suna ba kulob din hakuri bisa kuskuren da aka tabka a wasan na ranar Asabar. City na cin daya ne a Goodison Park a lokacin da dan wasan tsakiyarta Rodri ya taba kwallo da hannu a da’irar gola. To amma lafari Paul Tierney ya ce ba tabin a zo a gani bane,…
Cigaba Da KarantawaWasanni: Hukumar Kwallon Kafa Ta Dauki Tsattsauran Mataki Kan Rasha
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta fada wa Rasha cewa za ta buga wasannin share fagen zuwa gasar cin kofin duniya ne da sunan ‘Football Union of Russia’, saboda kutsawa Ukraine da ta yi. Hakama FIFA ta ce ba za ta yi amfani da tutar Rasha ba, kuma zata buga wasannin ne a wata kasa daban. To amma tuni kasashe da dama sun bayyana cewa ba za su buga wasa da Rasha ba. Dama Rasha na da wasan share fagen zuwa Qatar 2022 da Poland, kafin ta buga da Chek…
Cigaba Da KarantawaZa A Buga Wasan Karshe Na Kofin Zakarun Turai A Paris
Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai watau Champions League na bana a Paris, bayan da aka dauke daga Rasha saboda kutsen da kasar ta yi a Ukraine. A baya an shirya buga wasan mafi girma a Turai a filin wasa na Gazprom Arena da ke St Petersburg a ranar 28 ga watan Mayu. Amma a yanzu hukumar kwallon Turai – UEFA ta ce a filin wasa na Stade de France da ke Paris. Hukumar Uefa ta nuna godiya ga shugaban Faransa, Emmanuel Macron saboda “nuna…
Cigaba Da KarantawaBuhari Ya Taya Senegal Murnar Lashe Kofin Afirka
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya takwaransa na Senegal Macky Sall murna, bayan da kasarsa ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika. Tawagar Teranga Lions ce ta yi nasarar lashe kofin na gasar AFCON da aka kammala a Kamaru makon da ya wuce. Shugaba Buhari ya yi murnar ne yayin da yake karbar bakuncin jakadan Senegal a Najeriya Babacar Matar Ndiaye a fadarsa da ke Abuja
Cigaba Da KarantawaAn Bankado Badakalar Kudade A Kungiyar Bercelona
Wani rahoto kan yadda aka gudanar da hada-hadar kuÉ—aÉ—e a Æ™ungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya nuna cewa an aikata manyan laifuka da suka saÉ“a doka. An yanke shawarar gudanar da binciken ne a watan Oktoban bara bayan gano cewa ana bin kungiyar bashin sama da dala biliyan É—aya da rabi. Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kulob din ya kai koke makon da ya wuce ga masu shigar da kara na cikin gida don ya gano an aikata ba daidai ba a lokacin mulkin Josep Maria Bartomeo da ya…
Cigaba Da KarantawaDa Dumi-Dumi: Kocin Super Eagles Ya Ajiye Aiki
Kocin Æ™wallon Æ™afa na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Austin Eguavoen, ya ajiye aiki a matsayin kocin riko bayan an fitar da kungiyar daga gasar Kofin Ƙasashen Afrika ranar Lahadi. Bayan nasarorin da suka samu a wasannin rukuni, kungiyar ta kasa yin nasara a kan Tunisiya a wasan zagaye na ‘yan 16. A wani taron manema labarai wanda aka yi bayan wasan, Eguavoen ya ce ya yanke hukuncin komawa tsohon matsiyansa na mai kula da harkokin wasanni na NFF. Eguavoen ya ce “abin da zai faru shi ne; ni ne…
Cigaba Da Karantawa