Buhari Zai Ziyarci Amurka Yau Lahadi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi taro kasar Amurka yau Lahadi.

Buhari zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 77 da za a gudanar a birnin New York na ƙasar ta Amurka.

A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya ce shugaban zai gabatar da jawabi a ranar Laraba a taron da shugabannin kasashen duniya za su halarta.

Labarai Makamanta