Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi Jamhuriyar Nijar domin halartar taron ƙolin ƙasashen Afika da kuma ƙaddamar da littafi.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya ce shugaban Buhari zai bar ƙasar yau Alhamis domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Afirka kan bunƙasa masana’antu da tattalin arziki.
Gabanin fara taron ƙolin shugaba Buhari zai halarci taron ƙaddamar da littafin – da Farfesa John Paden na jami’ar George Mason da ke Amurka – mai taken Muhammdu Buhari: ‘The Challenges of Leadership in Nigeria’.
You must log in to post a comment.