Za A Yi Jana’izar Mutane 51 Da ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Zamfara

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar nan gaba a yau ne za a yi jana’izar ƙarin wasu mutane da ‘yan Bindiga suka kashe bayan wani mummunan artabun da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya. Wani ganau ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa marecen Laraba, sun ƙirga mutum 51 da aka kashe daga ƙauyukan gundumar Magami daban-daban. ‘Yan fashin daji sun auka wa mutane ne lokacin da suka yi yunƙurin kai ɗauki ga mutanen ‘Yar Doka, waɗanda wasu bayanai ke cewa sun…

Cigaba Da Karantawa

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Haramta Tashe A Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta hana yin tashe a jihar ne saboda yadda wasu ɓata- gari ke amfani da lokacin tashe wajen yin faɗace-faɗacen daba. A cewar kakakin ‘yan sandan ta Kano, DSP Abdulahi Haruna Kiyawa, hana yin tashe mataki ne na kare al’adar da masu shaye-shaye, da fadan daban ke san lalatawa. Tashe dai dadaddiyar al’adace da aka shafe shekaru masu yawa ana yi a kasashen Hausa, a cikin watan azumi.

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Ɗaliban Jami’a Sun Bukaci Kudin Fansa

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan Bindigar da suka sace dalibai a wata jami’a mai zaman kanta a Kaduna mai suna Greenfield sun nemi kuɗin fansa har Naira Miliyan 800, Daya daga cikin iyalan daliban Jami’ar Greenfield da ke Kaduna ya ce ‘yan bindigan sun bukaci a biya Naira miliyan 800 matsayin kudin fansa kafin su sako daliban 23. “Ana tattaunawa, masu garkuwar sun tuntubi wasu iyalan daliban suna neman a biya Naira miliyan 800,” a cewar, Georgina Stephen, yar uwan daya daga cikin daliban da aka ace.…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Da Dama A Jami’ar Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ɗauke manyan makamai sun kai hari kan Jami’ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka sace dalibai da dama. Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari a Jami’ar ne da daren Talata inda suka yi awon gaba da dalibai da yawa. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa “ya zuwa yanzu ba mu kai ga tantance adadin daliban…

Cigaba Da Karantawa

Kisan Ƙare Dangi Ga ‘Yan Bindiga Ne Laƙanin Samun Zaman Lafiya – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, ya ba Gwamnati Shawarar cewa kamata yayi a kashe gaba dayan ‘yan Bindiga. Ya bayyana hakane a wajan taro na musamman da aka yi a babban birnin tarayya Abuja. Gwamna El-Rufai yace ta hakane kawai za’a samu zaman Lafiya a makarantu da sauransu. Yace duk wani dake zaune a cikin daji yana da Laifi dan haka kawai ya kamata Sojojin sama dake da kayan aiki suwa dazukan Najeriya da masu laifi ke boye a ciki luguden wuta.

Cigaba Da Karantawa

Dalilan Da Ya Sa Muka Tura Karnuka Gadin Makarantu – Masari

Gwamnatin jihar Katsina ta ce karnukan za su dinga sanar da masu gadi da dalibai duk wani motsi ko bakuwar fuskar da ba su amince da ita ba ta hanyar haushi Gwamntin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce za ta tura karnuka domin aikin gadi a makarantun da ke fadin jihar. Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Badamasi Lawal Chiranci ya shaida wa BBC cewa jihar ta ware makudan kudade domin samar da tsaro a makarantun ciki har da kewaye su da kuma ajiye karnuka. “Gwamnan jihar Katsina Alhaji…

Cigaba Da Karantawa

Yaƙi Da Ta’addanci: Sojin Najeriya Basu Da Kayan Aiki – Shettima

Tsohon Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Kashim Shettima yace sojojin Najeriya basu da isassun kayan aikin da zasu iya murkushe mayakan Boko haram. Yayin da yake tsokaci kan matsalar tsaro da talaucin da suka addabi yankin arewacin Najeriya, Shettima yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada isassun kudaden da za’a sayawa sojoji kayan aiki amma wadanda aka dorawa hurumin aikin sun gaza. Tsohon gwamnan yace abin takaici ne yadda matsalar tsaro ke cigaba da addabar Najeriya a karkashin gwamnatin su ta Jam’iyyar APC ba wadda ta kwashe shekaru 6 a…

