Fitaccen Jarumi Adam ZANGO ya bayyana damuwar sa da cewa ” Nayi aure banji Dadi ba matukar wanann itama tasa muka rabu tabbas na hakura ba zan sake yin wani aure ba a rayuwata, zan zauna ni kadai sabida na gaji da yadda nake tsintar kaina duk da nasan kaddara ta ce hakan. Jawabai da dama ne suka fito Daga Bakin fitaccen Jarumi Adam ZANGO yayin da yake zubar da hawaye da Kuma nuna halinda yake ciki na rashin samun lokacinsa da matarsa Bata dashi sai business dinga kawai tasa…
Cigaba Da KarantawaCategory: Nishadi
Nishadi
Burina In Jefar Da Rera Waka In Koma Rera Alkur’ani – Ali Jita
Sanannen Mawaƙin finafinan Hausa Ali Isa Jita ya bayyana cewar babban burin da yake dashi a yanzu shi ne jingine waƙa da komawa tilawar Kur’ani. Mawaƙin ya bayyana wannan aniyar tasa ne a tattaunawar da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin daga bakin mai Ita. Ali Jita ya ƙara da cewar dukkanin wata nasara da Mawaƙin zamani ke nema a ƙasar Hausa Allah ya bashi, bisa ga haka yana matuƙar godiya da fatan sauya Alƙiblar rayuwa a nan gaba. Sai dai jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin…
Cigaba Da KarantawaFina-Finai: Jarumi Ahmad S. Nuhu Ya Cika Shekaru 16 Da Rasuwa
A ranar 1 ga watan 1 na shekarar 2023, fitaccen jarumin masana’antar Kannywood Marigayi Ahmad S. Nuhu ya cika shekaru 16 da rasuwa. Ya rasu a ranar 1 ga watan 1 na shekarar 2007 a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar sa ta zuwa Maiduguri tare da wasu abokan sa su 3, wato Abubakar Didos, Hamza da kuma Ahmad Singa Boy. Wadda kuma Singa Boy din ne kawai ya rage a raye, amma su ragowar Ukun duka sun rasu. Ya rasu ya bar matar sa,…
Cigaba Da KarantawaAkwai Gyara A Harkar ‘Yan Kannywood – Adam Zango
Shahararren dan wasan Hausa fim na masana’atar Kannywood Adam Zango ya bayyana cewar da akwai gyara a yadda harkar ta su ke tafiya a halin yanzu da ya kamata a ɗauki matakin gyara. Adam Zango na bayani ne a yayin mayar da martani dangane da sukar da malaman addini da sauran jama’a ke yi musu na bata tarbiyya maimakon gyaranta. Jarumin ya ce tabbas idan har ɓera da sata babu shakka daddawa ma ta wari, yadda harkar ‘yan fim ke tafiya a yanzu abin takaici ne, an kai ga matsayin…
Cigaba Da KarantawaFina-Finai: Marigayi Ibiro Ya Cika Shekaru Takwas Da Rasuwa
An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne ya shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan kwaikwayo. Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar Fim a tun ya na aji uku na makarantar sakandare. Ya na…
Cigaba Da KarantawaDuniyar Fina-Finai: Jaruma Halima Atete Za Ta Amarce
Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar fitacciyar Jarumar Kannywood Hajiya Halima Atete za ta amarce a Kwanan nan. Tauraruwar Kannywood Halima Yusuf Atete za ta amarce da angonta Mohammed Mohammed Kala wadanda za a daura aurensu ranar Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri. A ‘yan lokutan nan dai ana yawan samun yin aure na Jaruman Kannywood lamarin da jama’a ke gani wata alama ce da Jaruman na Kannywood musamman Mata za su yi bankwana da Masana’antar zuwa gidan Aure.
