Buga Takardun Kudi: Babu Gaskiya A Maganar Obaseki – Ministar Kudi

Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin da Gwamnan Jihar Edo ya yi cewa ta buga Naira biliyan 60 ta zuba cikin kudaden kasafin da ta ke rabawa a watan Maris. Ministar harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta karyata Gwamna Obaseki, a lokacin da ta ke wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa. Minista Zainab ta kara da cewa ikirarin Obaseki abin takaici ne kuma abin haushi, saboda ko kadan ba gaskiya ba ne. “Wannan ikirari da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi ni dai a bangare…

Cigaba Da Karantawa

Hukumar EFCC Ta Saki Okorochas

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta sako tsohon gwamnan jihar Imo, kuma Sanata a yanzu Rochas Okorocha bayan ya yi kwanaki biyu a hannunta yana amsa tambayoyi. Hadimin Okorocha, wanda ya yi magana da Daily Trust a wayar tarho ya ce an sako tsohon gwamnan misalin karfe 5.45 na yamma kuma a halin yanzu yana gidansa da ke Maitama a Abuja. Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar na yaki da rashawa, Wilson Uwujaren ya ce a bashi lokaci kafin ya yi…

Cigaba Da Karantawa

Bashi Na Dab Da Durkusar Da Najeriya – Sanusi

Tsigaggen Sarkin Kano kuma Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi, ya bayyana cewa tulin basussukan da Najeriya ta ciwo a kasashen waje idan aka kwatanta da 2011 zuwa 2021, to ya rubanya yawan kudin shigar da Najeriya ta samu sau 400. Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano mai murabus, ya nuna tsananin damuwa kan irin gudun famfalakin ciwo bashin da Najeriya ke yi, wanda ya ce abin ya yi munin da zai iya jefa kasar a cikin ramin da samun wanda zai iya ceto ta, sai an sha wahalar sosai.…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Taya Ɗangote Murnar Cika Shekaru 64

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote murnar cika shekaru 64, inda ya bayyana wadannan shekarun a matsayin masu albarka sannan ya yi addu’ar ƙarin lafiya da kyakkyawan cigaba a gareshi. A cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya bayyana Dangote, wanda ya cika shekaru 64 a ranar Asabar, a matsayin babban abokin tarayya kuma “Jarumin yakin Korona” wanda ya ci gaba da nuna cikakken imani da kasar Najeriya. Buhari ya lura cewa duk…

Cigaba Da Karantawa

An Shiga Takun Saƙa Tsakanin Ɗangote Da Isiyaka Rabi’u

Kamfanin BUA mallakar sanannen ɗan kasuwar nan Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabi’u ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya. Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana’antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saɓa tsarin sukari na Najeriya (NSMP). Tsarin NSMP wani shiri ne da aka yi a 2013 na tabbatar da cewa Najeriya ta samu isasshen sukari da…

Cigaba Da Karantawa

Al-Mundahana: EFCC Ta Sake Gayyatar Yari

Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon gwamnar jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya bayyana gabanta ranar Alhamis domin amsa wasu tambayoyi. Hukumar ta umarci Yari ya bayyana a ofishunta dake Sokoto domin amsa tambayoyi. Idan ba a manta hukumar ta gayyaci tsohon gwamnan a watan Faburairu ofishinta dake Legas, inda ya bayyana ya shafe awowi ya na amsa tambayoyi. Ko a wancan lokacin an bukaci Yari ya amsa tambayoyin kokarin canja wa wasu biliyoyin naira wuri dake dankare a wani asusun bankin kasar nan. Hukumar ta tsare Yari na wani lokaci mai…

Cigaba Da Karantawa

Ba Za Mu Yafe Bashin Da Muke Bin Najeriya Ba – Bankin Bada Lamuni

A daidai lokacin da ɗimbin bashi ya yi wa Najeriya tarnaki a wuya, Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da zata yafewa bashin da take bi. Zuwa yanzu Hukumar ta ware wasu kasashe 28 da zata yafewa bashin, inda za’a yi amfani da wasu kudi da aka ajiye na ko ta kwana wajen biyawa wadannan kasashen bashin da hukumar ke binsu. Kasashen da aka yiwa yafiyar dai sune, Afghanistan, Benin, Burkina Faso, Burundi, Central African Republic, Chad, Comoros, Democratic Republic of the Congo,…

Cigaba Da Karantawa

Hukumar Yaƙi Da Rashawa Na Bincikar Masarautar Kano

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya ta ce tana gudanar da binciken masarautar Kano kan badakalar sayar da wasu filaye a unguwannin Gandun Sarki da Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale. Shugaban hukumar Muhiyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa BBC cewa tun lokacin sarki na baya hukumar ta hana a sayar da filayen duk da cewa akwai takarda da masarautar ta bayar da dama a yi amfani da wurin domin gudanar da wasu abubuwa da za su kawo ci gaba. Ya kuma…

Cigaba Da Karantawa

Korona: An Yi Kira Ga Buhari Ya Binciki Gwamnan Kogi

Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil’adama da saka ido kan al’amuran kuɗi (SERAP) ta roƙi shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da Naira Biliyan 4.5 kuɗin tallafin korona a Jihar Kogi. Gwamnatin tarayya ta tura ma gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 4.5 da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don yaƙi da cutar COVID-19, kamar yadda aka ake wa sauran Jihohi. SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar inda ta roƙi shugaba Buhari da yaba Ministan shari’a…

