Cancantar Takara: Kotu Ta Ayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Atiku

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya ta sa ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022 domin yanke hukunci kan ko Atiku Abubakar, na da damar neman kujerar shugabancin kasa.

Alkalin kotun, mai sharia Inyang Ekwo, shine ya sanar da ranar bayan kammala sauraron kowane bangare.

A kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, wata kungiya ta Nahiyar Afirka, (EMA) ta gurfanar da Atiku, jam’iyyar PDP, hukumar zaɓe INEC, da Antoni Janar na kasa inda ta kalubalanci cewa Atiku ba shi da damar neman kujerar shugaban ƙasar Najeriya kasancewar ba’a Najeriya aka haife shi ba

Labarai Makamanta