Iran Ta Damke Shahararriya Jarumar Fina-Finan Kasar

An kama tauraruwar fim Taraneh Alidoosti a Iran yayin da zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin ƙasar da ake yi ta shiga wata na huɗu. Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce an kama jarumar ne bayan ta wallafa wani sako da hukumomi suka kira na ƙarya da kuma ƙokarin tunzira masu zanga-zanga a shafinta na sada zumunta. Shahararriyar da ta samu lambobin yabo da dama ta yi Allah-wadai da hukuncin kisan da aka yanke wa wani mai zanga-zanga a farkon watan nan. A makonnin baya, ‘yar fim ɗin ta sanya wani…

Cigaba Da Karantawa

Jajirtaccen Shugaba: Kasar Guinea Bissau Za Ta Karrama Buhari

Gwamnatin Guinea Bissau za ta karrama shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da lambar girmama mafi a kasar. Za ta karrama shugaba Buharin ne bisa la’akari da gudummuwar da yake bayarwa wajen daidaitawa da bunkasa demokuradiyya a shiyyar Afirka ta yamma. Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoko Embalo shi ne zai lika wa shugaba Buharin lambar yabon, a wani gagarumin biki da aka shirya a kasar. Wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban Najeriya a kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar ta ce gwamnatin Guinea Bissau din ta yanke…

Cigaba Da Karantawa

Miliyoyin Yara Na Fuskantar Yunwa A Kasar Habasha – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce mummunan fari da ba taɓa gani ba cikin gomma shekaru ya jefa miliyoyon yara cikin matsalar rashin abinci da ruwan sha a ƙasar Habasha wato Ethiopia. A wani saƙo da UNICEF ɗin ya wallafa a shafinsa Tuwita ya ce da yawa daga cikin yaran na cikin hatsarin mutuwa sakamakon cutar cutar Tamowa. Yankin gabashin Afirka na fama da mummnan farin da ba a taɓa gani ba cikin gwamman shekaru, bayan da aka kwashe damina biyar ba tare da samun…

Cigaba Da Karantawa

Abin Da Na Shaidawa Sarki Charles A Ziyarar Da Na Kai – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a lokacin ganawa da Sarki Charles na III, a fadar Buckingham ya shaida masa cewa ba shi da gida kan sa a Burtaniya. A lokacin ganawa da ‘yan jarida bayan ganawa da sarkin mai shekara 73, ya ce sarkin ya tambaye shi ne ko yana da gidan kansa a Burtaniya. Buhari ya ce makusudin ziyara ita ce tattaunawa kan alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da diflomasiyya. Ya ce an tsara ganawar ta su ce a baya a Kigali tun kafin ya zama sarki,…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: Ukraine Ta Gargadi Iran Kan Goyon Bayan Rasha

Gwamnatin kasar Ukraine ta gargaɗi da kakkausan harshe ga ƙasar Iran da cewa ‘asarar’ da za ta tafka sakamakon goya wa Rasha baya a yaƙin da take a Ukraine ya fi ‘ribar’ da za ta samu na yin hakan. Gargaɗin na zuwa ne bayan da a karon farko Iran ta amince cewa ta sayar wa da Rasha jirage marasa matuƙa, to sai dai tana mai cewa ta yi hakan ne tun kafin fara yaƙin Ukraine. Ƙasashen yamma na zargin Rasha da amfani da jirage marasa matuƙa na Iran wajen kai…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: Adadin Wadanda Suka Mutu A Turmutsitsin Koriya Sun Doshi 200

Mutum aƙalla 154 ne suka mutu ranar Asabar a birnin Seoul na Koriya ta Kudu sakamakon turereniyar da ta faru a bikin Halloween, a cewar ‘yan sandan birnin. Cikin mutanen da suka mutu, 98 mata ne da kuma maza 56. ‘Yan sanda sun tantance 153 daga cikinsu kuma sun sanar da iyalansu, kamar yadda rahoton kamfanin labarai na Yonhap ya ruwaito. Ana ci gaba da tantance mamaci ɗaya, yayin da wasu 133 suka ji raunuka, a cewar hukumar kashe gobara.

