Gayyatar Yariman Saudiyya Jana’izar Sarauniya Ya Haifar Da Surutai

Gayyatar da Birtaniya ta yi wa Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman zuwa jana’izar Sarauniya ya janyo zanga-zanga daga masu rajin kare hakkin bil-adama. Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu wajen kisa tare da daddatsa gawar dan jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya. Sai dai a lokuta da dama Yariman na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya musanta wannan zargi da ake yi masa tare da…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Ziyarci Amurka Yau Lahadi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi taro kasar Amurka yau Lahadi. Buhari zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da za a gudanar a birnin New York na ƙasar ta Amurka. A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya ce shugaban zai gabatar da jawabi a ranar Laraba a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.

Cigaba Da Karantawa

Tafiyar Atiku Turai Ta Haifar Da Surutai

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar awanni kadan bayan sanar da tafiyar ɗan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Abubakar Abubakar zuwa turai wani taro mai muhimmanci surutai sun karaɗe Jama’a. Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, Atiku zai tafi turai ne domin halartar wani zama na harkallar kasuwancinsa. Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da hadimin Atiku, Mazi Paul Ibe ya fitar ya ce mai gidan nasa zai tafi turai bayan kammala wani zama da masu ruwa da tsaki na…

Cigaba Da Karantawa

Gumurzun Boko Haram Da ISWAP Ya Bar Tulin Gawarwaki

Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar an yi wata arangama tsakanin Kungiyar Boko Haram da tsagen kungiyar karkashin ISWAP. Rahotanni sun bayyana cewar lamarin fafatawar ya yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandoji daga ɓangaren kungiyoyin ta’addan biyu masu gaba da juna. Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno. Wata majiyar tsaro ta ce Kwamandojin Boko Haram da tawagarsu na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro: An Gano Bakin Zare Tun Da An Fara Shiga Daji Kisan ‘Yan Bindiga – El Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasiru Ahmed El-rufa’i na Jihar ya ce shawarar da su ka dade su na ba gwamnatin tarayya ta kutsawa daji don kashe ‘yan-bindiga, wadda sai yanzu gwamnati ta fara aiki da ita, yanzu cikin takaitaccen lokaci matsalar tsaro ta yi sauki. Gwamnan wanda ke jawabi ga kungiyar ‘yan-kasuwa a ranar Alhamis a gidan gwamnati, ya ce indai jami’an tsaro za su ci gaba da shiga daji don farautar ‘yan-bindiga to kwananan za a kawo karshen matsalar tsaro. El-rufa’i ya…

Cigaba Da Karantawa

Ambaliyar Ruwa: Manoman Jihar Adamawa Sun Bukaci Agajin Gwamnati

Manoma a Jihar Adamawa sun bukaci gwamnatin tarayya da jihar da su taimaka musu biyo bayan ambaliyar ruwa da yayi sanadiyar salwantar gonakinsu da dama tare da yin asarar dukiyoyi masu yawa. Shugaban Kungiyar manoma na Yankore dake Jambutu a cikin karamar hukumar Yola ta Arewa fadar gwamnatin jihar Adamawa, Alhaji Abdulrazak Abubakar ne yayi wannan kira a zantawarsa da Wakilinmu a Yola. Abdulrazak Abubakar yace ambaliyar ruwa yaci musu gonaki da dama tare da gidaje don haka ya zama wajibi su kirayi gwamnatin tarayya dana jihar da suyi wa…

Cigaba Da Karantawa

Dalilin Da Ya Sa Nake Tikar Rawa Da Waka A Gidan Gala – Tahir Fagge

Shahararren Dan wasan kwaikwayo Mai Suna Alhaji Tahir Fagge ya Bayyana cewa Dole Ce ta Sanya shi fitowa a cikin wata Waka da aka Ganshi Yana taka rawa da wata yarinya awajen Wani Gala. Tahir Fagge yace ya shiga mawuyacin Hali sakamakon jarrabawa da Allah yayi Masa na Rayuwar Sa. “Yace ya kasance Cikin mawuyacin hali Kuma Babu yadda zaiyi sakamakon yadda wasu Mutane suka Gaza fahimtar halin da yake ciki na rashin lafiya. “Bani da kudin da Ake bukata a ASibiti Kuma sau dadama wasu mutane basa iya taimakon…