Cigaba Da Karantawa

Muna Dab Da Dira Arewa – Tsagerun Inyamurai

Kungiyar Mayakan Inyamurai ta IPOB, ESN ta bayyana cewa nan babda dadewa za su dira yankin Arewa. Hakan ya biyo wani martani ne da ƙungiyar ta fitar game da wani zargi da Kungiyar Miyetti Allah za su shigo da wasu yan uwan su 5000 da taya su samar musu kariya da tsaro daga ESN dake kai musu hari. Daily Nigerian ta ruwaito cewa a wannan takarda wanda mai magana da yawun kungiyar Emmanuel Powerful ya sa wa hannu, ya ce ” Shege ka fasa, suna jiran wadanda ‘Yan kungiyar Miyetti…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Yi Odar Karnuka Domin Gadin Makarantu

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura Karnuka gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami’ar tsaro wajen dakile ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Kwamishinan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar. “An bamu shawaran tura Karnuka kowace makaranta saboda suna da horaswa na gano wani mai yunkurin kutse fiye da dan Adam.” “Wadannan karnukan idan aka tura su, zasu ankarar da dalibai da sauran jami’an tsaro idan wasu yan bindiga na kokarin zuwa.”…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 500 Kuɗin Fansar Ɗalibai

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake yankin ƙaramar Hukumar Igabi Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar ‘ya’yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su. An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan ‘ya’yansu, duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021. A yayin tattaunawa da…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: An Kama Jami’an Tsaro Masu Taimakawa ‘Yan Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama wasu jami’an tsaro bakwai a jihar bisa zarginsu da taimaka wa ‘yan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar. Gwamnatin ta sanar da haka ne a yayin wani taron manema labarai da ma’aikatun watsa labarai da harkokin tsaron na jihar suka gudanar a yau. A sanarwar da gwamnatin ta raba wa manema labarai ta ce jami’an tsaron bakwai sun fuskanci tambayoyi kuma sun amsa laifukansu da suka hada da ƙyanƙyasa wa ‘yan ta’adda bayanan sirri na soji, da samar musu makamai da…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Jama’ar Gari Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 30

Mazauna kauyen Majifa da ‘yan banga a karamar hukumar Kankara sun kashe a kalla mutane 30 da ake zargin yan bindiga ne a jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Duk da cewa bayyanai basu kamalla fitowa ba a lokacin hada wannan rahoton, majiyarmu ta gano cewa yan kauyen sun kafa wa yan bindigan tarko ne. Wani mazaunin kauyen ya shaidawa majiyarmu cewa lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin. “Mazauna kauyen sun samu labarin cewa yan bindigan na shirin kawo musu hari cikin dare, hakan yasa suka…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Matan Chibok Sun Cika Shekaru 7 A Hannun Boko Haram

Rahotanni daga Maiduguri Fadar gwamnatin Jihar Borno na bayyana cewar a daidai lokacin da ‘yan matan Chibok suka cika shekaru 7 a hannun Boko Haram, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce da sannu za’a ceto dalibai matan da yan ta’addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Chibok a 2014. Zulum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar bayan shekaru bakwai da ‘yan Boko Haram sukayi awon gaba da daliban yayinda suke shirin rubuta jarabawar kammala Sakandare. Duk da cewa an ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kwalejin Soji Dake Jaji

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki kwalejin Sojoji dake garin Jaji, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. Wasu mazauna garin da aka zanta dasu sun bayyana cewa yan bindigan sun je garkuwa da wasu ma’aikatan kwalejin ne da kuma mazauna garin na Jaji dake hanyar Kaduna zuwa Zariya. Kwalejin Sojin dake Jaji shahararriyar makaranta ce da ake horas ds Sojojin kasa, na sama da kuma na ruwa a tsawon lokaci. Wani mazauni Garin mai suna Malam Adamu, ya bayyanawa…

