Kaduna: El Rufa’i Zai Rushe Cocin Da Yafi Dadewa A Arewa

Kungiyar mabiya addinin kirista reshen jihar Kaduna ta bayyana rashin jin dadinta dangane da yunkurin gwamnati na rusa cocin Anglican na Saint Geoges da ke Sabon garin Zaria, wadda aka gina a 1908. An dai ce gwamnati na son rusa cocin ne da manufar fadada wata kasuwa da ke kusa da ita. Shugaban kungiyar, Reverend John Hayab ya bayyana wa BBC cewa an sha yunkurin rusa majami`ar da nufin fadada kasuwar da ke makwabtaka da cocin ana fasawa saboda tarihinta. “Yawancin wadanda suke shugabanci a yanzu ba a haife su…

Read More

Babu Abin Da Gwamnatin Buhari Ta Tsinana Wa ‘Yan Najeriya Sai Talauci – Dr Gumi

Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi ya ce zaben 2019 shi ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya, kasancewar a lokacin ne aka zabi gwamnatin da bata tsinanawa jama’a komi karkashin jagoranci Muhammadu Buhari. Sheikh Gumi ya daura laifin wannan gwamnatin ne a kan manya-manyan ‘yan siyasan kudancin Najeriya, inda ya ce babu abinda gwamnatin Buhari ta yiwa Najeriya in banda jefa mutane cikin talauci. Malamin ya bayyana wannan abu a matsayin ganganci daga bangaren ‘yan siyansan kudancin Najeriya, inda ya ce sun marawa Buhari baya ne a…

Read More

Majalisar Tarayya Za Ta Dakatar Da Dokar CBN

Yunkurin da babbab bankin Nijeriya CBN ya zo da shi na zarar kudin masu ajiya ko kuma masu cira za ta zo karshe. Domin kuwa zauren majalisar Wakilai sun nemi CBN ya dakatar da wannan kudiri. Benjamen Kalu daga jihar Abia shine wanda ya shigar da korafi a gaban majalisa. Bayan shafe dogon lokaci Benjamen yana zabga Turanci, inda yake bayanin nuna rashin gamsuwa da wannan kudi, nan take sauran wadanda suke cikin zauren suka nuna goyon bayansu tare da amincews. Ba tare da bata Lokaci ba, shugaban Majalisar ya…

Read More

Rufe Kan Iyakokin Kasa Alheri Ne – Sarki Sanusi

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana gamsuwarsu a kan shawarar da gwamnatin tarayya ta dauka na rufe iyakokinta da makwabtan kasashe, tare da bayyana hakan a matsayin hanya daya tilo da Najeriya za ta tilasta yin biyayya ga dokokinta na yaki da sumogalin. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin gana wa da manema labarai a fadarsa domin jinjina wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan nada sabbin mambobin kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki (EAC). Sarki Sanusi ya zargi kin biyan gwamnati haraji da wasu…

Read More

Harin Saudiyya: Buhari Ya Yi Allah Wadai

Shugaba Buhari ya ce Gwamnatin tarayyar Nijeriya tana nuna alhininta tare da jajantawa kasar Saudiya bisa harin da aka kai mata a matatar man kasar dake Khurais da Abqaiq. A cikin kalaman nasa, shugaba Buhari yace: “Mu ma a nan Nijeriya mun taba samun irin wannan harin a matatar man mu. Amma insha Allahu kamar yadda ba su yi nasara a baya ba, haka ba za sucyi wata nasara anan gaba ba da yardar Allah. “Koda yake har yanzu ba a san ko su waye suka kai harin da jirgi…

Read More

2019: Gidan Talabijin Na LIBERTY Ya Zama Gwarzon Shekara

Gidan talbijin na TVC dake Jihar ikko (Lagos) ne yai nasarar lashe kyautar Nigeria Media Night Out Award (NMNA) na wannnan shekarar. Inda Liberty TV dake jihar kaduna karkashin jagorancin Dr Ahmed Tijjani Ramalan Yazo na daya a yankin Arewacin Najeriya. An karrama su ne domin jajircewar su wurin kawo ingantattun labarai da ruhotannin fadakar da Al’ummar arewacin Najeriya da Najeriya baki daya. Wannan ba shine Karon farko da liberty 🗽 TV da Radio 📻 ta Fara karban kyaututtukan girmamawa ba, domin kusan duk shekara tunda aka kafa wannnan Kafar…

Read More

Sabuwar Dokar CBN Ga Ajiyar Kudade A Bankuna

Daga yau Laraba bisa umarnin babban bankin Ƙasa wato CBN, bankunan kasuwanci irin su First Bank da GTBank da Zanith Bank da makamantansu za su fara cazar kwastomomin su adadin wani kaso daga cikin kuɗin da za su ajiye ko kuma za su fitar daga asusunsu, matuƙar dai wannan kuɗi ya kai N500,000 (dubu 500) ga kwastoma ɗaya, ko kuma N3,000,000 (miliyan 3) ga kamfanunnuka da manyan ma’aikatu. Yadda tsarin yake, idan kaje da niyyar saka N500,000 a cikin asusun ka dole ne bankin zai cajeka kaso 3 na adadin…

