An Samar Da Maganin Ciwon Zazzabin Lassa A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar da ke inganta tsirrai da dabbobi ta Najeriya ta ce ta yi nasarar samar da maganin zazzabi Lassa, wanda ke halaka al`umma a wasu kasashen Afirka, ciki har da Najeriya. Zazzabin Lassa dai ba shi da wani magani sadidan, cuta ce wacce ta daɗe tana kisa a Najeriya wadda aka tabbatar da ɓeraye ne ke haddasa ta. Amma yanzu hukumar ta ce jami`anta sun gano maganin, bayan shafe shekara shida suna gudanar da bincike, kuma a halin da…

Cigaba Da Karantawa

Likitoci Sun Bukaci Sanya Hannu A Dokar Kare Hakkin Mata

Ƙungiyar likitoci masu lura da lafiyar mata ta ƙasa ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya sanya hannu kan dokar kare lafiyar mata da jarirai. A cewar ƙungiyar hakan zai zamo wani abin tarihi, wanda al’ummar ƙasar ba za su manta da shi ba. Shugaban ƙungiyar, Dr Habib Sadauki ne ya buƙaci hakan a wata ganawa da ya yi da manema labarai ranar Lahadi. Sadauki ya ce dokar za ta taimaka wajen rage mutuwar mata masu juna-biyu da jarirai. Ya ƙara da cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da…

Cigaba Da Karantawa

Lalacewar Makaratu: Malaman Jinya Da Anguwan Zoma Sun Yi Zanga-Zanga A Taraba

BASHIR ADAMU, JALINGO. Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Taraba yanzu na cewa, biyo bayan cigaba da tabarbarewan da Makarantar koyar da Jinya da Anguwan Zoma na Jihar Taraba wato (Taraba State College of Nursing and Midwifery) na zaman Makokin Sati guda saboda tsananin lalacewar da Makarantan tayi da zaman alhini bayan shekaru biyar da rasuwan wanda ya gina Makarantan don cigaban Al’umman Jihar Taraba, Marigayi Danbaba Danfulani Suntai. A cewan Malaman Makarantar, zaman makokin Sati gudan da suka fara shine don Addu’a dauki daga wurin Ubangiji Allah daya kawo…

Cigaba Da Karantawa

Arewa Maso Yamma Na Fama Da Gagarumar Matsalar Rashin Lafiya – Likitocin Duniya

Kungiyar likitocin duniya ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ce arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar gagarumar matsalar kiwon lafiya. Kungiyar ta ce kananan yara masu dimbin yawa suna fuskantar matsalar tamoiwa. MSF ta bayar da kulawa ga kananan yara 100,000 da ke fama da tamowa tun daga farkon shekarar nan, tana mai cewa kimanin yara 17,000 suna bukatar kulawar asibiti. Kungiyar ta kara da cewa taimakon da ake bai wa yaran ya yi matukar kadan, domin kuwa an mayar da hankali kan yankin arewa maso gabashin kasar inda ake…

Cigaba Da Karantawa

NAFDAC Ta Gargadi Masu Bleaching

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC, ta gargadi ‘yan kasar da su ƙaurace wa amfani da kayan kwalliyar da kan sauya fatar jikin bil adama daga baƙa zuwa fara. Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Olusayo Akintola ya aike wa manema labarai ranar Lahadi. NAFDAC ta umarci a kama da gurfanar da wadanda suke tallata wannan sinadari ba tare da sahalewar hukumomin kasar ba. Ta ce an haramta…

Cigaba Da Karantawa

‘Yar Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ta Roki ‘Yan Najeriya Koda

Sonia, diyar sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda. Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta. An kama Ekweremadu da matarsa a watan Yuni lokacin da suke kokarin samawa Sonia gudunmawar koda daga wani matashi a birnin Landan, an gurfanar da ma’auratan a gaban kotu kan zargin safarar mutum da kokarin cire wani sassa na jikin karamin yaro da bai balaga ba. Daga…

