An Kashe Malamai 10 Da Garkuwa Da 50 A Kaduna – Kungiyar Malamai

Kungiyar malaman sakandare a Najeriya reshen Jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun kashe mambobinta malaman makaranta 10 sannan sun yi garkuwa da wasu malamai 50 a fadin kananan hukumomin jihar 23 daga watan Janairu zuwa yanzu. Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnan jihar Nasiru El-Rufai da yayi amfani da ikon da yake da shi domin ceto malaman da kuma sauran wadanda ‘yan bindiga ke ci gaba da tsare wa. Shugaban kungiyar na JIhar Kaduna, Ishaya Dauda ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labara da…

Cigaba Da Karantawa

Sana’ar Gyaran Takalmi Ta Yi Mini Komai – Bello Nasarawa

Muhammad Bello Adamu Nassarawa Dake Karamar Hukumar Chikun a Jihar KadunaMai Sana’ar gyaran Takalmi ne Wanda ya shafe Sama Shekaru 35 Yana wannan Sana’ar yace Sana’ar Gyaran Takalmi wato Shoe Shiner Sana’a ce Mai cike da Rufin Asiri, domin a cikinta yake ci Kuma yake Sha harma da Sauran bukatunsa na yau da Kullum. ya Kara da Cewa wannan sana’a tasa tayi Masa Riga da wando duk da Cewa wasu na Mata kallon sana’a ce ta Kaskanci amma agunsa ba haka abin yake ba. Inda yace da Wannan Sana’ar yayi…

Cigaba Da Karantawa

‘Yan Kasuwa Za Su Fara Cin Gajiyar Dubu 50-50 Duk Wata – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan ‘yan kasuwa a Nigeria. A wannan sabon shirin, a cewar shugaba Buhari, gwamnati za ta dinga tallafawa ‘yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata.Sai dai, gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo ‘yan kasuwan da za su ci moriyar wannan tallafi, kuma ‘yan kasuwar za su fito daga kowanne fanni na kasuwanci. Haka zalika, shugaban kasar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na farfado da tattalin…

Cigaba Da Karantawa

Kwangilar Gas: Najeriya Ta Yi Nasara Akan Kamfanin Birtaniya

Gwamnatin Najeriya ta samu nasarar karin wa’adin lokaci don daukaka kara gaban kotu a shari’ar da ta ke da katafaren kamfanin Birtaniya na P&ID kan kwangilar gas da kamfanin ke zargin kasar da saba ka’idoji. Nasarar da Najeriya ta samu a jiya juma’a gaban kotun Birtaniyar, na nuna cewa ta na da cikakkiyar damar kalubalantar hukuncin watan Agustan bara da ya yi umarnin kwace mata kadarorin da yakai darajar dala biliyan 9 da miliyan 600 da ke matsayin kashi 1 bisa 5 na yawan kudadenta da ke asusun ketare. Cikin…

Cigaba Da Karantawa