Bauchi: Jami’ar Tafawa Balewa Ta Kirkiri Na’urar Kashe CORONA

Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta kirkiri wata na’ura da za ta taimaka wajen dakile yaduwar kwayar cutar covid-19 a Najeriya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Abdulazeez, ne ya sanar da hakan yayin da ya ke magana a wurin kaddamar da na’urar wanda aka yi ranar Talata a Bauchi. Ya bayyana cewa kirkirar na’aurar tamkar sauke nauyin da ke kan jami’ar ne a matsayinta na cibiyar bincike da kirkiro sabbin abubuwa. Farfesa Abdulazeez ya ce yanzu haka jami’ar tana kokarin kirkirar na’urar…

Karanta...

Za A Yi Amfani Da Fasahar Zamani Ta ICT Domin Samar Da Ayyuka Ga Matasa – Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital sheikh Isa Pantami ya ce gwamnati za ta bayar da himma ga Fasahar Sadarwar zamani da Harkokin Kasuwanci don kara samar da ayyukan yi ga matasa. Ministan ya yi wannan alƙawarin ne yayin ƙaddamar da membobi a kwamitin masu bada shawara na kungiyar, Regional Entrepreneurship Acceleration Programme Supported dake makarantar fasaha ta Massachusetts dake Abuja. “Kamar yawan al’ummomin Afirka, kashi 60 na matasa ne; amma babu wadatattun ayyuka na yau da kullun (a cikin gwamnati ko kamfanoni) don yawan jama’a. “Duk da cewa…

Karanta...

Buhari Ya Soke Dakatarwa Da Aka Yi Wa Shugaban Lantarki

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke dakatarwar da aka yi wa Damilola Ogunbiyi a matsayin babban manajan Hukumar samar da lantarki na karkara (REA). Idan ba a manta ba dai ministan makamashi, Sale Mamman ne ya dakatar da Ogunbiyi. Ya kuma bayar da umurnin gudanar da bincike a kan zargin aikata ba dai-dai ba a lokacin da ta ke shugabancin hukumar. Kafin dakatar da ita, Ogunbiyi wacce ita ce shugaba mace na farko a hukumar ta REA, ta mika takardan yin murabus dinta domin ta samu sabon aiki a Majalisar Dinkin…

Karanta...

Buhari Ya Naɗa Sabon Shugaban Hukumar DPR

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sarki Auwalu a matsayin sabon shugaban hukumar da ke kula da man fetur ta kasa (DPR). Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya fitar da sanarwar nadin ta Mista Auwalu. Mista Adesina ya ce sabon shugaban da aka nada zai rike mukamin ne na tsawo shekaru hudu. “Mista Auwalu wanda injiniya ne na sinadaren chemical ya kasance daya daga cikin jigo a hukumar ta DPR tun da ya fara aiki a hukumar a matsayin babban injiniya a 1998. “Sabon…

Karanta...

Ana Yi Mini Zagon Ƙasa – Pantami

Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya yi gargadi ga wasu marasa kishin kasa dake kokarin yiwa ma’aikatarsa zagon kasa kan ayyukan walwalan jama’an da suke yiwa yan Najeriya. Malam Pantami, ya yi wannan gargadi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman, a jawabin da ta saki ranar Litinin a Abuja. A jawabin yace binciken da aka kaddamar kan wasu masu almundahana ya sa suna kokarin yada labaran karya kan ma’aikatar. Ministan ya ce wadannan mutane sun fara kokarin bata masa suna saboda basu jin dadin irin…

Karanta...

Gudanar Da Mulki: Gwamnatin Tarayya Ta Hada Hannu Da Wani Kamfani

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki da kamfanin Galazxy Backbone a tsarin zamanantar da aikin gwamnati ta hanyar yanar gizo. Mustapha ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce a shirye gwamnati take ta yi maraba da zuba jari akan abubuwan da suka shafi fasahar zamani. Ya ce jajircewa da kuma yin abubuwan da suka kamata zai taimaka wajen cika burin gwamnati na zamanantar da aikace-aikacen ta. Mustapha ya kara da cewa horas da ma’aikatan…

Karanta...

Wani Malamin Makaranta Ya Samu Kyautar Naira Miliyan 360

Wani malamin makaranta a kauyen Kenya da ya saba bayar da akasarin albashinsa domin taimaka wa dalibai marasa galiho ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon malami na duniya. Peter Tabichi ya samu dala miliyan 1, wato kimanin kudin Najeriya naira miliyan 360 ke nan. Malamin ya samu yabo wajen taimaka wa wata makaranta mai karancin azuzuwa da yawan dalibai. Mista Peter wanda yake koyar da darasin kimiyya ya ce yana so dalibai su nakalci kimiyya domin kawo ci gaba a rayuwar gobe. An bayyana malamin wanda aka bashi kyautar a…

Karanta...

Na Cire Tsammanin Fitowa a Raye >>> Inji ‘Dan Jaridar Da Akayi Garkuwa Dashi

Anyi garkuwa da Ahmed Garba ma’aikacin jaridar daily trust a yammacin ranar da akayi zaben gwamnoni a hanyar sa ta dawo wa Kaduna daga babban birnin tarayya abuja. Ahmed yace “,na cire rai zanfito a raye daga dajin da aka ijeye mu bayan anyi garkuwa da mu . Masu garkuwan suna ta yimin barazanar kisa a kullum a kwanaki takwas da na shafe a wurin su. Ahmad ya bayyana hakan ne a lokacin da abokan aikin sa suka kai masa ziyarar jaje awanni kadan bayan ya samu ‘yancin kansa ranar…

Karanta...

Kamfanin NNPC: An Samu Dala Biliyan 5 Daga Man Fetur Da Gas- NDU

Kamfanin matatar mai na Najeriya NNPC ya ce kudin da aka samu wajen sayar  danyen man fetur da kuma Gas a watan Agusta ya kai Dala Miliyan 470. Kamfanin ya ce kudin da Najeriya ta samu a watan Agusta ya zarce abinda aka samu a watan Yuli da kusan Dala Miliyan 80. Mai magana da yawun kamfanin Ndu Ughamdu ya ce an sami kudi sosai a cikin watan Agustan shekara ta 2018, inda  Najeriya ke  samun fiye da kashi 70 na kudin shigan ta ne daga mai. Ya tabbatar da…

Karanta...