Cigaba Da KarantawaFina-Finai: Ina Nan Da Raina Ban Mutu Ba – Kamaye
A safiyar ranar jiya ne wani labari ya karade shafukan sada zumunta ana fadin cewa Allah yayiwa fitaccen Marubucin nan kuma darakta haka kuma a lokaci daya jarumi a masana’antar kannywood Dan Azumi Baba wanda akafi sani da Kamaye rasuwa. Jaruman Kannywood da dama sun wallafa hakan,wasun su sun karyata kansu daga baya,yayin da wasu kuma suka cire wallafar ba tare da bada wani ba’asi ba. Bayan mun gudanar da bincike ne muka tabbatar muku da cewa yana nan a raye cikin koshin Lafiya. Haka kuma shima jarumin da kansa…
Cigaba Da KarantawaDalilina Na Daina Rubuta Shirin Fim Din Labarina – Birniwa
Shahararren marubucin fina-finan Kannywood Ibrahim Birniwa ya ce ya daina rubuta fitaccen fim ɗin Labarina mai dogon zango saboda rashin jituwa tsakaninsa da masu shirya shi da kuma aiki kan nasa fim ɗin. Duk da cewa rashin jituwa ce ta sa marubucin ya fita daga fim ɗin, sai dai ya ƙi faɗa wa BBC Hausa ainahin abin da ya faru, yana mai cewa “da ni nake rubuta fim ɗin da zuwa yanzu ya zo ƙarshe”. Da yake magana ta cikin shirin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa na BBC a ƙarshen…
Cigaba Da KarantawaKano: Tinubu Ya Gwangaje Kannywood Da Kyautar Miliyan 50
Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya gwangwaje masana’antar Kannywood da gudumawar N50 miliyan domin cigaban masana’antar. Mujallar fim ta ruwaito cewa, Tinubu ya bayar da wannan makudan kudaden ne a yayin da ya halarci taro na musamman da ‘yan fim suka hada masa a daren Lahadi a fadar gwamnatin jihar Kano. A yayin jawabi kan manufar taron, Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ya ce: “Wannan taron na matasan fim ne masu goyon…
Cigaba Da KarantawaDalilin Da Ya Sa Nake Tikar Rawa Da Waka A Gidan Gala – Tahir Fagge
Shahararren Dan wasan kwaikwayo Mai Suna Alhaji Tahir Fagge ya Bayyana cewa Dole Ce ta Sanya shi fitowa a cikin wata Waka da aka Ganshi Yana taka rawa da wata yarinya awajen Wani Gala. Tahir Fagge yace ya shiga mawuyacin Hali sakamakon jarrabawa da Allah yayi Masa na Rayuwar Sa. “Yace ya kasance Cikin mawuyacin hali Kuma Babu yadda zaiyi sakamakon yadda wasu Mutane suka Gaza fahimtar halin da yake ciki na rashin lafiya. “Bani da kudin da Ake bukata a ASibiti Kuma sau dadama wasu mutane basa iya taimakon…
Cigaba Da KarantawaKano: Kotu Ta Bada Umarnin Kama Mawaki Ado Gwanja
Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar wata kotun shari’a ta umurci hukumar yan sanda ta damke sanannen mawaƙi Ado Gwanja da wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan koyawa matasa rashin tarbiyya a kafafen ra’ayi da sada zumunta, wani jami’in kotun ya bayyanawa AFP ranar Alhamis. Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon jiya bayan lauyoyi sun shigar da kara inda suka bukaci hukunta Ado Gwanja da ire-irensa bisa wakokin rashin tarbiyya da daurawa a yanar gizo, jami’in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan.…
Cigaba Da KarantawaHar Yanzu Ban Samu Namijin Da Ya Yi Mini Ba – Jarumar Fina-Finai
Fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure. A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta ba wa ‘danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci. Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, ta bayyana yadda take kula da ‘danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba. “Ba abun wasa…
Cigaba Da KarantawaAn Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon A Kotun Shari’a Ta Kaduna
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta sanin ma’aikacin nan ɗan shekara 48, Bala Musa, wanda ya yi ikirarin ta masa alƙawarin aure. Jarumar wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ranar Talata, ta faɗa wa Kotun cewa ba ta san mutumin da ake magana a kan shi ba. Da take jawabi ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a harabar Kotun, Gabon ta musanta tuhumar da ake mata baki ɗaya inda…