Cigaba Da Karantawa

Kyandar Biri: Hukumar Lafiya Ta Kalubalanci ‘Yan Luwadi Su Rage Barbara

Hukumar Lafiya ta Duniya ta shawarci maza da ke neman ‘yan uwansu maza da su rage yawan abokan mu’amular tasu, domin takaita yaduwar cutar kyandar biri. Ta kuma nemi su dinga musayar bayanai game da su. Kashi 98 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar maza ne masu neman maza ‘yan uwansu. WHO ta ce an bayar da rahoton mutum 18,000 a kasashe 78 da suka kamu, galibi a kasashen Turai. An samu mutuwar mutum biyar. Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce za a iya dakatar da cutar…

Cigaba Da Karantawa

Bullar Sabuwar Cuta: NCDC Ta Shiga Bincike

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wata baƙuwar cuta da ta ɓulla a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar. Rahotanni na cewa a makon da ya gabata wani ɗalibi ya mutu tare da kwantar da wasu tara a asibiti sakamakon cutar a yankin Boji-Boji na Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas. Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, NCDC ta ce tana sane da wata cuta da aka…

Cigaba Da Karantawa

Har Yanzu Korona Na Kisan Jama’a – Hukumar Lafiya

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargaɗin cewa jerin waɗanda suka kamu da cutar korona na nuna cewa har yanzu ba a kuɓuta daga annobar ba. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce cutar na ci gaba da yaɗuwa, don haka akwai buƙatar ƙasashe su ɗauki matakan ɗakile ta. Ya ce, ya damu da yadda ake samun ƙaruwar kamuwa da cutar korona. Wannan lamari yana ƙara takura tsarin kiwon lafiya dake cikin matsi, da ma su ma’aikatan lafiyar. Yana jawabi ne a wajen taron kwamitin na WHO, wanda ya yanke hukuncin…

Cigaba Da Karantawa

Zukar Taba Na Hallaka ‘Yan Najeriya 30,000 Duk Shekara – Hukumar Lafiya

Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Walter Mulombo ya bayyana cewa sama da Yan Najeriya 30,000 ne suke mutuwa a duk shekara sakamakon cututtukan da ke da alaƙa da shan taba sigari. Ya bayyana haka ne a Abuja a yayin wani taro da aka shirya na yaƙi da shan taba. Mulombo ya ce mutanen da taba sigari ke kashewa ya zarta na waɗanda korona ta kashe a Najeriya inda ya ce taba na kashe mutum ne a hankali.

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: An Daga Darajar Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Yola Zuwa Asibitin Jami’a

Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana jira daga ƙarshe shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da cibiyar kiwon lafiya ta tarayya dake Yola wato FMC Yola da ta zama asibitn koyarwa na Jami ar Modibbo Adama dake Yola. Darakta yada labarai na ofishin Sakataren gwamnatin tarayya Mr Willie Bassey ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Amincewar dai ta biyo bayan bukatar al’umma jihar ta Adamawa tare da gwamnatin jihar wanda hakan zai taimaka wajen horas da Likitoci har ma da inganta kiwon lafiya…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Najeriya Ta Janye Dokar Korona

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama’a a tarukan bikin aure da na waƙe-waƙe waɗanda aka saka da zimmar yaƙi da annobar korona. Kwamatin yaƙi da cutar na shugaban ƙasa ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a ƙasar. Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan ɓullar annobar cikin ƙasar a watan Fabarairun 2020. Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar haɗarin…

Cigaba Da Karantawa

Sama Da Mutum 120 Na Goga Wa Cutar Kanjamau – Wata Budurwa

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana yawan mutanen da ta shafa wa cutar kanjamau bayan ta gano tana da cuta mai karya garkuwar jiki a shekarar 2016. Ta yi wannan bayanin ne a Twitter bayan wata ma’abociyar amfani da Twitter ta sanar da yadda take rayuwa da cutar tsawon shekaru uku bayan ta same ta. Ta bayyana cewa ta samu cuta mai karya garkuwar jikin yayin da take da shekaru 21 a duniya kuma yanzu shekarunta 24. “Na samu cutar kanjamau inda da shekaru 21 kuma yanzu shekaru na 24…

