2023: Tabbas Tinubu Ne Shugaban Kasa – Kingibe

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne shugaban kasar Najeriya na gaba a babban zaben da za a yi na shekarar 2023. Bola Tinubu dai shine ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwaninta da ya gudana a Eagle Square a ranar Laraba, 8 ga watan Yunin shekarar da muke ciki. Jigon na APC kuma babban jagoran Jam’iyyar ya samu kuri’u 1,271 inda ya kayar da sauran abokan karawarsa su…

Cigaba Da Karantawa

Takara: Wankin Hula Zai Kai Ahmed Lawan Dare

Idan ba a manta ba Sanata Ahmed Lawan shugaban majalisar Dattawa ya fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC rabar 8 ga watan Yuni. Kafin zaɓen an yi masa kyakyawar zaton cewa shina jam’iyyar ta ke so ta tsayar ɗan takarar ta amma kuma hakan bai yiwu ba. An ruwaito cewa wanda yayi nasara a zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Bashir Machina ya ce ba zai sauka daga kujerar takara ba.

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Bukaci Jama’a Su Guji Siyasar Kabilanci – Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa

A yayin da ake gudanar da bikin ranar dimukuradiyya a Najeriya an kira yi ‘yan Najeriya da a daina siyasar kabilanci, ɓangaranci dama addini domin cigaban dimokuraɗiyya harma da cigaban Najeriya baki daya. Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a lokacin zantawarsa da wakilinmu a Yola Fadar gwamnatin jihar Adamawa. Alhaji Ibrahim yace ya kamata ‘yan Najeriya suyi karatun ta nutsu wajen daina siyasar kabilanci ko bangaranci dama addini wanda acewarsa yin siyasar kabilanci ba zai haifawa dimokuraɗiyya ɗa mai ido ba.…

Cigaba Da Karantawa

Nasarawa: Rashin Cika Alkawari Ya Sa Deligates Fito Na Fito Da Dan Takarar Sanata

Daga Ishaq Saeed Hamza Kimanin makwannin biyu ke nan da kammala zaben fidda gwani na ɗan kujerar sanata mai wakiltar Nasarawa ta yamma kujerar da shugaban jamiyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya bari bayan zama shugaban jamiyyar APC na kasa. ‘Yan siyasa uku ne suka yi hankoron samun nasarar gadar Abdullahi Adamu da suka hada daHonorabul Aliyu Wadada (Sarkin Yaƙin Keffi)Honorabul Arch Shehu Tukur (Sarkin Fadan Keffi)Hon Barr. Labaran Magaji (Matawallen Toto). Kafin akai ga zaben fidda gwanin Honorabul Aliyu Wadada ya sanar da janye takararsa ‘yan awanni…

Cigaba Da Karantawa

INEC Ta Yi Watsi Da Dan Takarar Sanatan APC A Akwa-Ibom

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta yi watsi da zaben fidda gwanin da ya samar da Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takarar kujerar sanata Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma karkashin jam’iyyar APC. Akpabio, wanda ya janye daga takarar shugabancin kasa yace a zabi Tinubu a zaben fidda gwanin APC, an bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na kujerar sanatan Akwa Ibom a ranar Alhamis. Kamar yadda sakamakon sake zaben ya nuna, Akpabio ya yi nasara inda ya samu kuri’u 478, yayin da DIG…

Cigaba Da Karantawa

Jahadin Dake Kan ‘Yan Najeriya Shi Ne Kawar Da APC – Atiku

Dan takarar shugaban kasa na Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga yan Najeriya da su fatattaki jam’iyyar All APC daga mulki a babban zaben 2023 mai zuwa domin dawo da Najeriya cikin hayyacinta. Atiku ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, a cikin sakonsa na ranar dimokradiyya, yana mai cewa hakan shine babban jahadi kuma abin da za a iya sakawa jaruman dimokradiyyan kasar nan da shi. Dan siyasar ya yi imanin cewa wannan bukin lokaci ne da dukkan masu…

