Shuka Alheri: Ɗalibin Da Kwankwaso Ya Gina, Ya Gina Ɗalibai

Wani dalibi da ya ci gajiyar tsarin tallafin karatu kyauta na tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Garba ya dauki nauyin karatun dalibai fiye da 150 a makarantun gaba da sakandari da dama a ciki da wajen Kano. Garba ya shiga cikin dalibai 501 da Kwankwaso ya turasu kasar Malaysia domin su yi karatun digiri na uku a bangaren dabarun tafiyar da kasuwanci, inda a yanzu haka yake koyarwa a sashin gudanar da kasuwanci na jami’ar Bayero. Garba yace ya dauki gabaran daukan tallafin daliban ne domin…

Karanta...

Gombe: An Kaddamar Da Cibiyoyin Ilimantar Da ‘Ya’ya Mata

A Ƙoƙarin da gwamnatin jihar Gombe ta ke yi na ciyar da ilimi musamman na yara mata gaba, gwamnatin jihar a karkashin shirin ta na bunƙasa harkar ilmi ta samar da cibiyoyin harkar ilimi a yankin Kuri da ke ƙaramar hukumar Yemeltu Deba da ke jihar. A yayin bikin kaddamar da cibiyoyin, Uwargidan Gwamnan jihar Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa, ta bayyana muhimmanci da tasirin ilimi a tsakanin ‘ya’ya Mata. Ta kalubalanci iyaye da su dage wajen sanya ‘ya’yan su makaranta domin rage yawaitar yara da basu zuwa makarantu a faɗin…

Karanta...

‘Yan Najeriya Zasu Zama Masu Fasahar Zamani Kafin 2030 – Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Isa Ali Pantami ya ba da sanarwar cewa a cikin shekaru 10 masu zuwa na kashi 95 cikin 100 na ‘yan Najeriya za su iya samun ilimin rubutu da Karatu na dijital, sakamakon haka ne za a watsar da duk wasu ayyukanyi na kasar. Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai na ICT a Abuja. A cewarsa, ma’aikatar sadarwa tana shirin fara horar da ‘yan Najeriya game da iya karatu da rubutu da fasahar zamani,…

Karanta...

Ɗiyar Buhari Ta Kammala Jami’ar Landan Da Sakamako Mafi Daraja

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi bikin murnar kammala digirin ‘yarta, Hanan, daga jami’a. A wata sanarwar da Aisha Buhari ta yi a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa Hanan ta kammala ne da digiri mai darajar farko. Uwargidan shugaban kasar ta mika godiyarta ga wadanda suka tallafawa ‘yarta wajen kammala aikinta na shekarar karshe. Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta wallafa hotunanta tare da Hanan Buhari a yayin murnar kammala digirinta na farko daga wata jami’a a Kasar Ingila. Bayanai sun nuna cewa, Hanan ta kammala…

Karanta...

Ilimi: Uwargidan Shugaban Kasa Ta Ɗauki Nauyin Biyan Jarrabawar Ɗalibai

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta dauki biya ma dalibai 5000 yan asalin jahar Adamawa kudin zana jarabawar kammala Sakandare ta WAEC da NECO, tare da daukan nauyin basu horo a kan yadda zasu fuskanci jarabawar. Aisha ta dauki nauyin wannan hidima ne a karkashin gidauniyarta ta Future Assured, inda kamar yadda jami’i mai kula da gidauniyar a jahar Adamawa, Ya’u Babayi ya bayyana a yayin taron yaye mata da matasa 600 da suka samu horo a sana’o’i daban daban. Babayi yace manufar gidauniyar shi ne tallafa ma mata da…

Karanta...

Ilimi Shine Babbar Hanyar Kawar Da Talauci A Najeriya – Atiku Abubakar

Dan takarar shugabancin Najeriya, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace: samarwa ‘yan Najeriya ilimi shine kadai zai sanya kasar zata fitadaga matsayin ta na Helkwatar talauci ta duniya. Atiku Abubakar, yayi wannan magana ne jiya, yayin da yake gabatar da jawabin sa a wajen taron mahukunta na jami’ar Amurika (AUN) ta kasa Najeriya dake jihar Adamawa karo na 14, wanda ya gudana a dakin taro na Lamido Aliyu Mustapha dake babban matsugunin jami’ar ta Amurika dake Yolan jihar Adamawa. Kafin fara gabatar da jawabin sa a wannan waje,…

Karanta...

Babbar Gata Da Zaka Yi Wa Matashi Ita Ce Tallafawa Ilimin Shi – Uba Sani

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Uba Sani, yace a wani bangare na bunkasa harkar ilimi a mazabar Kaduna ta tsakiya, ya ɗauki nauyin ɗalibai 100 a Kwalejin koyar da dabarun ayyukan noma da kiwo ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Kaduna. Sanatan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a yayin taron kungiyar tsofaffin dalibai na Kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna a Asabar ɗin nan. Dan Majalisar ya kara da cewar babu wani tagomashi da za ka yi…

Karanta...

Borno: Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Makarantar Marayu

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da makarantar da aka ginawa yara marayu akalla guda 540 a jihar. Wani attajiri mazaunin Maiduguri ne ya daukin nauyin wannan gini gaba dayansa. A bangarensa, gwamnan ya bada kyautan motocin da za’a rika amfani da su wajen kai yaran makaranta. Wakilinmu ya samu labarin ne a jawabin da hadimin gwamnan ya saki a shafinsa na Facebook inda yace: “Gwamna Babagana Umara Zulum ya kaddamar da makaranta mai iya daukan marayu 540 da wani mutumin kirki ya gina. ” Wani attajirin Maiduguri,…

Karanta...

