Katsina: Masari Ya Sallami Shugaban Jami’ar Umaru Yar’adua

Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Majalisar Zartaswa Jihar Wadda Gwamna Aminu Bello Masari ke Jagoranta ta Amince da Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina Farfesa Sanusi Mamman ya gaggauta Ajiye muƙaminsa, Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan Rahotan da Gwamna ya kafa ne ya ba shi shawara, kan Rahotan da aka gabatar mashi akan Korafe-korafe da aka gabatar akansa. Mai baiwa Gwamna Shawara kan Ilimi mai Zurfi, Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da maanema…

Cigaba Da Karantawa

An Amince Da Koyar Da Yara Karatu Da Harsunan Gida A Makarantu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar ministoci ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan gida wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar. Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka  ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro. Ministan ya bayyana cewa ” ka’idojin koyarwa na shekaru shida na farko a…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Darasin Tarihi A Makarantu

Gwamnatin tarayya ta sanar da dawo da darasin tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a cikin manhajar ilimi na matakin farko a Nijeriya, shekaru 13 bayan an soke shi. Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Abuja, wajen bikin kaddamar da shirin sake koyar da ilimin tarihi da horar da malaman tarihi a matakin farko. Ya nuna damuwar sa da yadda hadin kai a Nijeriya ya yi ƙaranci, inda mutane su ka saka kabilanci a zuƙatansu, inda ya ƙara da cewa rashin samun ilimin…

Cigaba Da Karantawa

Rabin Albashi: ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta yi wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan rikicinta da gwamnatin tarayya da kuma rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata. ASUU ta ce wannan zanga-zanga sun yi ta ne don nuna damuwa ga yadda ake yiwa Malaman rikon sakainar kashi da kuma alanta tsarin ‘ba aiki ba albashi a kansu’, da kuma tursasa su su koma bakin aiki ba tare da samun hakkinsu ba. Kungiyar ta ce, matukar gwamnati ta gaza biya musu bukata,…

Cigaba Da Karantawa

Sulhu Ya Kamaci ASUU Ba Yajin Aiki Ba – Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci kungiyar malaman jami’o’i da sauran kungiyoyin ma’aikata da su rungumi sulhu da gwamnati tare da gudun yajin aiki a matsayin hanyar neman a biya musu bukatu. Buhari ya bayyana hakan ne a taro na 74 na yaye dalibai a jami’ar Ibadan a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba shekarar da muke ciki ta 2022. Shugaba Buhari ya samu wakilcin farfesa Abubakar Rasheed ne a taron, wanda shine babban sakataren hukumar jami’o’i ta kasa (NUC). Buhari ya kuma yaba da kokarin gudunarwar jami’ar Ibadan bisa…

Cigaba Da Karantawa

Ba Za Mu Biya ASUU Albashin Aikin Da Basu Yi Ba – Ministan Ilimi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba. Ministan ilimin Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar. Yayin da…

Cigaba Da Karantawa

Rikicin ASUU: Ya Zama Tilas Buhari Ya Biya Albashin Su – Falana

Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Femi Falana (SAN) ya shawarci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da ya bayar da umarni a biya malaman jami’o’in ƙasar duka albashinsu na wata takwas. Wasu daga cikin malaman Jami’o’in ne dai suka yi ƙorafin cewa an biya su rabin albashinsu a watan Oktoba, maimakon albashin wata takwas da suka yi alkawari da gwamnati gabanin janye yajin aikin. To sai a martanin da gwamnatin tarayyar ta yi ta ce ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar ASUU Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu. A wata tattaunawa da mataimakin shugaban kungiyar da BBC ta yi, Dr Chris Piwuna, ya ce kungiyar na shirin gudanar da taron gaggawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan. ‘’Za mu hadu nan gaba mambobinmu suna mana tambayoyi dole mu hadu mu san amsar da za mu ba su,’’ in ji shi. Malaman na korafi kan yadda…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Biya ASUU Albashin Rabin Wata

Gwamnatin tarayya ta biya Malaman jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, domin rage musu radadin rashin albashi na tsawon watanni takwas da suka shafe suna yajin aiki. Malaman jami’o’i da dama da Wakilinmu ya tuntuba sun tabbatar da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba ne. A bayanin da wani malamin jami’a yayi wa wakilinmu yace ya samu albashin babu zato balle tsammani duk da cewa ba wannan bace yarjejeniyar dake tsakaninsu…

Cigaba Da Karantawa

Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kulle Jami’o’i 62 Na Bogi

Hukumar da ke yaki da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC ta ce ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a fadin kasar. Hukumar ta ce wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, domin kuwa babu wata jiha a fadin kasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta. Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye, ta kai ga gano adadin makarantu da…

Cigaba Da Karantawa

Kano: Malaman Jami’ar Bayero Sun Koma Bakin Aiki

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar malaman Jami’ar Bayero sun koma bakin aiki a ranar Litinin bayan kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta sanar da janye yajin aikin da suka shafe wata takwas suna yi. Dalibai da ma’aikata sun fara shiga jami’ar a ranar Litinin inda suka bayyana farin cikinsu tare da fatan za a fara daukar darasi. Kungiyar dai ta ce ta rubuta wa hukumar jami’ar Bayero Kano cewa malaman sun dawo bakin aiki. Yayin da malaman jami’ar suka janye wannan yajin aiki, ga alama, shirye-shirye…