Cigaba Da KarantawaMagidanci Ya Maka Hadiza Gabon Kotu Saboda Kin Aurensa
Wani maigidanci mai kimanin shekara 48 ya maka jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Hadiza Gabon, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna saboda ta ki amincewa ta aure shi. Maigidancin, mai suna Bala Musa, wanda ma’aikacin gwamnati ne ya shaida wa kotun cewa sun jima suna soyayya da jarumar, bisa alkawarin za ta aure shi, amma ta ci gaba da yaudarar shi. Bala ya ce, “Ya zuwa yanzu, na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta tambaye ni kudi na kan kashe mata ba bata lokaci cikin fatan…
Cigaba Da KarantawaFina-Finai: Gwamnatin Kaduna Za Ta Gina Fim Village
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar babban sakataren hukumar KADIPA na jihar Kaduna, Khalil Nur Khalil ya cigaba da kokarin ganin an gina kauyen shirya wasan kwaikwayo wato’Fim Village’. A wani jawabi da ya fito daga shafin KADIPA a dandalin Twitter a ranar Alhamis, an fahimci gwamnatin Kaduna tana nan a kan aikin ‘Film Village’ domin bunkasa rayuwar matasa. Khalil Nur Khalil ya hadu da wakilan KCTA, shugabar Fasaha Café, Joseph Ike, da fitacciyar ‘yar wasar kwaikwayo, Rahma Sadau a kan wannan shirin. Shugaban na KADIPA…
Cigaba Da KarantawaNa Yi Nadamar Shiga Rikicin Zango Da Ali Nuhu – BMB
Jarumin fina-finan Hausa, wanda furodusa ne kuma darakta, Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da BMB, ya bayyana shirinsa na dawowa sana’ar fim da sauran abubuwa dangane da rayuwarsa ta ilimantarwa. A tattaunawar da Daily Trust ta yi da BMB, ya fara da gabatar da kansa inda ya ce: “Sunana Bello Muhammad Bello, an fi sani da General BMB. Ni furodusa ne, darekta ne, jarumi sannan mai rubuta labari kuma na tashi ne a cikin rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato. Kuma na yi makarantar…
Cigaba Da Karantawa‘Ya’yan Sarkin Kano Na Neman Rayuwata – Tsohuwar Jarumar Kannywood
Tsohuwar jarumar Kannywood, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Ibrahim, na neman agajin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam da sauran jama’a kan halin ha’ula’in da ta ke ciki Lokacin da ta ke fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, sunan ta Maijidda Ibrahim, yanzu kuma Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero. Ta na ɗaya daga cikin ɗimbin mata ‘yan fim da su ka yi aure kuma su na zaune a gidan miji. Tsawon shekaru 21 kenan tun da tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Khusufi saboda wani fitaccen…
Cigaba Da KarantawaMutuwa Ta Dauke Jarumar Kudanci A Coci
Labarin dake shigo mana daga Jihar Enugu na bayyana cewar Likitoci a asibitin East Side a Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar jarumar fina-fina ta Nollywood, Chinedu Bernard. Ta yanke jiki ta fadi ne a yayin da ta ke aikin tsaftace coci na St. Leo the Great Catholic Church da ke rukunin gidajen Tarayya a jihar. Faston cocin, Rabaran Fada Uchendu Chukwuma, da wasu masu ibada a cocin, sun garzaya da ita asibitin a inda aka tabbatar ta rasu. A cewar wani rubutu da daya daga cikin masu aiki a…
Cigaba Da KarantawaJaruma Ummi Rahab Za Ta Amarce
Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar manuniya tana nuna cewa jarumi kuma mawaki sannan mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya na gab da auren jarumar da ke haska fim din, Ummi Rahab. A makon da ya gabata rade-radin ya karu bayan jarumar ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta na Instagram, inda ta kira shi da “Masoyinta kuma mijinta kuma Aljannarta.” A karkashin rubutun na ta kamar yadda Aminiya ta nuna, mutane sun dinga tsokaci iri-iri har Ali Artwork yana cewa: “Insha…
Cigaba Da KarantawaAlmajiranci: Fati Slow Ta Goyi Bayan Sarkin Waƙa
Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci. Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa. A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take…
Cigaba Da Karantawa