Sanannen Mawaƙin finafinan Hausa Ali Isa Jita ya bayyana cewar babban burin da yake dashi a yanzu shi ne jingine waƙa da komawa tilawar Kur’ani.
Mawaƙin ya bayyana wannan aniyar tasa ne a tattaunawar da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin daga bakin mai Ita.
Ali Jita ya ƙara da cewar dukkanin wata nasara da Mawaƙin zamani ke nema a ƙasar Hausa Allah ya bashi, bisa ga haka yana matuƙar godiya da fatan sauya Alƙiblar rayuwa a nan gaba.
Sai dai jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin su kan furucin na Ali Jita, inda wasu ke yi mishi addu’a da fatan cikar burin nasa, yayin da wasu ke ganin shaci fadi kawai ya yi a kalaman nasa.
You must log in to post a comment.