Read More

ECOWAS Ta Bukaci Najeriya Ta Bude Iyakokin Ta

Majalisar zartarwa ta kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ta roki gwamnatin Nijeriya da ta bude iyakokinta da ta rufe. Kakakin majalisar, majalisar Hon. Moustapha Cisse Lo, ya yi wannan kiran ne a taron majalisar zartarwar kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma kashi na biyu da aka yi a Monrovia, Liberia. Ya kara da cewa, rufe iyakokin ya zama barazana ga yarjejeniyar shiga da ficen da ke tsakanin kasashen. Kuma hakan yazo ne a lokacin da Afirka ke bukatar kokarin cire duk wani shinge tsakanin kasashenta. Cisse Lo, ya jawo…

Read More

Sabon Albashi: Gwamnati Ta Kasa Cimma Matsaya

A wani zaman da aka yi tsakanin Wakilan Gwamnatin Tarayya da na Majalisar Tattaunawar Kungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati (JNPSNC), an kasa cimma yarjejeniya a kan yadda za a saisaita tsarin biyan karin albashi. Babban Sakataren JNPSNC na bangaren ma’aikata, Alade Lawal, ya shaida wa manema labarai cewa Kungiyar Kwadago za su je su zauna su yi tunanin mataki na gaba da za su dauka dangane da batun karin mafi kankantar albashi. Ya ce kuma nan ba da dadewa ba za su sanar da ’yan Najeriya halin da ake ciki. “Mun yi…

Read More

Kisan ‘Yan Najeriya: Tawagar Afirka Ta Kudu Sun Iso Najeriya

Tawagar shugaban kasar Africa ta kudu Cyril Ramaphosa ya turo ta iso Nijeriya. Tawagar ta gana da shugaba Buhari a yau a Litinin, 16, Stumba 2019. Ganawar dai an yi ta ne tare da shugaba Buhari da kuma Minista Rauf Agregbesola, da kuma mai bada shawara na musamman ga shugaban kasar Afrika ta kudu. Wannan ganawar ba za ta rasa nasaba da wulakanta ‘yan Nijeriya da kasar Afrika da kudu kecyi ba. Muna kira da babbar murya ga shugaba Buhari, ya tabbatarwa wadannan wakilai na Africa ta kudu cewa idan…

Read More

Shari’ar Zaben 2019: Gaskiyar INEC Ta Fito Fili

Ganin yadda hukuncin Kotun Daukaka Kara ya kasance, inda tun kafin a kai ga korar karar da PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka kai, sai da alkalan biyar su ka fara yin fatali da zargin da Atiku ya yi cewa wai INEC ta tattara bayanan sakamakon zaben 2019 a cikin rumbun na’urar tattara bayanai, wato ‘SERVER’. Alkalan dai dai sun ce Atiku da PDP sun kasa gabatar da kwararan hujjoji da za su gamsar da kotu. Sannan kuma shaidar da suka gabatar ya kasa kawo wata kwakkwarar…

Read More

Biafra: Kanu Zai Jagoranci Inyamurai Majalisar Dinkin Duniya

Nnamdi Zai Jagoranci Tawagar Wakilai Zuwa Zauren Majalisar Dinkin Duniya Dake Ganeva. Shugaban Haramtacciyar kungiyar nan dake kokarin kwatar yanci daga Nijeriya zuwa Biafara, Nnamdi Kanu Zai jagoranci wata tawaga zuwa zauren majalisar dinkin duniya dake Birnin Ganeva na a kasar Switzerland. Sai dai Emma Powerful sakataren yada Labaran kungiyar yace bazasu bayyan jama’a dalilin ziyarar ba. Wato tun lokacinda Nmadi Kanu ya ziyarci zauren kungiyar Tarayyar Turai ta EU, sai ya bayyana cewa ziyararsa ta gaba itace a zauren majalisar dinkin duniya. Wato a ‘yan shekarunnan masu fafutukur kafa…

Read More

Ban Da Niyyar Kara Wa ‘Yan Najeriya Talauci – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta kara wa ‘yan Nijeriya wahala a kan wadda suke ciki ba. Ya yi maganar ne yayin da Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa (TUC), Quadri Olaleye, ya jagoranci wata tawaga zuwa Fadar Aso Rock a yau Alhamis. Buhari ya ce gwamnatinsa ta gwammace ta bi wasu hanyoyi da za su saukaka wahalar da jama’ar Nijeriya ke ciki, ba za ta yarda ta kara wahala a kan wacce ‘yan Nijeriya ke ciki ba. “Game da farashin mai, na yarda da kai cewa akwai bukatar…

Read More

Garkuwa Da Mutane: Pantami Ya Samar Da Mafita

Ministan Sadarwar Nigeria Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu amincewa tare da hadin Kan bangarorin tsaron Nigeria game da yanda za’a magance kidnapping, ya tabbatar da cewa za’a kulle (SIM cards) layukan sadarwa sama da miliyan Tara da dubu dari biyu a fadin Nigeria wadanda basu da cikakkiyar rijista, Dr. Pantami ya kalubalanci layukan sadarwa masu zaman kan su cewa ana amfani dasu wurin sace mutane, yace dole mu kawo karshen wannan al-amarin a duk fadin Nigeria. . Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa idan aka yi kidnapping din…

Read More

Cin Hanci Da Rashawa Ne Silar Wahalar ‘Yan Najeriya – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana dalilan da ya sanya ‘yan Nijeriya suke shan wuya. Inda shugaban kasar ya bayyana rashawa a matsayin daya daga cikin manyan abin da ke sanya miliyoyin ‘yan Nijeriya ke shan wuya a kasarnan. Buhari ya kara da cewa; rashawa a kowanne mataki babban kalubalen ne da yake durkusar da tattalin arzikin Nijeriya tare da kawo cikas ga ci gaban kasar. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara kan tattalin kudi da Makarantar…

Read More