Cigaba Da Karantawa

Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Daga Comr Abba Sani Pantami Kungiyar malaman Jami’o’i ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi, duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba, amma wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja. Da yake zantawa da wakilin jaridar Punch wata majiya mai cikakken bayani a cikin hukumar ta NEC ta ce, “Eh, an dakatar da shi”. Da aka nemi karin bayani, majiyar ta…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU: Dalibai Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗaliban jami’o’in Najeriya na ci gaba da zanga-zangar lumana a sassan ƙasar daban-daban biyo bayan yadda yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsawon lokaci. Ko a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ɗaliban sun toshe hanyar shiga filin jirgin sama na Murtala Muhammad tare da wasu manyan hanyoyi, wani lamari da ya haifar da cikas ga sufurin jiragen. Hakan dai wani ƙoƙari ne da suke yi domin matsawa gwamnatin ƙasar lamba don ta magance…

Cigaba Da Karantawa

Tsawaita Yajin Aikin ASUU Ya Haifar Da Rudani A Najeriya

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da zazzafar muhawara, musamman a shafukan sada zumunta, dangane da tirka-tirkar da a ke yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, game da kin biyan malaman jami’o’i albashi saboda yajin aikin da suke gudanarwa. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta tsawaita yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar Kungiyar da ke Jami’ar Abuja. Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu, saboda gaza biya mata tarin bukatunta daga bangaren gwamnatin tarayayyar kasar. Hakan ne ya…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU: Ba Za Mu Biya Albashin Watanni Shidda Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ministan ilimi Adamu Adamu ya ce batun biyan malaman jami’o’i albashinsu na tsawon watannin da ba su yi aiki ba shi ne kaɗai abin da ya rage ba a cimma ba a yarjejeniyar ASUU da gwamnati. Minsitan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Sannan Malam Adamu Adamu, ya ce hakkin malaman jami’o’i ne su biya ɗalibai diyya saboda ɓata musu lokacin da suka yi tsawon wata…

Cigaba Da Karantawa

Yajin Aikin ASUU: Zan Kori Dukkanin Malaman KASU – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yayi barazanar sai ya kori duka malaman jami’ar jihar Kaduna KASU, muddin ya bincika ya gano sun shiga yajin aikin da ASUU ke yi. Muryoyi ta ruwaito Gwamnan wanda ke hirar kai tsaye da yan jarida a daren ranar Laraba a Kaduna ya ce a baya ya tsaida albashin ma’aikatan jami’ar amma sai aka shaida masa cewa basu shiga yajin aiki ba “Ma’aikatan jami’ar jihar Kaduna, KASU basu da matsala da Gwamnatin jihar Kaduna domin komi suka nema munyi masu, hakanan duk bukatun ASUU…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: An Shawarci Musulmi Da Yin Addu’a Domin Nasarar Zaben 2023

A yayin da aka fuskanci Babban zaben shekarar ta 2023 an kirayi al’umma Musulmi da su kasance masu yin addu’o’i a koda yaushe domin ganin an kammala zaben lafiya da cigaban kasa baki daya. Shugabar kungiyar Jama’atu Nasaril Islam bangaren mata dake jihar Adamawa Hajiya Amina Bashir ce tayi wannan kira a wajen adu a ta musamman wanda kungiyar ta shirya a Yola. Hajiya Amina tace shirya irin wadannan addu’o’i yana da mutukan muhimanci don haka ya kamata iyaye su kasance masu shirya addu’o’i da su da yaransu domin neman…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Ya Umarci Ministan Ilimi Ya Yi Gaggawar Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi Malam Adamu Adamu da ya kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’in ƙasar. An ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin da ya sasanta abubuwan da ake taƙaddama a kai cikin mako biyu sa’annan a kai masa rahoto. A ranar Talata Shugaba Buharin ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki waɗanda ke da alaƙa da ɓangaren ilimi a ƙasar…

Cigaba Da Karantawa

Korar Malaman Kaduna: Malamai Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman firamare sama 2000 a cikin makon jiya bisa dalilin basu zauna rubuta jarabawar kwarewa da gwamnatin ta shirya ba. Cikin waɗanda aka kora har da Shugaban kungiyar na kasa Mista Amba Audu wanda shima bai zauna rubuta jarabawar ba. Rahotanni sun bayyana Shugaban ƙungiyar ya umarci malamai da su kaurace wa jarabawar saboda babu dalilin sake rubuta irin wannan jarabawa bayan an taɓa rubuta irints a baya. Dalilin haka Shugaban Malaman ya ki rubuta jarabawar da wasu malamai sama…

Cigaba Da Karantawa

Jira Ya Kare: Daliban Jami’a Za Su Koma Darasi – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce nan bada jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a kasar. Ngige ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban kasa. Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da korafe-korafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabancin kungiyar. Ministan ya kara da cewa…

Cigaba Da Karantawa