Cigaba Da Karantawa

Duniya Na Cikin Yanayi Mafi Muni A Tarihi – Shugaban Rasha

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce duniya bata taba samun kanta cikin mawuyacin hali ba tun bayan yakin duniya na biyu kamar a wannan karon. A jawabinsa Putin ya zargi kasashen Yamma da kokarin tursasa wa duniya siyasarsu da al’adunsu. Ya ce kasashen Turan suna so kowa ya bi salon yadda suke gudanar da rayuwa ko yana so ko baya so, wanda kuma hakan a cewarsa mulkin mallaka ne. Putin ya ce su ne suka haddasa yakin da ke faruwa a Ukraine, kuma yana da yakinin a karshe Amurka da…

Cigaba Da Karantawa

Sudan Za Ta Binciki Musabbabin Rikicin Hausawa Da Kabilun Kasar

Hukumomin sojin kasar Sudan sun kaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rigingimun da suka haddasa kashe-kashe a jihar Blue Nile da ke kudancin kasar. Shafin intanet na kafar yaɗa labaran ƙasar wato Suna ya ruwaito cewa rikicin ya yi sanadiyyar rayuka kusan 200 tare da raba dubbai da muhallansu. Kashe-kashen ya biyo bayan rikici tsakanin Hausawa da wasu ƙabilun ƙasar, wanda ya ƙara zafafa a makon da ya gabata. Mai magana da yawun sojin kasar kanar Nabil Abdullah ya ce kwamitin da aka kafa zai yi…

Cigaba Da Karantawa

Sama Da Mutum 200 Aka Kashe A Rikicin Hausawa Da Kabilun Sudan

Rahoton dake shigo mana daga birnin Khartum na kasar Sudan na bayyana cewar Hukumomi a kasar ta Sudan sun ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin ƙabilanci da ake yi a kudancin kasar tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berta ya ƙaru zuwa 200. Wani shugaban al’umma a Jihar Blue Nile ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyuwa uku, inda ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su taimaka wajen binne gawarwakin wadanda suka rasu. Rahotanni na cewa rikici tsakanin Hausawa da Berta ya ɓarke ne kan gonaki. A…

Cigaba Da Karantawa

Dubai Ta Dakatar Da Ba ‘Yan Najeriya Biza

Hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ‘yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A wata sanarwa da suka aike wa kamfanonin shirya tafiye-tafiye a Najeriya ranar Juma’a, hukumomin kasar ta UAE sun ce ”duka takardun neman izinin biza da aka cike an dakatar da su yanzu”. An ruwaito gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba. Ta kuma…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: Matan Kasar Kenya Na Mutuwa A Saudiyya

Mata ‘yan ƙasar Kenya 85 da ke aiki a ƙasashen waje akasari Saudiyya ne suka mutu a cikin wata uku da suka gabata, kamar yadda wani ɗan siyasa ya faɗa wa majalisar dokokin kasar ta Kenya. Gidan Talbijin na Citizen a kasar ya ambato Alfred Mutua, wanda a yanzu ake tantance shi a majalisar dokokin kasar domin nada shi a matsayin ministan harkokin kasashen waje ya kuma ce an tasa keyar wasu matan kasar kimanin 1000 zuwa kasar daga Saudiyyar. Mafi yawan matan kasar Kenya kan tafi kasar Saudiyya da…

Cigaba Da Karantawa

Birtaniya Ta Sanya Ranar Bada Sanda Ga Sarki Charles III

Za a yi shagalin bikin nadin sarautar Sarki Charles III a ranar Asabar 6 ga watan Mayun 2023. Za a yi shagalin ne a Westminster Abbey, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar. Takardar da iyalan gidan sarautar suka fitar mai taken, “Nadin sarautar Mai Martaba Sarki.” Takardar tace: “Fadar Buckingham na farin cikin sanar da cewa za a yi nadin sarautar Mai Martaba Sarki a ranar 6 ga watan Mayun 2023. “Za a yi nadin sarautar a Westminster Abbey dake Landan kuma Archbishop na Canterbury ne zai jagoranci nadin’. “A…

Cigaba Da Karantawa

Babu Imani A Harin Da Rasha Ta Kai Ukraine Da Makami Mai Linzami – Amurka

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kaddamar ranar Litinin zuwa wasu yankuna na Ukraine, sun nuna irin ‘rashin imanin’ Vladimir Putin kan haramtaccen yakin da yake yi a Ukraine. Yana mai zargin Rasha da kashe tare da raunata fararen hula masu dimbin yawa, ya kara da cewa kasarsa na tare da al’umar Ukraine. Ya nanata kiran Rasha da ta gaggauta kawo karshen wannan yaki, tare da janye dakarunta daga Ukraine. Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce ya kadu matuka…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: Morocco Ta Halasta Noman Tabar Wiwi

