Kano: An Janye Dokar Hana ‘Yan A Daidaita Sahu Hawa Manyan Tituna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar da ta hana ƴan adaidaita-sahu bin wasu manyan tituna cikin kwaryar Kano. Shugaban Hukumar kula Da Zirga-zirgar Ababen-hawa, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Kano. Ya ce an janye dokar ne saboda matuƙa baburan adaidaita-sahu ɗin sun yi biyayya kuma al’umma sun yi suka a kan dokar.

Cigaba Da Karantawa

Zagin Aisha Buhari: An Garkame Dalibi Aminu A Kurkuku

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin Uwargidan Shugaban ƙasa Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari. Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba. Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli…

Cigaba Da Karantawa

Lallai A Kama Aisha Buhari Sakamakon Cin Zarafin Dalibin Da Ta Yi – Naja’atu Mohammed

A hira da gogaggiyar ƴar siyasa kuma mai kare hakkin ɗan Adam, Naja’atu Mohammed ta yi kira ga rundunar tsaron Najeriya su gaggauta yin awon gaba da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, saboda kama wani Aminu Mohammed da tasa aka yi sannan ta rika jibgarsa. Idan ba a manta ba Aisha Buhar ta sa an tattaki tun daga Abuja zuwa garin Dutse inda aka kama wani matashin ɗaliɓi wai don ya saka rubutu da ya shafi uwargidan a shafin tiwita. Jaridar Daily Nigerian ta buga hira da ta yi da…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Daure Shugaban ‘Yan Sanda Watanni 3 A Kurkuku

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Talata ta yanke wa Sufeto-Janar, IGP, na ƴan sanda, Usman Baba, zaman gidan yari na tsawon watanni uku, bisa zargin kin bin umarnin hukuncin da wata kotu ta yanke na kin mayar da wani jami’in dan sanda, Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritaya ta ƙarfi da yaji bakin aiki. Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Okoli, Arinze Egbo, ya shigar, ya kuma gargadi Baba kan rashin bin hukuncin da kotun farko ta yanke…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Mata 721 Aka Yi Wa Fyade Cikin Watanni Tara – Hukumar Kare Hakkin Dan Adam

Hukumar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta ce cikin watanni tara sun karbi bayanan aikata fyade har 721 daga sassan jihar. Shugaban hukumar ya shaida wa BBC cewa cibiyar da ke lura da wadanda aka yi wa fyade da sauran nau’ukan cin zarafin mata mai suna WARAKA ce ta tantance tare da bin diddigin al’amarin. Fyaɗe, matsala ce da ke ƙara ƙamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da kananan yara ta hanyar fyaden. Cibiyar WARAKA ta karbi korafin aikata fyade da sauran nau’ukan cin zarafin…

Cigaba Da Karantawa

Amnesty Ta Yi Kiran A Gaggauta Sakin Dalibin Da Ya Soki Aisha Buhari

Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam ta Amnesty International ta yi kira da a gaggauta sakin Aminu Adamu Muhammed, dalibi dan shekara 23 a Jami’ar Tarayya ta Dutse, wanda jami’an tsaro da ake zargin jami’an DSS ne su ka kama tun a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 da tsakar dare, kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, da ake zargin cin mutunci ne ga uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari. A ranar 8 ga watan Yuni ne Muhammad ya wallafa hoton Aisha Buhari a shafinsa na twitter, inda…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Fara Zirga-Zirgar Jirgin Abuja-Kaduna Yau Litinin

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna ba zai ci gaba da aiki ranar Litinin ba kamar yadda wasu kafofin yaɗa labarai suka ruwaito tun farko. Wata majiya a Ma’aikatar Zirga-Zirgar Jiragen Ƙasa ta shaida wa BBC Hausa cewa sai “nan gaba kaɗan” jirgin zai dawo aiki kamar yadda ministan ma’aikatar ya sanar a baya. A ranar Lahadi ne Minista Muazu Jaji Sambo ya kai ziyarar ganin gyaran da aka gudanar a kan titin jirgin sakamakon lalata shi da ‘yan bindiga suka yi a harin…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: An Damke Matar Da Ta Jefa Dan Kishiyarta A Rijiya

