Buhari Zai Ziyarci Kasar Ruwanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth na ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a ƙasar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a.

Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka da Turai da kuma yankin Pacific.

Labarai Makamanta