Cigaba Da Karantawa

Masarautar Kano Ta Nada Sheikh Aminu Daurawa Limanci

A ranar Alhamis 15/9/2022, Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero, ya amince da nadin babban Malamin addinin musulunci Sheik Ibrahim Daurawa, a matsayin sabon limamin masallacin juma’a na makarantar Skyline University, dake cikin birnin Kano. Malam Daurawa wanda ya yi fice wajen hidimta wa musulunci da karantar da al’umma addini. Mutane daga kowanne bangare suna masu nuna farin cikinsu tare da fatan alkhairi domin an ajiye Kwarya a gurbinta. Ni Indabawa Aliyu Imam ba ni da Malamin da nake kauna da amfanuwa da shi sama da Malam Daurawa.…

Cigaba Da Karantawa

2023: Jonathan Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Zaben Tumun Dare

Rahoton dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya shawaci ‘yan Najeriya kan irin shugabannin da ya kamata a ce sun zaba a zaben 2023 mai zuwa. Jonathan ya bayyana wannan batu ne jim kaɗan bayan ganawa da tsoffin shugabannin Najeriya biyu na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar a birnin Minna na jihar Neja. Da yake bayyana shawararsa, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su maida hankali su zabi shugabannin da za su yi…

Cigaba Da Karantawa

Kama Tukur Mamu Ba Zai Shafi Ceto Sauran Fasinjoji Ba – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta ce kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani a kokarin sakin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, ba zai kawo cikas ga yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na kubutar da sauran fasinjojin da suka rage a hannun ‘yan bindiga ba. Ministan kula da harkokin ‘yan sanda na kasar Mohammed Maigari Dingiyadi ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi a Abuja ranar Alhamis. “Ina ganin masu maganar sun…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar PDP Ta Sha Mummunan Kaye A 2023 – George

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya gargadi jam’iyyar hamayyar cewa za ta iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. George, ya yi gargadin cewa PDP tana iya rabuwa biyu Jam’iyyar PDP ta Arewa da Jam’iyyar PDP ta Kudu, idan shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ki yin murabus kamar yadda aka buƙaci hakan tun farko. “Bari in fadi karara cewa shugaban jam’iyya na kasa da dan takarar shugaban kasa bai kamata…

Cigaba Da Karantawa

Fitinar ‘Yan Bindiga: Mata A Gombe Sun Yi Zanga-Zanga

Labarin dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar wasu matan daga garin Filiya, a karamar hukumar Shongom ta Jihar a ranar Laraba sun yi zanga-zangan lumana bayan kisan da ake zargin makiyaya suke yi wa mazan su. Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar an kashe mutum 11 sannan an kona gidaje 11 a harin baya-bayan nan a Kushi. Matan da suka yi zanga-zangan sun rufe hanyar zuwa garin suna cewa sun aikata hakan ne don nuna damuwa, sun kuma ce ba su gamsu da matakan…

Cigaba Da Karantawa

Shugaban Hukumar Ayyukan ‘Yan Sanda Musiliu Smith Ya Aje Aiki

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar kula da ayyukan yan sandan Najeriya, PSC, Musiliu Smith ya yi murabus daga aikinsa, an ruwaito cewa kwamitin hukumar ne ta bukaci Smith ya yi murabus kuma ya amince. Wani majiya mai tushe ya shaidawa majiyarmu ta Jaridar Daily Trust cewa Smith, tsohon sufeta janar na yan sanda, zai mika mukamin ne ga tsohon alkali Clara Ogunbiyi da ke wakiltar bangaren shari’a a hukumar. Hukumar ta rika kai ruwa rana da ofishin sufeta janar na yan sanda…

