Tirkashi: Faisal Maina Ya Cire Milyan 58 Cikin Sa’a Guda

A ranar Litinin, Wani jami’in hukumar hana almundhana da yiwa tattalin arzikin zagon kasa EFCC, Mohammed Goji, ya bayyanawa kotu cewa Faisal Maina, yaron tsohon shugaban kwamitin gyara harkar fansho, Abdulrashid Maina, ya cire N58m daga cikin asusun kudi a bankin UBA. Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Goji, wanda babban jami’in bincike ne a hukumar EFCC ya yi shaida a kotu inda aka gurfanar da Faisal Maina. Goji ya bayyana hakan ne gaban Alkali Okon Abang, na babbar kotun tarayya Abuja. Ya laburtawa kotu cewa Faisal ya…

Karanta...

Zama Gidan Yari: Maina Ya Kamu Da Rashin Lafiya

An samu cikas wajen gurfanar tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, AbdulRashid Maina, gaban alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Alkali Okon Abang, a ranar Talata sakamakon rashin lafiya. Hukumar EFCC ta kai karar Maina kotun ne kan zargin almundahana, babakere da yaudara na kudin fanshon jama’a kimanin Bilyan dari. Yayin da kotu ta dawo zama yau Talata, jami’an hukumar gidajen yarin da sauya hali sun gabatarwa Alkalin kotun da wata takardar likitan gidan yarin mai suna, Idowu Ajayi, cewa Maina ya kamu da rashin lafiya. Bayan karanta wasikar, Alkali Okon…

Karanta...

Ban Karbi Sarautar Bichi Don Tozarta Sunusi Ba – Aminu Ado

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero yace bai karbi sarautar Bichi da zummar cin mutunci ko ragewar sarautar Sarki Sunusi daraja ba. Sarkin ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai inda bayyana karbar sarautar ba a matsayin mataki na cin mutunci Muhammadu Sunusi II ba. Yace yakamata mutane su gane cewa komai yana iya chanzawa a kowana irin lokaci. “Tun cikin shekarar 1963 da mahaifina ya zama Sarkin Kano, abubuwa sukayi ta chanzawa, kuma zasu cigaba da chanzawa.” “Bari na baku wani misali; mahaifina ya nada…

Karanta...

Babu Wanda Ya Kamani, Kanzon Kurege Ne Kawai – Zazzabi

Sanannen mawakin finafinan Hausa Sadik Zazzabi ya karyata labarin da ke yawo a wasu kafafen yada labarai na cewar wai wata kotu a Kano ta garkame shi saboda fitar da wata waka da yayi ba bisa ka’ida ba. Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, Sadik Zazzabi ya ce bai san daga inda wannan labarin ya fito ba, ya wayi gari ne ya ga labarin na yawo ta kafafen sadarwa na zamani. Shahararren mawakin ya kara da cewar, yana kira ga kafafen yada labarai da su rinka tantace labarai…

Karanta...

Damfara: An Kama Wani Mai Amfani Da Sunan El-Rufa’i Ya Na Cutar Mutane

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta kama wani mai suna Mohammed Jamilu da ya kware wajen amfani da sunan mutane domin bata masu suna. Wanda ake tuhumar dai ya kware wajen amfani da sunan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya na aikata laifuka, inda ya ke tsoratar da wadanda ya ke cutar ta hanyoyi da dama. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Ahmad Abdulrahman da ya gabatar da wanda ake zargin a helkwatar ‘yan sanda ta Kaduna, ya ce wanda ake tuhumar ya na zuwa wajen malamai…

Karanta...

Badakalar NBC: Lai Mohammed Ya Amince Da Kuskuren Da Ya Tafka Na Sa Kwangila Hannu

Ministan Yada Labarai da al’adu Lai Mohammed, ya amince cewa bai yi kwakkwaran bincike kafin ya yi gaugawar sa hannu a biyan harkallar kudaden kwangilar naira biliyan 2 da rabi da ta dabaibaye Hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ba. An dai sa hannu a kwangilar ne, inda aka amince a ba kamfanin Pinnacle Communications tsabar kudi har naira bilyan 2 da rabi  domin aikin inganta tashar talbijin daga tsohon ya yi zuwa na zamani. Lai Mohammed ya shaida wa hukumar ICPC cewa, ya sa hannun biyan kudin ne…

Karanta...

Matsalar Albashi: Likitoci Sun Shiga Yajin Aiki Saboda Rashin Sahihin Albashi

Kungiyar likitoci ta Nijeriya reshen jihar Imo, ta sanar da shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani a ranar Larabar da ta gabata, bisa matsalar albashi da ke tsakanin ta da gwamnatin jihar da ta ki ci ta ki cinyewa. Shugaban kungiyar Dakta Kyrian Duruewure ya tabbatar da haka, yayin da ya ke ganawa da manema labarai a birnin Owerri na jihar Imo. Dakta Kyrian, ya ce yayin da takwarorin su na sauran jahohi su ka fara cin gajiyar sabon tsarin albashin ma’aikatan likitoci, su kuma gwamnatin jihar Imo ta yi biris…

Karanta...