Cigaba Da Karantawa

Ranar Dimukuradiyya: Ku Mallaki Katin Zabe Domin Zabar ‘Yan Takara Na Kwarai – Ramalan

Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe domin samun nasarar zaɓar ‘yan takarar da suka dace a zaɓen dake tafe na 2023. Ramalan ya yi wannan kiran ne a sakon murnar ranar dimukuradiyya ta bana 12 ga Watan Yunin Shekarar 2023. Shugabàn Kamfanin na ATAR ya bayyana ranar Dimukuraɗiyya a matsayin wata rana mai muhimmanci a Najeriya sannan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Nijeriya…

Cigaba Da Karantawa

2023: Babu Matsala Idan Tinubu Ya Dauki Mataimaki Musulmi – Kayode

Tsohon Ministan Sufurin sama, Femi Fani-Kayode yace zai goyi bayan dan takaran shugaban kasan jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, koda ya zabi mataimaki Musulmi. Kayode ya bayyana hakan ne yayin hira a shirin ‘Politics Today’ na tashar ChannelsTV ranar Alhamis. Yace sam ba zai yiwu ace za’a cire addini daga cikin siyasa ba: “Matsala ne kuma wajibi ne mu yi wa mutane bayani idan muka yanke shawarar yin haka. Ba ni da matsala idan aka yi haka (Musulmi da Musulmi). idan dan takarar mu Tinubu ya zabi hakan zamu goya…

Cigaba Da Karantawa

INEC Ta Tura Karin Na’urorin Rijistar Zabe A Jihohi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta ce ta yanke shawarar tura ƙarin na’urorin yin rajistar zaɓe a wasu jihohi saboda cunkoso da ake samu a wuraren da ake ƙorafe-ƙorafe. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce ta lura cewa an fi samun cunkoson a jihohin Kano da Legas da kuma yankin Kudu maso Gabas, inda ta tura ƙarin na’urorin 209. “Hukumar za ta ci gaba da sa ido kan aikin na tsawon kwanaki sannan ta sake duba ci gaban da aka samu,” a…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Adawa Suka Hanani Aiki Sosai – Gwamnan Kogi

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce kararrrakin da ‘yan adawa suka kai shi kotu lokacin da ya lashe zaben gwamna a karon farko su ne suka hana shi aiki sosai a jihar. Ya bayyana haka ne a cikin shirin A Fada A Cika, na gidan Rediyon BBC Hausa. Gwamna Yahaya Bello ya ƙara da cewar “Nasarar da muka samu a karo na biyu ta fi ta shekara hudu da muka yi a baya… mun yi aiki sosai amma saboda an kai mu kotu, an raba mana hankali. “Shari’u ashirin…

Cigaba Da Karantawa

Fidda Gwani: Osinbajo Ya Shiga Rudani Bayan Shan Kaye

Mataimakin Shugaban ƙasa Osinbajo ya yi warwas a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC inda tsohon ubangidansa kuma jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu kuri’u 1,271 kuma ya tabbata ‘dan takara shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a APC. Kafin zaben, masu nazarin al’amurra sun yi ittifakin cewa ta yiwu Osinbajo ya sha wuya tunda a bayyane ya kalubalanci tsohon ubangidansa, jigon siyasar kasar Yarbawa kuma ‘dan takarar da yayi nasarar samun tikitin APC. Kin goyon bayansa a bayyane da Buhari ya yi A yayin da ya…

Cigaba Da Karantawa

Nasarar Tinubu Alama Ce Ta Samun Karbuwa A Arewa – Ganduje

Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya taya Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, murnar samun nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyya mai mulki ta APC. A cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren watsa labarai na gwamnan ya fitar, na bayyana Ganduje ya ce nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa da ƙasa baki daya. Gwamnan na Kano kuma ya ce nasarar ta Tinubu za ta karfafa jam’iyyar kuma…