Yadda Na Zama Farfesa Daga Sana’ar Dukanci – Shugaban Jami’ar Yobe

Labarin Farfesa Andrew Haruna na daya daga cikin labaran mutanen da suka yi nasara ta hanyar jajircewa, aiki tukuru da kuma rashin yanke tsammani. Wadannan abubuwan kuwa na iya sa mutum ya kai kololuwar daukaka. Farfesa Haruna shine shugaban jami’ar tarayya da ke Gashua, jihar Yobe. A farkon rayuwarsa, ya dukufa ne yin kananan aiyuka don samun mafita. Tun kuwa yana karami yake son karatu tare da burin zama mai ilimi. Hakan kuwa ne yasa ya fara zuwa makaranta duk da iyayenshi basu da kudin kaishi. An haifeshi a 1957…

Karanta...

Duniyar Fasaha: Pantami Zai Jagoranci Bada Ilimin Kwamfuta Ga Ma’aikata

Ministan sadarwa da tattalin arziki na dijital, Sheik Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa ma’aikatar karkashin kulawarsa za ta ba da fifikon ilimin zamani na Digital tare da tabbatar da cewa nan da shekarar 2022 zuwa 2023 dukkan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya suna masu ilimin kwamfuta. Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da jawabi a yayin taron rufe makaratar ci gaban ci gaban gwamnatoci a Najeriya da kuma Babban Cibiyar horar da gwamnatoci a Najeriya. Gwamnatin Koriya ta kudu ta aiwatar da…

Karanta...

Neja: Hatsarin Mota Ya Lakume Ran Hafizin Kur’ani A Hanyar Zuwa Musabaƙa

Mun samu labarin wani mummunar hadarin mota da ya rutsa da Hafizan alkur’ani maigirma wadanda suka taso daga Kontagora zuwa Minna domin halartar musabukan alkur’ani maigirma da za’a gudanar. Rahoton da muka samu ya tabbatar da cewar har daya daga cikin hafizan ya rasa ransa, yayin da wasu suka jikkata. Muna rokon Allah ya jikan mamacin, wadanda sukayi rauni Allah ya basu lafiya. Daga Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora

Karanta...

Yobe: Gwamna Mai Mala Ya Raba Kujerun Makka Da Motoci Ga Mahaddatan Al-Kur’ani

Gwamnan jahar Yobe, Mai Mala Buni ya bada kyautukan motocin alfarma da guraben aikin Hajji ga mahaddatan da suka yi zarra a gasar haddar Al-Qur’ani na jahar da hukumar ilimin larabci da ilimin addinin Musulunci ta jahar ta shirya. Wakilinmu ya ruwaito mahaddata daga kananan hukumomin jahar 17 ne suka fafata a gasar, yayin da zakaran gasar zai wakilci jahar a babban gasar haddar Al-Qur’ani ta kasa da kasa da za’a yi a jahar Legas. Alaramma Maina Muhammad daga karamar hukumar Machina ne ya lashe gasar a fannin haddar izu…

Karanta...

Na Auri Mijina Tun Ban Girma Ba – Uwargidan Gwamnan Bauchi

Aishatu Mohammed, Uwargidar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta bayyana a ranar Asabar cewa bata yi karatu ba lokacin da ta auri mijinta. Hajiya Aishatu ta bayyana hakan ne a jihar Bauchi a taron da kwamitin tallafin kananan yaran ta majalisar dinkin dunya UNICEF. Tace: “Ina yar shekara 16 kuma a jahilce lokacin da na auri mijina.” “Mu yara mata 100 ne a danginmu; babu wacce tayi karatun Boko cikinmu; sai da na haifi yara uku na fara karatu.” “Dalilin haka shine iyayenmu basu yarda da ilmantar da diya mace…

Karanta...

Ilimi: Baturiya Halima ‘Yar Fulani Ta Ƙirƙiri Littafin Kurame Na Hausa

Wata baturiya mai suna Dakta Constanza wadda mutane ke kiranta da Halima ‘yar Fulani ta kirkiri wani littafin bebaye na Hausa domin tallafa wa bebayen su yi karatu da harshensu. Halima ta byyana cewa ta rubuta littafin daga na daya har zuwa na takwas a halin yanzu. Ta ce suna yin amfani da litattafan a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a Kano. Ta nemi masu hannu da shuni su taimaka da kudaden da za a ci gaba da buga littafan na bebaye domin inganta rayuwarsu.

Karanta...

Borno: Gwamna Zulum Ya Sha Alwashin Biyan Makudan Kudade Ga ‘Yan Bautar Kasa

Gwamnatin jihar Barno a ranar Alhamis tayi kira ga masu hidimar kasa da su garzayo jihar don kwasar sha tara ta arziki da gwamnatin jihar ta tanadar. Gwamnatin jihar tayi alkawarin biyan duk mai bautar kasa N10,000 a duk wata ta kara da cewa, akwai tabbacin tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu da gwamnatin jihar ke da shi. Gwamnatin jihar Barno a ranar Alhamis ta sanar da cewa zata dinga ba wa duk dan hidimar kasa N10,000 a duk wata. Shugaban hukumar NYSC na jihar, Dr Sambo Barka Amaza, yace ,…

Karanta...