A ranar Laraba ne hukumar kasar Morocco ta ba da izini 10 na farko don amfani da tabar wiwi a masana’antu, magunguna da kuma fitar da su zuwa kasashen waje. Hukumar ta ce manoman da su ka kafa ƙungiyoyi a yankunan Al Houceima, Taounat da Chefchaouen ma su tsaunuka sannu a hankali za a ba su damar noman wiwi domin yin kasuwanci bisa matakin doka . An riga an noma tabar wiwi a Marocco ba bisa ka’ida ba, kuma sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: Morocco Ta Halasta Noman Tabar Wiwi

A ranar Laraba ne hukumar kasar Morocco ta ba da izini 10 na farko don amfani da tabar wiwi a masana’antu, magunguna da kuma fitar da su zuwa kasashen waje. Hukumar ta ce manoman da su ka kafa ƙungiyoyi a yankunan Al Houceima, Taounat da Chefchaouen ma su tsaunuka sannu a hankali za a ba su damar noman wiwi domin yin kasuwanci bisa matakin doka . An riga an noma tabar wiwi a Marocco ba bisa ka’ida ba, kuma sabuwar dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a…

Cigaba Da Karantawa

Yahudu Da Nasara Ke Daukar Nauyin Masu Bore A Iran – Ayatollah Khamenei

Jagoran addinin Iran ya zargi Amurka da Isra’ila da hannu wurin gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta karade kasar, a jawabin da ya yi kan batun a karon farko. Ayatollah Ali Khamenei ya ce rikakkun makiya Iran ne suka “kitsa” jerin “bore” da zanga-zangar, yana mai zargin cewa an kona Alkur’anai a wuraren boren. Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi damarar fuskantar karin zanga-zangar da za a yi. Zanga-zangar – wadda ta kasance kalubale mafi girma na mulkin da ya kwashe tsawon shekaru yana yi –…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: ECOWAS Ta Yi Tir Da Juyin Mulkin Burkina Faso

Ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi wadarai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso, tana mai bayyana shi da “koma-baya” bayan ci gaban da aka samu. “Ecowas na jaddada rashin amincewarta da ƙwace mulki ba ta hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada ba,” a cewar sanarwar da ta fitar. Ta ƙara da cewa “muna kira da a yi gaggawar komawa kan yarjejeniyar da aka cimma ta mayar da mulki ga farar hula a ranar 1 ga watan Yulin 2024”. Ƙungiyar mai…

Cigaba Da Karantawa

Ketare: An Bayyana Makasudin Mutuwar Sarauniya Elizabeth ll

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar maƙasudin abinda ya haddasa mutuwar Basarakiyar Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta II ya bayyana. A bayanan da ke ƙunshe a takardar shaidar mutuwarta, ya nuna cewa tsufa ne ya yi ajalin Sarauniyar wadda ta lashe shekaru 70 tana mulkin ƙasar ta Birtaniya. A takardar shaidar da National Records of Scotland ta fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, marigayya Sarauniya ta mutu ne da ƙarfe 3:10 na yamma ranar 8 ga watan Satumba, 2022 a Fadar Balmoral,…

Cigaba Da Karantawa

Saudiyya: Sarki Salman Ya Nada Yarima Mai Jiran Gado Mukamin Firaminista

Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ya nada dansa kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ga mukamin firaministan kasar sannan ya nada dansa na biyu Yarima Khalid a matsayin ministan tsaro, kamar yadda wata dokar da Sarkin ya sanya wa hannu ta sanar. Sauyin ya kuma bar Yarima Abdulaziz bin Salman a matsayinsa na ministan makamashi. Ministan harkoki da kasashen waje Yarima Faisal bin Farhan al Saud da ministan kudi Mohammed al-Jadaan da kuma ministan zuba jari Khalid al-Falih sun ci gaba da rike mukamansu. Yarima Mohammed bin…

Cigaba Da Karantawa

Sama Jannati: Saudiyya Za Ta Tura Mace Ta Farko Sararin Samaniya

Hukumar kula da sararin samaniya ta Saudiyya ta ƙaddamar da shirin sama jannati a karon farko da ya haɗa da aika mace ta farko ƴar ƙasar zuwa sararin samaniya a 2023. Shirin zai mayar da hankali ne wajen horar da ƙwararru ƴan asalin Saudiyya don su yi tafiya mai nisan zango da mai gajeren zango a jirgin sama jannati zuwa sarrain samaniyar. Shirin zai bai wa ƴan sama jannati Saudiyya damar aiwatar da binciken kimiyya don ci gaban ɗan adam a ɓangarorin da suka fi muhimmanci kamar lafiya da ci…

Cigaba Da Karantawa