Zargin Cin Zarafi: Jam’iyyar PDP Ta Janye Kudirin Gudanar Da Zanga-Zanga A Kano

Jam’iyyar PDP ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa sakamakon cin zarafi da muzgunawa da keta haddi da kuma barazanar mutuwa da wasu hukumomin tsaro ke yi wa ‘ya’yan ta a jihar Kano. Sakataren kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na jihar Kano Shehu Wada Sagagi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya fayyace dalilin janye zanga-zangar da jam’iyyar ta yi. Sagagi ya kara da cewa, duba da yadda aka samu rangwamen cin kashin da ake yi wa ‘ya’yan ta, ya sa uwar jam’iyyar ta yanke…

Karanta...

Wa’adin Mulki: Buhari Ya Umarci Ministoci Su Mika Rahoton Ayyukan Su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bada umarnin cewa kowane minista ya gaggauta mika cikakken bayanin ayyuka da tsare-tsaren da ya gunanar tsawon shekaru hudu da ya yi a kan mukamin sa. Umurnin dai ya shafi ministoci da shugabannin hukumomi da sauran bangarorin gwamnatin tarayya, inda aka ba su wa’adin nan da zuwa ranar 24 ga Afrilu kowa ya mika rahoton shi ga Kwamitin Shugaban Kasa Mai Bin Diddigin Ayyuka da ke ofishin Mataimakin Shugaban Kasa. Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu…

Karanta...

Bayyana Kadarori: Kotu Ta Yanke Wa Onnoghen Hukunce-Hukunce Uku

Kotun ladaftar da ma’aikatan gwamnati, ta yanke wa tsohon shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen hukunci, bisa zargin rashin bayyana dukkan dukiyoyin sa kamar yadda dokar hukumar kula da da’ar ma’aikata ta tanada. Alkalin kotun Danladi Umar ya tabbatar da zargin da ake yi wa Onnoghen, tare da yanke ma shu hukunce-hukunce uku. Hukunce-hukuncen kuwa sun hada da umurnin a sauke Onnoghen daga kujerar shugaban Alkalai, sannan an haramta ma shi rike wani mukamin gwamnati na tsawon shekaru goma, sannan an kwace duk kudaden da aka samu a cikin asusun ajiya…

Karanta...

Guraben Aiki: Hukumar Kwastan Za Ta Dauki Sabbin Ma’aikata 3,200

Rahotanni na cewa, Hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya, ta sanar da daukar sabbin ma’aikata 3,200 a fadin Nijeriya. Hukumar dai ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana shafin da za a iya neman aikin ta yanar gizo. A cikin sanarwar, hukumar ta ce za a rufe amsar bayanan masu neman aikin a ranar 7 ga watan Mayu, kuma ba za a karbi takardun duk wanda ya mika takardun sa a ofisoshin hukuma ko hedikwatar ta da ke Abuja ba. Sanarwar ta…

Karanta...

Shan-Inna: Rotary International Ta Ba Nijeriya Gudunmawar Dala Miliyan 5.7

Kungiyar ‘Rotary International’, ta tallafa wa gwamnatin Nijeriya da dala miliyan 5 da dubu 700 domin kawar da cutar shan’inna. ‘Rotary International’, ta damka kudaden ne ga wakiliyar hukumar tallafa wa kananman yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF a makon da ta gabata a Abuja. Ministan lafiya Isaac Adewole, ya jinjina wa kungiyar bisa wannan tallafi, sannan ya ce Nijeriya za ta maida hankali wajen ganin ta kawar da cutar kwata-kwata. Adewole ya kuma yaba da kokarin da hukumar cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko ta kasa game da ayyukan kawar…

Karanta...

Yaki Da Ta’addanci: Sojoji Na Ci-Gaba Da Amon Wuta Akan ‘Yan Bindigar Zamfara

Dakarun Sojin Nijeriya na musamman, sun tarwatsa wani gungun ‘yan bindiga da su ka kaddamar da hare hare a kauyukan Rafi da Dola da ke cikin lardin Mada na karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara. Kakakin rundunar Ibikunle Daramola ya bayyana haka, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce sun samu bayanan da ke nuna ‘yan bindigar sun fara taruwa a kauyukan Rafi da Dola da nufin kai hari, lamarin da ya sa su ka garzaya domin fatattakar su. Daramola yana cigaba da cewa, ba…

Karanta...

Bakin Kishi: Amarya Yar Shekaru 15 Ta Zuba Wa Mijin Ta Gubar Bera A Abinci

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta kama wata amarya ‘yar shekaru 15 mai suna Hassana Lawan, bisa laifin zuba wa mijin ta mai suna Sale Abubakar a cikin abincin sa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin ne a cikin wata sanarwa da ya bayyana wa manema labarai a Kano. DSP Haruna, ya ce ranar Talatar da ta da misalin karfe 2 na rana, ‘yan sanda sun samu labarin cewa wadda ake zargin ta zuba wa mijinta gubar bera a…

Karanta...

Zaben 2019: Zan Gayyato Kwararru Daga Amurka Domin Tabbatar Da Nasara Ta – Atiku

Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar PDP

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya ce ya na gab da gayyato kwararru daga Kamfanonin fasaha na Microsoft da IBM da kuma Oracle, domin tabbatar da zargin sa na cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a watan Maris. Atiku Abubakar dai ya yi ikirarin cewa, hatta shafin hukumar zaben Nijeriya ya tabbatar da cewa, ya doke shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da kuri’un da yawan su ya kai miliyan 1 da dubu dari 6. Kalaman na Atiku dais u na…

Karanta...