Dakile CORONA: Ganduje Ya Tsawaita Hutu Ga Ma’aikata

Gwamnatin jihar Kano ta kara baiwa ma’aikatan ta hutun makonni biyu domin su ci gaba da zama a gida sakamakon dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar. A jiya ne dai Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da karin hutun. Sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar shine ya fitar da sanarwar mai kunshe da sa hannunsa. An dai kara kwanakin ne bayan cikar wa’adin hutun makwanni biyu wanda gwamnatin ta bayar a baya sakamakon dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a Kano.

Karanta...

Dakile CORONA: Ganduje Ya Tsawaita Hutu Ga Ma’aikata

Gwamnatin jihar Kano ta kara baiwa ma’aikatan ta hutun makonni biyu domin su ci gaba da zama a gida sakamakon dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar. A jiya ne dai Gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da karin hutun. Sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar shine ya fitar da sanarwar mai kunshe da sa hannunsa. An dai kara kwanakin ne bayan cikar wa’adin hutun makwanni biyu wanda gwamnatin ta bayar a baya sakamakon dakile yaduwar cutar ta Coronavirus a Kano.

Karanta...

Mutane 33 Sun Warke Daga Corona A Najeriya

Hukumomin Nijeriya sun bayyana cewar mutane 33 ne suka warke daga cutar COVID-19 wadda ta kama mutane 232 a kasar, ta kuma kashe 5 daga cikinsu. Wannan ya biyo bayan samun karin mutane 8 da suka kamu da cutar a ranar Lahadi. Hukumar Yaki da Cututtuka a Nijeriya ta ce, mutane takwas aka gano suna dauke da cutar a yammacin jiya Lahadi, wadanda suka fito daga Lagos da Abuja da kuma Kaduna, abin da ya kawo adadin mutanen da aka samu a yinin jiyan zuwa 18. Wannan na zuwa ne…

Karanta...

An Damke Mai Cutar CORONA Data Tsere A Ogun

Marar lafiyar dake dauke da cutar Corona Virus da ta gudu daga Cibiyar kula da lafiya dake Ejigbo a Jihar Osun an kamo ta an dawo da ita cibiyar kamar yadda PUNCH ta ruwaito. Marar lafiyar mace ce, an kama ta a garin Ejigbo yayin da ta koma wurin ‘yan sanda da tsakiyar ranar nan. Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Osun, Ismail Omipidan, ya tabbatar wa da Jaridar The PUNCH hakan. Ya ce an kama marar lafiyar kuma an dawo da ita asibitin.

Karanta...

Yakar Corona: Likitoci 18 Zasu Diro Najeriya Daga China

Likitoci 18 daga kasar China suna kan hanyar zuwa Nigeria domin shawo kan cutar Corona Virus da ta fara kyamari a kasar kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Ministan Lafiya Dr. Osage Ehanire shine ya bayyana haka a yayin tattauna da manema labarai a jiya a Abuja, yace likitoci da Nurse tare da mashawarta a harkar lafiya su 18 ne zasu zo Nigeria daga kasar China. Inda ake sa ran zasu taho da Ventilators tare da sauran kayayyakin kula da marasa lafiya, duk a kokarin kasar China na kawar da…

Karanta...

Tilas Ta Sa Muka Janye Dokar Ta Baci – Gwamnatin Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa saboda gudun shiga matsi da jama’ar Bauchi za su shiga ya sa ta janye dokar hana zirga-zirga. Mataimakin gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar a jihar, Sanata Baba Tela shine ya shaida haka a yayin taron manema labaru da suka yi jiya a gidan gwamnatin jihar. Yace yanzu haka jihar Bauchi nada masu dauke da cutar mutum uku, inda mutum biyu daga cikinsu ya shaida cewar an kusa sallamar su sakamakon saukin da suke samu daga cutar. Baba Tela ya kara…

Karanta...

CORONAVIRUS: Buhari Ya Ja Kunnen Dakarun Soji

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi jami’an hukumomin tsaro da aka jibge su domin tabbatar da dabbaka dokar hana shige da fice a jahohin Najeriya da su daina cin zarafin jama’a tare da kuntata musu. An ruwaito sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na ko-ta-kwana a kan Coronavirus ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabin ayyukansu a ranar Juma’a, a Abuja. Boss ya yi kira ga ‘yan Najeriya su kasance masu bin doka da oda, tare da kasancewa masu hakuri da kuma kiyayewa.…

Karanta...

