Gwamnatin Tarayya Za Ta Mallaki Kadada Dubu 720 A Kowace Jiha – Nanono

Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin mallakar sama da kadada dubu 720,000 daga jihohi daban-daban don inganta amfanin gona, Ministan Noma da Raya Karkara, Alh. Sabo Nanono ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a wata ganawa da ya yi da shugabannin gudanarwa na maaikatu da kuma manyan jami’an gudanarwa na Ma’aikatar aikin Gona ta tarayya da raya Karkara a Abuja. Ya ce ma’aikatarsa ​​ta tanadin fili tsakanin kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha da nufin bunkasa bangaren noman kasar nan. Gwamnatin Tarayya za ta mallaki kadada dubu…

Cigaba Da Karantawa

2022: Za A Haramta Shigo Da Madara Najeriya

Gwamnatin Nijeriya Za Ta Haramta Shigo Da Madara Daga Shekarar 2022, domin inganta kayayyakin haɗin cikin gida yadda Najeriya zata tsayu da ƙafafuwan ta, ta wannan ɓangare. Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya yi bayanin cewa ma’aikatarsa na shirye-shirye domin tabbatar da samar da kayayyaki don samar da madara a dukkanin fadin kasar. Da wannan dalilin ne gwamnatin tarayya za ta haramta shigo da madara cikin kasar daga shekarar 2022. Nanono ya bayyana hakan ne a yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja, a wani taro kan…

Cigaba Da Karantawa

Najeriya Ce Gaba Wajen Noman Shinkafa A Afirka – Ministan Noma

Ministan harkokin noma da cigaban karkara, Muhammad Sabo Nanono ya bayyana cewa akwai abubuwan da za su sa kasar ta yi murna da zuwan rana irin ta yau, 1 ga watan Oktoba, wato ranar bikin ‘yancin kai duk da irin kalubalen da ake fuskanta a Najeriya, nasarorin da aka samu a Najeriya sun cancanci ayi murna. “Ina yi maku murna ‘yan Najeriya na cika shekaru 60 da samun ‘yanci a kasarmu. Murnar samun ‘yancin-kai abu ne da ya kamata ayi farin-ciki.” Ministan harkar noman ya kara da cewa dole ayi…

Cigaba Da Karantawa

Babban Bankin Najeriya Ya Raba Tallafin Bashin Noma A Neja

A ƙoƙarin bunƙasa harkar noma a Najeriya. Babban bankin ƙasa (CBN) haɗin guiwa da gwamnatin Jihar, ta raba tallafin bashin kayan noma ga manoman shinkafa sama da ɗari biyar a garin Kontagora dake Jihar Neja. Bashin kayan noman waɗanda suka haɗa ba, buhun shinkafa, buhunan takin zamani, maganin feshi, injimin ban ruwa, injimin feshi. Domin bunƙasa harkar noman shinkafa a cikin ƙasa. Ƙaddamarwar wanda ya gudana a jiya alhamis ƙarƙashin jagorancin babban bankin Najeriya, da wakilcin Ƙungiyar manoma shinkafa ta ƙasa (RIFAN) da wakilin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Neja Alhaji…

Cigaba Da Karantawa

Tallafin Biliyan 600 Ga Manoma: Kayan Aiki Zamu Raba Ba Kuɗi Ba – Ministan Noma

Ministan harkokin noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar narka biliyan N600 a harkar noma domin farfrado da bangaren. Nanono, tsohon manomi daga jihar Kano, ya ce za a narkar da kudaden ne a kan kananan manoma domin tabbatar da yalwar abinci da dorewar hakan a fadin kasa. Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai kamfanin sarrafa takin zamani da hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kammala ginawa a jihar Legas. Kazalika, Nanono ya gana da sauran ma su kamfanonin…

Cigaba Da Karantawa

Tallafin Biliyan 600 Ga Manoma: Kayan Aiki Zamu Raba Ba Kuɗi Ba – Nanono

Ministan harkokin noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kashe biliyan N600 a harkar noma domin farfrado da bangaren. Nanono, tsohon manomi daga jihar Kano, ya ce za a narkar da kudaden ne a kan kananan manoma domin tabbatar da yalwar abinci da dorewar hakan a fadin kasa. Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai kamfanin sarrafa takin zamani da hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kammala ginawa a jihar Legas. Kazalika, Nanono ya gana da sauran ma su kamfanonin…

Cigaba Da Karantawa

Manoma Sun Arce Da Bashin Babban Bankin Najeriya

Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba su ka yi batan dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga Babban Bankin Najeriya CBN a Shekarar da ta gabata. Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafan Najeriya, shiya jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan inda yace Manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noman rani, sannan aka neme su daga baya domin biyan bashin aka rasa. A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan. Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace…

Cigaba Da Karantawa

Manoma Sun Arce Da Bashin Babban Bankin Najeriya

Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba su ka yi batan dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga Babban Bankin Najeriya CBN a Shekarar da ta gabata. Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafan Najeriya, shiya jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan inda yace Manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noman rani, sannan aka neme su daga baya domin biyan bashin aka rasa. A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan. Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace…

Cigaba Da Karantawa