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta kama Maryam Habibu, ƴar shekara 18 da haihuwa, bisa zarginta da jefa ɗan kishiyarta mai shekaru hudu cikin rijiya a ƙaramar hukumar ƙafur ta jihar. Maryam wadda ta fito daga ƙauyen Leko da ke ƙaramar hukumar Ɗanja tare da wasu mutane 11 da ake tuhuma da laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami da satar shanu, an gabatar dasu a ranar Juma’a a shelkwatar ƴan sanda da ke Katsina. Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Gambo Isah, yayin da yake zantawa da…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Bukaci Gwamnati Da Ta Aiwatar Da Dokar Kare Hakkin Yara

An kirayi gwamnatin jihar Adamawa da ta kafa kwamitin da zai aiwatar da dokan kare hakkin yara a fadin jihar baki daya. Kodinatan kungiyar kare hakkin yara a jihar Adamawa Kwamared Sunday Kadiri ne ya yi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa. Mr Sunday yace kafa kwamitin zai taimaka gaya wajen aiwatar da dokar a tsakanin al’umma don haka nema yake jaddada kiransa ga gwamnatin da ta gaggauta kafa kwamitin domin ganin an samu cigaba wajen kare hakkin yara a fadin jihar baki…

Cigaba Da Karantawa

Za A Farfado Da Sufurin Motocin Haya A Abuja – Hukumar Birnin Tarayya

Rahoton dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da harkoki ke ci gaba da bunkasa da mutane, wata matsala da ake fuskanta a birnin ita ce ta sufuri musamman na motocin haya. Sufuri a birnin dai na da matukar muhimmanci saboda yawan ma’aikatan da ake da su kama daga na gwamnati da ma na kamfanonin masu zaman kansu, wannan ne ya sa sufuri ke da muhimmancin gaske a Abuja. Bisa la’akari da muhimmancin na sa ne hukumar babban birnin tarayyar, ta karfafa wa kamfaninta…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Bude Makarantun Islamiyya

A wani mataki na inganta karatun addinin musulunci an kirayi al’umma Musulmi da su maida hankali wajen bude makarantun islamiyoyi tare kuma da ingantasu domin samun cigaban addinin musulunci. Shugaban majalisar makarantun islamiyoyi a jihar Adamawa Mallam Muktar Dayyib ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola. Mallam Muktar ya kuma ja hankalin iyaye da malamai da su kasance masu hada kansu domin yin aiki kafada da kafada wanda a cewarsa hakan zai karawa yaran kwarin gwiwa ta maida hankali akan karatunsu yadda ya kamata. Da wannan…

Cigaba Da Karantawa

An Kara Farashin Akushin Abincin Dalibai A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an sake duba shirin ciyar da yaran makaranta a Najeriya inda aka duba shi tare da kara N30 kan N70 na kudin abincin ‘yan makaranta a jihar Delta da wasu Jihohi. Kwamishinan jin kai da tallafi na jihar Delta Dakta Darlington Ijeh, wanda ya bayyana hakan a Asaba, ya bayyana takaicinsa kan yadda masu dafa abincin ke kauro. Dakta Ijeh, wanda Gwamna Ifeanyi Okowa ya rantsar a watan Augustan 2022, ya sha alwashin lura da shirin gwamnatin tarayyan domin…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Zamfara Za Ta Dauki Nauyin Gasar Karatun Al’kur’ani Ta Bana

Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala shirye-shirye don daukar nauyin gasar al-Qur’ani ta kasa wanda za a yi a ranar 16 ga watan Disamba na wannan shekara mai ƙarewa ta 2023. Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a wajen bikin bude gasar al-Qur’ani na jihar wanda aka yi a Gusau a ranar Talata. Nasiha ya bayar da tabbacin cewa a shirye gwamnatin jihar take ta bayar da duk gudunmawar da ake bukata na kudi don gudanar da gasar cikin nasara da ba baki masu halartan gasar kulawar…