CORONA: Za A Tilasta Amfani Da Takunkumi

Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar tilasta wa dukkanin ‘yan Najeriya amfani da takunkumin rufe fuska domin hana yaduwar cutar COVID-19, wanda ke ci gaba da hauhawa a fadin kasar. Har ila yau gwamnatin na sake duba yarjejeniyar rufe jihohin Lagas da Ogun da kuma babban birnin tarayya na kwanaki 14, jaridar Thisday ta ruwaito. Domin kara kaimi wajen warkar da wadanda suka harbu da cutar, gwamnati ta dawo da ma’aikatan lafiya da suka yi ritaya inda a yanzu ake horar dasu domin su taimaka wajen kula da warkar da wadanda…

Karanta...

Kaduna: Adadin Masu Corona Ya Kai Mutum Hudu

Hukumomi a jihar Kaduna sun tabbatar da kamuwar mutum na 4 da cutar coronavirus a jihar. Kamishinar Lafiyar Jihar Kaduna, Hadiza Mohammed Baloni ta sanar da hakan a cikin wani sako da ta fitar. Samun karin wanda cutar coronavirus ta kama a jihar na zuwa ne washegarin ranar da gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita da ta sanya, domin dakile yaduwar cutar a jihar. Ma’aikatar Lafiyar jihar ta ce tana kokarin gano mutanen da masu cutar suka yi hulda da su domin a killace, a kuma lura da su.…

Karanta...

Yakar Annoba: Doka Bata Amince Ayi Amfani Da Karfin Soji Ba – Falana

Femi Falana, babban lauya mai rajin kare hakkin bil Adam, ya ce babu dokar da ta amince a yi amfani da sojoji don hana jama’a walwala a kan annoba. A jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ga ‘yan Najeriya a ranar Lahadi, ya bada umarnin rufe jihohin Ogun, Abuja da Legas daga karfe 11 na daren Litinin har zuwa yadda hali yayi. Amma kuma Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, ya ce yayi nasarar shawo kan shugaba Buhari a kan kara kwanakin zuwa ranar Juma’a ta yadda za a samu…

Karanta...

Filato: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Sake Gayyatar Jingir

Rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ta sake kiran shugaban majalisar koli ta malaman Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, tare da yi masa tambayoyi an kan rashin biyayya ga umarnin jiha na hana dukkan wani taro har na addini a jihar saboda gujewa kamuwa da kwayar coronavirus. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya shaidawa manema labarai, da yammacin ranar Talata, cewa sun gayyaci Sheikh Jingir zuwa hedikwatar saboda ya jagoranci magoya bayansa sallar Juma’a duk da an saka dokar hana taron jama’a. A…

Karanta...

CORONA: El Rufa’i Na Killace

Hankalin gwamnatin jihar Kaduna ya zo kan wani Bidiyo da ake yaɗawa wadda ke nuna Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i ke zirga zirga a kan wasu titunan cikin garin Kaduna domin tabbatar da al’umma sun bi dokar da aka saka. Da haka ne gwamnatin ke sanar da al’umma cewa wannan Bidiyon an dauka ne a ranar Juma’a 27 ga watan Maris kwana daya kafin ya ke6e kansa. A ranar Asabar 28 ga watan Maris, Malam Nasir ya fito ya yi wa duniya jawabin sakamakon gwajin da aka yi masa na cutar…

Karanta...

Kaduna: El Rufa’i Ya Harbi Mutum Biyu Da CORONA

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar Kaduna, Dakta Amina Baloni, ta tabbatar da cewa lallai mutane biyun da suka kamu da cutar Coronavirus a Kaduna wadanda suka hadu da El-Rufa’i ne. Mun kawo muku rahoton cewa cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC a ranar Litinin ta alanta cewa an samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kaduna. Hakazalika a ranar 28 ga Maris, gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar. A jawabin da Balori ta saki ranar…

Karanta...

Yakar CORONA: China Ta Bada Magunguna Ga Gwamnatin Bauchi

Gidauniyar Mutual Commitment Group (MCG) daga Kasar Sin ta bada tallafin magunguna na yaki da cutar corona virus ga gwamnatin jihar Bauchi don magance yaduwar cutar. Manajin daraktan gidauniyar Mr. Lui Zhaolong yace, sun samar da kayan yaKi da cutar guda dubu dari da hamsin, wadanda za’a yi amfani da su wajen dalike yaduwar cutar. Mr Zhaolong ya kara da cewa, gidauniyar za ta cigaba da tallafawa yaKi da cutar a fadin Najeriya, tare da koyar da sabbin dabarun yaKi da cutar kamar yadda Kasar Sin din ta gabatar a…

Karanta...

CORONA: Gwamnan Kwara Ya Sadaukar Da Albashin Shi Na Shekara

Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya. An ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi, 29 ga watan Maris, a daidai lokacin da attajiran Najeriya suke bayar da nasu gudunmuwar domin taimaka ma gwamnati wajen yaki da cutar. A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi…

Karanta...