Canjin Kudi: ISWAP Ta Sanar Da Daina Karbar Takardun Naira

Majalisar Shura ta kungiyar yan ta’addan ISWAP ta sanar da cewa ta daina karban kudin Naira daga wajen Manoma da Masuntan dake biyanta haraji saboda shirin sauya fasalin Naira da gwamnatin Najeriya tayi.

Gwamnatin tarayya ta hannun Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, ta yanke shawara sauya fasalin kudin Naira na N200, N500, N1000 kuma za’a daina amfani da tsofafin takardun kudin ranar 31 ga Junairu, 2023.

An ruwaito cewa wannan abu ya tada hankulan ‘yan ta’addan ISWAP dake yankin Tumbus na tafkin Chadi, majiya mai karfi ta laburta cewa yanzu ‘yan ta’addan kudin CFA Franc suke karba domin rage asara.

Majiyoyin sun kara da cewa yan ta’addan sun hana manoma, masunta da masu kiwo shiga tafkin Chadi ta Marte, Abadam, da Gamboru Ngala domin taikata shigo da Naira sansanin yan ta’addan.

Kwamandojin ISWAP masu hakkin karban haraji, Ibn Umar da Malam Ba’ana ne suka kafa wannan sabuwar Doka. Yanzu sun kafa sabbin hanyoyi ta Kamaru (Bulgaram, Cikka, Guma, Maltam, Doron Liman da Ramin Dorina) Yanzu ISAWP ta koma karban CFA Francs 1,500 matsayin kudin harajin wata da take karba hannun mutane.

Labarai Makamanta