Cigaba Da Karantawa

Ya Zama Dole A Kara Kuɗin Litar Mai A Najeriya – NNPC

Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa ko bajima ko badade sai an sayi lita daya ta man fetur naira 234, domin ana sayarwa ne naira 162 a yanzu, saboda gwamnati na biyan naira bilyan 120 kudin tallafin fetur, wato ‘subsidy’ a duk wata. Shugaban NNPC Mele Kyari ne ya bayyana haka a wani taron musamman na kwamitin da shugaban kasa ya kafa. Ya ce a duk lokacin da aka sayar da litar fetur naira 162, to NNPC ke cika sauran gibin kudaden, wanda dimbin asara ce kawai gwamnati ke dibgawa. Kyari…

Cigaba Da Karantawa

A Shirye Nake In Ajiye Muƙamina – Shugaban EFCC

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya yi magana game da abin da zai sa shi ya bar kujerar da yake. Daily Trust ta rahoto cewa Mista Abdulrasheed Bawa ya sha alwashin yin murabus daga shugaban EFCC idan aka bukaci ya yi abin daa ya saba doka. Da aka yi hira da Abdulrasheed Bawa a wani shiri a gidan talabijin na NTA na kasa, ya bayyana cewa zai bi doka wajen duk aikin da zai yi a kujerarsa ta EFCC. Bawa ya ce…

Cigaba Da Karantawa

Naira 234 Ya Kamata A Sayar Da Litar Mai Ba 162 Ba – NNPC

Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin tarayya na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur. Kyari ya fadi hakan ne a taro na musamman da ministoci ke yi wa maneman labarai bayani karo na biyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Najeriya a Abuja. An ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ‘ƴan ƙasar su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Bada Umarnin Tura Wa Matasa Kudade A Bankuna

Ma’aikatar kwadago da ayyukan yi ta Najeriya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin fitar da makudan kudi domin soma biyan ‘yan Najeriya 774,000 da suka yi rijistar shirin SPW na tallafin korona. Karamin ministan kwadago Festus Keyamo ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter ranar Asabar. Ya ce nan ba dadewa ba wadanda suka yi rijistar shirin za su fara jin kararrawa a asusunsu na banki mai nuna alamun tallafin ya shigo. Kuma a cewarsa, za a yi amfani da lambar BVN ta banki…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban EFCC Ya Buƙaci Ma’aikatan Banki Su Bayyana Kadarorin Su

Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC ta umarci ma’aikatan banki da su bayyana kadarorinsu da suka mallaka ta kuma bada wa’adi zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021. Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya ce sun tattauna kan kokarin da hukumar ke yi na kawar da laifukan kudi a kasar. Bawa ya bayyana cewa an dauki matakin ne don duba rawar da bankuna ke takawa wajen rike…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Farashin Mai

LABARI MAI DADIBabban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rage farashin mai zuwa N100 kan kowace lita, kamar yadda Jaridar Vanguard News ta ruwaito. A cewar Enang, gwamnatin tarayya ta kuma kammala shirye-shiryenta na gudanar da taron kasa kan hada aikin matatar mai ta zamani domin inganta karfin aikin da kuma rage farashin albarkatun mai. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Farashin Mai

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rage farashin mai zuwa N100 kan kowace lita, kamar yadda Jaridar Vanguard News ta ruwaito. A cewar Enang, gwamnatin tarayya ta kuma kammala shirye-shiryenta na gudanar da taron kasa kan hada aikin matatar mai ta zamani domin inganta karfin aikin da kuma rage farashin albarkatun mai. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar…

Cigaba Da Karantawa

Satar Ibori: Kuɗin Da Birtaniya Ta Dawo Da Su Na Jihar Delta Ne – Majalisa

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da kudi fam miliyan 3.4 da aka dawo dasu daga Burtaniya da tsohon Gwamnan Jihar James Ibori ya sace mallakar gwamnatin jihar Delta ne, ba Gwamnatin Tarayya ba. Majalisar wakilan ta nemi gwamnatin tarayya ta hannun ministan kudi da ta dakatar da rabon kudin da aka kwato a hannun tsohon gwamnan Delta, cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba. Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan kudirin da ‘yan majalisa guda tara karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Ndudi Elumelu, suka…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Farashin Man Fetur

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rage farashin mai zuwa N100 kan kowace lita, kamar yadda Jaridar Vanguard News ta ruwaito. A cewar Enang, gwamnatin tarayya ta kuma kammala shirye-shiryenta na gudanar da taron kasa kan hada aikin matatar mai ta zamani domin inganta karfin aikin da kuma rage farashin albarkatun mai. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan lamuran Neja Delta, Ita Enang ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar…

Cigaba Da Karantawa

Karbar Dala: Kotu Ta Amince Ganduje Ya Sauya Lauya

Babbar kotun jihar Kano ta amince a zaman ta na jiya Litini cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauya shaidu da lauyoyin da ke kare shi a shari’ar da ake yi a tsakaninsa da dan jarida Jafar Jafar, mai wallafa jaridar Daily Nigerian ta intanet. Tun a ranar 10.11.2020 Gwamna Ganduje ya nemi hakan amma lauyan Jafar Jafar ya nuna rashin amincewarsa. Sai dai a zaman kotu na Litinin din nan alkali Suleiman Baba Namalam ya ce Gwamna Ganduje na da ‘yancin da zai iya sauya shaidu da lauyoyin nasa.…

Cigaba Da Karantawa

Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Lantarki Kurkuku

Tsohon karamin ministan wutar lantarki na Najeriya, Muhammad Wakil, zai zauna a gidan yari har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2021 bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja. Ana zargin Wakil da almundahanar kudade har biliyan N27 wanda aka ware domin biyan tsoffin ma’aikatan NEPA hakkinsu na murabus. Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ce ta gurfanar da Wakil a ranar Litinin a kan zarginsa da ake yi da laifuka biyu, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa. An gurfanar da…

Cigaba Da Karantawa