Cigaba Da Karantawa

Zan Ceto Sauran ‘Yan Matan Chibok Da Kaina – Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce za za a ceto sauran ‘yan matan Chibok da ma sauran mutanen da aka sace daga jihar cikin koshin lafiya. Zulum ya fadi hakan ne a cikin wani bayaninsa na cikar shekara bakwai da mayakan Boko Haram suka sace daliban na makarantar mata ta Chibok lokacin da suke gab da rubuta jarrabawarsu ta karshe. Duk da cewa an sako wasu daga cikin daliban to amma har yanzu akwai da dama wadanda suka rage a hannun kungiyar ta Boko Haram. Zulum ya ce a…

Cigaba Da Karantawa

Ban San Komai Ba A Ɓatar Kuɗin Makamai – Buratai

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya bayyana cewa babu ruwan sa da harkallar Dala Biliyan daya da aka fidda don sayen makamai. A wata takarda wadda lauyan sa, Osuagwu Ugochukwu, ya sa wa hannu, Buratai ya ce a iya sanin sa bai san da wata dala biliyan 1 da aka taba ba shi wai na makamai kuma tsoffin manyan hafsoshin Najeriya su ka yi awon gaba da su ba. “ Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mungono wanda aka danganta wannan kalamai da shi ya ce…

Cigaba Da Karantawa

Badaƙalar Makamai: Shugaban Dakarun Soji Ya Bayyana Gaban Majalisa

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa shugaban sojojin ƙasar nan, Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyana a gaban kwamitin majalisa don amsa tambayoyi dangane da batun makamai da ake ta cece kuce akai. Majalisar ta kafa kwamitin ne domin bincikar yanda aka siya, aka yi amfani da makamai da harsasai da sauran kayan yaƙi a rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro. Kwamitin ya gayyaci shugaban sojojin aƙalla sau biyu domin yazo ya amsa tambayoyi kan yadda aka siya makaman da kuma yadda aka yi amfani da su. Hakanan…

Cigaba Da Karantawa

Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Da Dama A Kauyen Rabah

Kawo yanzu ana cigaba da tattara gawawakin mutane da dama wadanda ‘yan bindiga suka yiwa kisan gilla a kauyen Rarah dake cikin karamar hukumar mulkin Rabah ta jahar sokoto da tsakar ranar yau dinnan kamar yadda muka baku labarin dazu. Daga cikin wadanda aka cinto gawawakin su Akwai ‘yan sakai da kuma Limamin masallacin jumu’ah na 2 dake kauyen Liman Shehu Rarah da wasu mutane. ‘yan ta’addan sun tabka Babbar barna a kauyen da har yanzu ba’a ida kammala tantancewa Ba. Amma sai dai, bayan sun kashe mutane haka ma…

Cigaba Da Karantawa

Kisan ‘Yan Arewa: Shiru A Arewa Ba Tsoro Bane – Babba Kaita

Sanata Ahmad mai wakiltar mazaɓar Katsina ta Arewa a majalisar Dattawa Sanata Ahmed Babba Kaita, ya yi kira da babbar murya akan a dakatar da kashe ‘yan arewa da ake faman yi a kudancin ƙasar nan cikin gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba. Sanata Babba Kaita, ya cigaba da cewar, kamar dai yadda yan kudancin ƙasar nan ke walwala a Arewa, yakamta abar kowane ɗan arewa ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali a sashin Kudancin kuma yakamata abarsu su yi kasuwancin a kudanci kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnoni Sun Bukaci Sabon Shugaban ‘Yan Sanda Ya Kawo Ƙarshen ‘Yan Ta’adda

Kungiyar Gwamnonin Arewa sun yi kira gami da neman sabon Shugaban rundunar ‘yan sandam Najeriya Usman Alkali, da yayi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin tsaro ya dawo a kasar nan musanman yankin Arewa. Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa kuma Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ne ya yi kiran a ranar Asabar, 10 ga Afrilu, a cikin sakon taya murna ga sabon shugaban ‘yan sandan, da ƙungiyar gwamnonin ta fitar. A cikin wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Makut Macham, ya ce Alkali ya cancanci wannan sabon matsayin duba…

Cigaba Da Karantawa