Cigaba Da Karantawa

An Biya Diyyar Wadanda SARS Suka Ci Zarafinsu

Rahoton da muke samu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar kare hakkin dan adam a Najeriya, ta biya kusan dala dubu 700 diyya ga mutanen da ‘yan sanda suka azabtar da kuma ci zarafinsu. Wasu da ga cikin mutane 58 da aka biya diyyar iyalai ko ‘yan uwan wadanda aka zabtar ne ko kuma sune da kansu. Hakan ya biyo bayan bincike a kan korafe-korafen da iyalan wadanda aka azabtar suka yi in da suke zargin jami’an ‘yan sanda da kisan da shari’a ba ta amince da shi…

Cigaba Da Karantawa

Ina Mamakin Yadda ‘Yan Najeriya Ba Su Ganin Kokarin Gwamnatinmu – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da yadda mutane ba sa fita suna yabawa da ƙwazon gwamnatinsa, duk kuwa da ɗumbin ayyukan raya ƙasa da yake ikirarin cewa tana aiwatarwa. Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a jihar Imo, lokacin da ya kai wata ziyarar aiki ta kwana guda,a ranar Talata. Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya karbi ragamar mulkin Najeriya a wani lokaci da kasar ta samu kanta a tsaka mai wuya. Adadin man da…

Cigaba Da Karantawa

Tsaro A Arewa: Gwamnoni Sun Yi Kiran Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 da sarakunan gargajiya a yankin sun yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulki na 1999, don samar da yan sandan jihohi. BBC ta rawaito cewa, a cewarsu wannan ne kadai zai sa a shawo kan matsalar tsaro da yankin ke fama da ita dama kasa baki daya. Yankin Arewacin na Najeriya ya jima yana fama da matsalar yan fashin daji, da satar mutane don neman kudin fansa, da sauran nau’o’in ayyukan ta’addanci. Kungiyar gwamnonin arewa ta NGF, da ta sarakunan gargajiya (NTRC)…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Shugaban Dillalan Mai Ya Yi Kiran Hadin Kai Don Fuskantar Zaben 2023

A yayin da aka fuskanci fara gangamin neman zabe domin gudanar da babban zaben shekara ta 2023 an kirayi ‘yan Najeriya da su kasance masu hada kansu a koda yaushe da kuma nesanta kansu da yin siyasar ɓangaranci ko addini domin samun haydin kan kasa da wanzar da zaman lafiya a faɗin Najeriya baki daya. Shugaban kungiyar Dillalan Man fetur na kasa IPMAN shiyar Jihohin Adamawa da Taraba Alhaji Dahiru Buba ne ya bayyana haka a zantawarsa da Wakilinmu a Yola. Alhaji Dahiru Buba yace hadin kai a tsakanin al’umma…

Cigaba Da Karantawa

Zan Haskaka Najeriya Idan Na Lashe Zabe – Atiku

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023. Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a a birnin Ikko na Jihar Legas. Da yake bayyana kadan daga manufofinsa, ya ce ya shirya tsaf don tabbatarwa da inganta tattalin arzikin Najeriya matukar ya gaji Buhari a shekarar 2023. A bangare guda, Atiku ya koka…

Cigaba Da Karantawa

Kaduna: Dakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Dakarun rundunar sojoji na 1 Division sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga tare da kama wasu da dama a ranar Litinin. Mai magana da yawun rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a shafin Twitter na rundunar a ranar Talata. A cewar sanarwar, GOC na 1 Division, Nigerian Army, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ne ya jagoranci tawagar da ta kai samamen tare da hadin gwiwan wasu kwamandoji. Nwachukwu ya ce: “Dakarun sojoji…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya: An Damke Wanda Ya Yi Wa Sarauniyar Ingila Aikin Umrah

Mahukunta a Saudiyya sun kama wani mutum wanda ya tafi Makka takanas don yin Umara a madadin Sarauniya Elizbeth ta II. A ranar Litinin ne mutumin, wanda dan asalin kasar Yemen ne ya wallafa bidiyonsa a babban masallacin Makka yana dawafi. A cikin bidiyon ya rubuta cewa na sadaukar da Umarar da na yi ga Sarauniya Elizebeth ta II, ya ce yana addu’ar Allah Ya yafe mata kura-kuranta. An dai yada bidiyon a kafafan sada zumuntar Saudiyya inda mutane suka rinka kira a shafukansu na Tiwita da a kama shi.…

Cigaba Da Karantawa