Jagorantar Idi: ‘Yan Sanda Sun Gayyaci Sheikh Khalifa Zariya

Duk da cewa Malamin ya bi umarnin da gwamnati ta bayar na cewa kowa ya yi sallah a gida, amma kasancewar Malamin yana da almajirai da iyalai da dama hakan ya sa jama’a sun samu halartar sallar duk da cewa a gidansa dake Zaria aka gudanar da sallar. Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan idar da sallar ne sai ga jami’an ‘yan sanda sun dira gidan malamin, inda suka ce masa ana gayyatarsa zuwa ofishinsu. Saidai wasu daga cikin wadanda suka halarci sallan sun fusata, inda suka ki yarda a…

Karanta...

Jagorantar Sallar Idi: ‘Yan Sun Gayyaci Sheikh Khalifa Zariya

Duk da cewa Malamin ya bi umarnin da gwamnati ta bayar na cewa kowa ya yi sallah a gida, amma kasancewar Malamin yana da almajirai da iyalai da dama hakan ya sa jama’a sun samu halartar sallar duk da cewa a gidansa dake Zaria aka gudanar da sallar. Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan idar da sallar ne sai ga jami’an ‘yan sanda sun dira gidan malamin, inda suka ce masa ana gayyatarsa zuwa ofishinsu. Saidai wasu daga cikin wadanda suka halarci sallan sun fusata, inda suka ki yarda a…

Karanta...

Da Dumi-Dumi: Kyari Ya Warke Daga CORONA

Abba Kyari Ya Warke Daga Cutar Corona Virus, Bayan Ya Shafe Kusan Makonni Biyu Yana Killace Abba Kyari, ya warke daga cutar Corona Virus bayan ya shafe kusan makonni biyu a killace na kamuwa da cutar da yayi kamar yadda Daily Correspondents ta ruwaito.

Karanta...

Yakar CORONA: Sanatoci Sun Bada Rabin Albashin Su

‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya sun sadaukar da rabin albashinsu domin tallafa wa yaki da cutar coronavirus. Kakakin Majalisar, Sanata Godiya Akwashiki ya sanar da cewa daga watan Maris da muke ciki ‘yan Majalisar za su ci gaba da bayar da bayar da rabin albashinsu har sai an magance cutar a Najeriya. Sanarwar gudunmuwar sanatocin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ministocin kasar sun sanar da mika da rabin albashinsu na watan Maris a matsayin tallafi ga kokarin kasar na yaki da annobar. Tallafin nasu kadan ne daga irin taimakon da…

Karanta...

CORONA: An Kafa Dokar Hana Fita A Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a fadin jihar da niyyar dakile yaduwar cutar coronavirus. Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta sanar da cewa dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren yau Alhamis, har sai abin da hali ya yi. Hadiza Balarabe ta ce dokar ta tilasta wa jama’a zama a gida, tare da haramta zuwa cibiyoyin kasuwanci da halartar wuraren ibada. Dokar ta kuma haramta dukkan tarukan jama’a da bukukuwa. Sai dai dokar ba ta shafi masu ayyuka na musamman da suka…

Karanta...

Da Dumi-Dumi!!! Abba Kyari Ya Harbu Da CORONA

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin. Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami’an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya. Ya dawo gida Najeriya bayan sati daya a ranar Asabar 14 ga watan Maris amma babu alamun ya kamu da cutar. Rahotanni sun bayyana cewa…

Karanta...

Da Dumi-Dumi!!! Abba Kyari Ya Harbu Da CORONA

A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin. Kyari ya tafi Jamus a ranar Asabar 7 ga watan Maris inda ya gana da wasu jami’an kamfanin Siemens a binrin Munich a kan shirin fadada aikin wutan lantarki a Najeriya. Ya dawo gida Najeriya bayan sati daya a ranar Asabar 14 ga watan Maris amma babu alamun ya kamu da cutar. Rahotanni sun bayyana cewa…

Karanta...

Coronavirus Ta Hana Taron Maulidin Sokoto

Khalifa Shehu Ahmad Tijjani Inyass ya bayar da sanarwar dage taron maulidin Shehu Ibrahim Inyass wanda Kungiyar majma’u Ahbabu Shehu Ibrahim zata shirya a garin Sokoto, sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun Faila maulana Sheikh Mahi Cisse a cikin wani dan gajeren muryar audio. A cikin jawaban nasa Sheikh Mahi Cisse ya bayyana cewa Khalifa ShehunTijjani Inyass ya bada izinin dage taron ne saboda kaucewa annobar cutar CoronaVirus wanda ta addabi al’ummar duniya, yayi kira ga “Kungiyar Majma’u Ahbabul Sheikh” da ta gaggauta dakatar da dukkan shirye…

Karanta...

