Buhari Zai Ziyarci Kasar Faransa A Yau Lahadi

Rahotanni daga Fadar Shugaban kasa Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari a yau Lahadi, 16 ga watan Mayu zai tashi daga Abuja zuwa Paris, Faransa, domin ziyarar aiki ta kwanaki hudu a halartar taron Kasashen Afirka da zai gudana a can.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Asabar, 15 ga watan Mayu, wacce aka sanya a shafin Twitter ta nuna cewa taron zai mayar da hankali ne kan nazarin tattalin arzikin Afirka, biyo bayan firgita daga annobar COVID-19.

Za a duba yiwuwar samun sauki, musamman daga karin nauyin bashi da ke kan kasashe, a wajen taron, da kuma lalubo hanyar warware matsalolin da ke addabar kasashen nahiyar Afirka.

Taron wanda Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai karbi bakuncinsa zai jawo hankalin manyan masu ruwa da tsaki a cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da wasu Shugabannin Gwamnati, wadanda za su hada kai, su tattauna batun samar da kudade daga waje da kuma bashi ga Afirka, da kuma sake fasalin kamfanoni masu zaman kansu.

Matsalar tsaro da za’a tattauna A yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai gana da Shugaba Macron don tattauna barazanar tsaro da ke ci gaba a yankin Sahel da Tafkin Chadi. Zai kuma tattauna kan alakar siyasa, alakar tattalin arziki, canjin yanayi da hadin gwiwa wajen siyan bangaren kiwon lafiya, musamman wajen duba yaduwar COVID-19, tare da karin bincike da allurar rigakafi.

Kafin dawowarsa Najeriya, Shugaba Buhari zai tarbi wasu manyan masu fada a ji a harkar mai da iskar gas, injiniyanci da sadarwa, Majalisar Tarayyar Turai da Wakilin Tarayyar Turai kan Manufofin Tsaro, da cigaban ‘yan Najeriya.

Shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ministan kasuwanci da zuba jari, Otunba Adeniyi Adebayo, da kuma ministan lafiya, Dr E. Osagie Ehanire.

Har ila yau, a cikin ziyarar akwai mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Mohammed Monguno (rtd) da kuma babban darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar.

Labarai Makamanta