Cigaba Da Karantawa

Shehu Sani Ya Gargadi China Kan Ba Najeriya Bashi

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi kira ga kasar China ta yi taka tsantsan wurin ba wa Najeriya bashi. Sanatan ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin da ya ke magana wurin wani taro da Cibiyar Nazarin China (CCS) ta shirya a birnin tarayya Abuja. Yayin da ya ke yaba wa China wurin kawo cigaba a Najeriya da Afirka baki daya, ya ce China ta rika bada bashi ne kawai wanda zai kawo sauyi a rayuwar yan Najeriya. Ya ce: “Yana da muhimmanci duk…

Cigaba Da Karantawa

Yada Labaran Karya: NBC Ta Ci Tarar Gidan Talabijin Na Arise

Hukumar kula da kafafen yaɗa labaru ta ƙasa NBC ta ci tarar kafar yaɗa labaru ta Arise saboda zargin ta da yaɗa labarin ƙarya. A ƙarshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar zaɓe na binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rinƙa yaɗawa a shafukan intanet. NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, “gagarumin karan-tsaye ne ga dokar yaɗa labaru ta ƙasa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da…

Cigaba Da Karantawa

Yada Labaran Karya: NBC Ta Ci Tarar Gidan Talabijin Na Arise

Hukumar kula da kafafen yaɗa labaru ta ƙasa NBC ta ci tarar kafar yaɗa labaru ta Arise saboda zargin ta da yaɗa labarin ƙarya. A ƙarshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar zaɓe na binciken ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rinƙa yaɗawa a shafukan intanet. NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, “gagarumin karan-tsaye ne ga dokar yaɗa labaru ta ƙasa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Shigar Da Sabbin Tuhume-Tuhume Kan Nnamdi Kanu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta sake shigar da kara kan tuhume-tuhume bakwai da ta yi wa gyara kan Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar msu neman kafa Biyafra, IPOB da ke tsare. Ƙarar da aka yi wa kwaskwarima mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015, wanda aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja na dauke da tuhume-tuhumen da a baya kotun ta amince da su. Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu ya ke tsare hannun DSS, a yayin da ya ke mamba na haramtaciyyar…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Janye Hukuncin Da Ta Zartar Kan Shugaban EFCC

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da ya samu shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa da laifin raina kotu. Mai shari’a Chizoba Oji ce ta ya yi watsi da hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafin da shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ya shigar. Kotun ta ce ta gano cewar ba za a iya cewa shugaban na EFCC ya raina kotu a lokacin da aka yanke hukuncin ba, kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda…

Cigaba Da Karantawa

Za A Rage Yawan Fursunoni A Gidajen Yari – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce tana son ƙara rage yawan fursunonin da ke cikin gidajen gyara hali da ke faɗin ƙasar domin rage cunkoso. Mai bai wa Ministan harkokin cikin gida shawara kan harkokin watsa labarai Sola Faure ne ya tabbatar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ministan wato Rauf Aregbesola ya aika takarda ga gwamnonin ƙasar domin neman haɗin kansu. Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola ya bayyana cewa yana so ya tattauna da gwamonin ƙasar domin sakin aƙalla kashi talatin cikin ɗari na fursunonin da…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Motar Tirela Ta Hallaka Mutane Da Dama A Jimeta

Labarin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka bayan da wata babbar motar dakon kaya ta kufce ta faɗa kan mutane a garin Jimeta. Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa mutum 11 ne suka mutu nan take sakamakon hatsarin. Sai dai shugaban Hukumar kare afkuwar haɗurra ta Najeriya reshen jihar Adamawa ya ce gaba ɗaya mutane 15 ne lamarin ya rutsa da su. Ya ƙara da cewa sun…

Cigaba Da Karantawa