Kotu Ta Dakatar Da Oshiomole Daga Shugabancin APC

Wata babbar kotun Abuja da ke Jabi, ta dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Mai shari’a Danlami Senchi, a yau Laraba, ya umarci Oshiomhole da ya sauka daga mukamin sa, yayin da kotun ta yanke hukunci kan batun ficewar sa na neman shugabancin jam’iyyar APC na dindindin. An yi kira daga sassan jam’iyyar APC akan Oshiomhole ya yi murabus kuma shugaban jam’iyyar Edo ya dakatar da shi a watan Nuwamban da ya gabata. Jam’iyyar ta dakatar da…

Karanta...

Cutar Coronavirus: Saudiyya Ta Haramta Umrah

Gwamnatin Saudiya ta bayyana dakatar da zuwa Umrah da al’ummar Musulmin duniya ke yi, domin kaucewa yada cutar coronavirus wadda ke cigaba da yaduwa kamar wutar daji zuwa kasashen duniya yanzu haka. Saudiyar ta bayyana kaduwa da yadda cutar ta shiga cikin wasu kasashe dake makotaka da ita. Majiyarmu ta ruwaito cewar babu dadi kan yanke hukuncin amma wannan hanyar ita ce hanya mafi da cewa daya kamata kasar ta dauka don kaucewa ci gaba da yaduwar cutar. Musulman duniya sun nuna rashin jin dadin su matuka sai dai bamu…

Karanta...

Kotu Ta Yankewa Maryam Sanda Hukuncin Kisa

Wata kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta. An yanke hukuncin ne bayan gurfanar da matar bisa laifin daba wa mijinta mai suna Bilyaminu Bello wuka a shekarar 2017, sakamakon rikici a tsakaninsu. A ranar Litinin ne kotun ta yanke hukuncin bayan dage zamanta a ranar 25 ga watan Nuwamba. Sanar da hukuncin ke da wuya, Maryam ta yi ta kuruwa a zauren kotu. A baya ta musanta zargin inda ta ce mijin nata ya…

Karanta...

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Da Wasu Manyan Birnin Gwari

Lamarin ya faru a ɗazu da misalin karfe 12 na rana wasu yan bindiga dauke da muggan makamai suka diro garin na Birnin Gwari inda sukayi garkuwa da Alhaji Yusuf Yahaya Mai Dubu (sarkin kudun birnin gwari) da sakataren ilimi na karamar hukumar birnin gwari Kamar yadda Muryar Yanci ta samu ruhoton yanzu daga birnin gwari, daya daga cikin wanda akayi garkuwan dasu wanda ake kira Alhaji Magaji Umar jagaban birnin gwari ya arce amman haryanzu shima ba a ganshi ba, saidai wata majiyar tace a yanzu haka yana hannun…

Karanta...

Kano: Sanusi Ya Kauce Haɗuwa Da Bayero

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya juya tare da ‘yan rakiyarsa daga shiga harabar Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ana hasashen Sarkin ya ɗauki matakin hakan ne saboda halartar Sabbin Sarakuna daga Masarautun Bichi, Gaya da Rano, wajen bikin yaye dalibai na farko a Jami’ar. Wannan mataki da Sarkin ya ɗauka ya jefa jama’a da yawa cikin mamaki a waje taron. Saboda an ji kade-kaden motarsa da bushe bushen kakaki, amma sai ya juya ya bar filin taron. An samu ra’ayoyi mabanbanta akan matakin da Sarkin…

Karanta...

Kano: Kotu Ta Haramtawa Ganduje Kafa Majalisar Sarakuna

Babbar kotun jihar Kano, karkashin mai Shari’a A. T Badamosi, ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, daga kafa majalisar sarakuna da nada mambobinta. A ranar Litinin ne gwamna Ganduje ya nada sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban sabuwar majalisar sarakunan Kano da ya kafa bayan kirkirar sabuwar dokar masarautu. Kotun ta zartar da hukuncin ne a yayin zamanta a yau Talata. Wannan dai shine karo na biyu da kotu ke dakatar da ganduje daga yunkurin shi na daddatsa Masarautar Kano mai tsohon tarihi.

Karanta...

Sabbin Masarautu: An Sake Maka Ganduje A Kotu

Masu nada sarki a masarautar Kano sun sake Kai gwamnatin jihar Abdullahi Ganduje da majalisar dokokin jihar kara gaban kotu. Suna kalubantar kafa sabuwar dokar kafa Masarautu ta 2019 bayan rushe tsohuwar da kotu tayi. Suna zargin cewa a wannan karon ma ba’a bi doka wajen Samar da masarautun ba, domin kuwa an samar dasu ne duk da umarnin wata kotu da ya hana yin hakan. Tuni kotun ta sanya ranar 17 ga watan nan domin fara sauraron karar.

Karanta...