Cigaba Da Karantawa

Za A Fara Biyan Mata Masu Juna Biyu Albashi A Jigawa

Rahotanni daga Dutse babban birnin Jihar Jigawa na bayyana cewa Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa komai ya kankama don fara biyan mata masu juna biyu sama da 5000 kudi dubu biyar-biyar a duk wata. Mataimakain Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar. Namadi yace jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna karkara don su rika zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa. Ya ce gwamnatin Muhammad Badaru ta sanya wannan kudi cikin kasafin…

Cigaba Da Karantawa

Cutar Lassa Ta Zama Annoba A Najeriya – Masana

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Masana na ci gaba da nuna damuwa kan rahoton da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta fitar, wanda ta ce mutum 96 sun kamu da cutar zazzabin Lassa cikin kananan hukumomi 27 a jihohin kasar. Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, kwarraren likita ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sahida wa BBC cewa adadin ka iya wuce haka idan aka fadada bincike. Likitan ya ce,”Akwai tashin hankali saboda idan da har za a zurfafa bincike to ko shakka ba…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Korona Ta Kama Ministan Abuja

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Abuja Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona. Mai magana da yawun ministan, Abubakar Sani ne ya tabbatar wa BBC da hakan. A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa bayan ya ji alamun rashin lafiya, ya yanke shawarar yin gwaji wanda bayan gwajin aka tabbatar da ya kamu da cutar. Ministan ya ce a halin yanzu lafiyarsa ƙalau amma yana jin ƙaiƙayi a maƙogwaronsa da kuma jin zazzaɓi da…

Cigaba Da Karantawa

Korona Za Ta Zama Tarihi A Shekarar 2022 – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa tana da yaƙinin cewa za a magance annobar korona a shekarar 2022 matuƙar ƙasashe suka haɗa kansu suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa. Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan inda ya ce a halin yanzu akwai abubuwan da ake amfani da su domin kare kai da kuma maganin korona amma a cewarsa, iƙirarin kishin ƙasa da kuma ɓoye rigakafi da wasu ƙasashe ke yi ne ya haddasa ɓullar sabon nau’in Omicron na korona. Mista Tedros ya…

Cigaba Da Karantawa

Kimanin ‘Yan Najeriya 100 Cutar Lassa Ta Kashe A 2021 – NCDC

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a yayin da annobar korona ke ci gaba ratsa sassan Najeriya, sabon rahoton hukumar NCDC ya nuna cewa zazzaɓin Lassa ya halaka mutum 92 a shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya ce ya zuwa lokacin rahoton Mako na 50, jumillar mutum 454 ne suka harbu da zazzaɓin a ƙaramar hukuma 66 da ke jiha 16 na faɗin Najeriya da kuma Abuja babban birnin ƙasar. Jiha uku daga ciki da suka haɗa da Edo (197) da Ondo (159) da Taraba (21)…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Gagari Korona – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga Fadar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ce shugaban ƙasar lafiyarsa ƙalau bayan an samu rahoton cewa makusantansa sun kamu da cutar korona a ƙarshen mako. Mai magana da yawun fadar Femi Adesina ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi. Da aka tambaye shi ko Buhari ya killace kansa sai ya ce: “Ina ganin shugaban ƙasa lafiyarsa ƙalau, yana ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba. Amma idan wani na kusa da…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Sabuwar Korona Ta Yi Babban Kamu A Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sabuwar nau’in cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami’an gwamnati suka kamu da cutar. An bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar. Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. Hakazalika akwai…

Cigaba Da Karantawa