Cigaba Da Karantawa

NNPP Ta Tsayar Da Kwankwaso Takarar Shugabancin Kasa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a ranar Laraba. Kwankwaso ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasar na NNPP ne bayan daligets 774 daga jihohi 36 sun sahale masa gaba daya ba tare da hamayya ba. Idan za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar na NNPP na kasa, Boniface Aniegbonam, ya ce Kwankwaso shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ka Da Kuyi Gangancin Sake Zabar PDP – Wasiyyar Buhari Ga ‘Yan Najeriya

Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su tabbata ba su bar jam’iyyar adawa ta PDP “ta mayar da ƙasa baya ba”. Da yake jawabi a wurin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta sauya Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa. “Wajibi ne mu zaɓi masu adalci ‘yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu…don ciyar da ita gaba. “Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba.” Zuwa lokacin haɗa wannan…

Cigaba Da Karantawa

Babban Abin Da Zan Aiwatar Da Zarar Na Yi Nasara – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga filin Eagles Square dake birnin tarayya Abuja inda ake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC na bayyana cewar, ɗan takarar shugabancin kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abin da zai aiwatar da zarar ya yi nasarar lashe zabe. A cewarsa, a shirye yake da ya soma aiki daga ranar farko da ya zama shugaban ƙasa, ba tare da ɓata wani lokaci ba domin lalubo mafita. Ya bayyana cewa shi mai ɗaukar abubuwa da gaske ne kuma bai zo…

Cigaba Da Karantawa

2023: Ni Nafi Kowa Cancantar Zama Shugaban Kasa – Ahmad Lawan

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar Dattawa kuma ɗan takarar Shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar APC Ahmed Lawan, ya bayyana cewar shi ne ya fi kowa cancantar zama shugaban ƙasa a shekarar zaɓe ta 2023. A cewarsa, ya shekara 23 a majalisa kuma a cewarsa yana da ƙwarewar da zai jagoranci Najeriya. Ya bayyana cewa ko a ƙasashen da suka ci gaba, akwai da dama daga cikin waɗanda suka zama shugaban ƙasa da ƴan majalisa ne inda ya ce hakan ya sa ya…

Cigaba Da Karantawa

Janyewar ‘Yan Takara Ga Tinubu Alamun Nasara Ne – Ganduje

Mai girma Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa janyewar da ‘yan takara suke don mara wa Bola Ahmed Tinubu baya alamu ne cewa ɗan takarar tasu zai yi nasara. Ganduje ya faɗi hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a filin Eagle Sqaure, inda taron jam’iyyaer APC ke gudana yanzu haka. “Wannan alamar nasara ce kuma ka ga yadda kowa yake murna saboda ɗan takararmu Bola Tinubu ya fi sauran ‘yan takara cancanta”.

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Najeriya Ne Suka Zabi Buhari Ba Mutum Guda Ba – Fadar Shugaban Kasa Ga Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Miliyoyin ‘yan Najeriya ne suka fito ƙwai da ƙwarƙwarta sukazaɓi Buhari ya shiga ofishin shugaban ƙasa a shekarar 2015. Babu wani mutum ɗaya da zai yi ikirarin cewa shi ya taimaka wa Buhari ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2015, a cewar fadar ta shugaban ƙasa. Fadar shugaban ƙasa ta yi wannan kalaman ne yayin martani ga ikirarin jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu dake ikirarin shine silar zaman Buhari Shugabàn ƙasa. A wata…

Cigaba Da Karantawa

Takarar Ahmad Lawan: Buhari Ya Yi Harshen Damo

Labarin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a ƙaƙaba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ba, za a kasa kowa ya ɗauka. A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari ya fitar, Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da gwamnonin APC na yankin Arewa suka yi da shi. Kalaman shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa…

Cigaba Da Karantawa

2023: APC Na Dab Da Zama Tarihi – Atiku

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ‘Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce wa jam’iyya mai mulki dubunta zai cika a zaben 2023. Atiku ya ce jam’iyya mai mulki ta APC ta gaza bayyana damuwarta game da wadanda ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a Owo, jihar Ondo yayin da gaba daya kasar ke cikin jimami. Sannan ta gaza fasa gabatar da taro da ‘yan takarar shugaban kasarta a ranar da aka kai harin, inda ya…

Cigaba Da Karantawa