Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wata baƙuwar cuta da ta ɓulla a Jihar Delta da ke kudancin ƙasar.
Rahotanni na cewa a makon da ya gabata wani ɗalibi ya mutu tare da kwantar da wasu tara a asibiti sakamakon cutar a yankin Boji-Boji na Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa-maso-Gabas.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, NCDC ta ce tana sane da wata cuta da aka ce ta ɓarke tsakanin ɗaliban sakandare.
NCDC ta ƙara da cewa tana haɗa hannu da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Delta.
You must log in to post a comment.