Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu ta fitar da sabuwar tantebur ɗin kamfen, wadda a ciki aka tabbatar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai taya shi kamfen aƙalla a jihohi 10.
Festus Kiyamo ne ya fitar da wannan sanarwar tare da sa mata hannu a ranar Juma’a.
Keyamo ya ce Buhari zai ɗaga wa talakawa tsintsiya a ranar 9 Ga Janairu a Adamawa, 10 ga Janairu a Yobe, 16 Ga Janairu a Sokoto, sai kuma Kwara a 17 Ga Janairu. Ogun kuma a ranar 17 Ga Janairu.
Keyamo ya ƙara da cewa Buhari zai halarci kamfen a Kuros Riba, a ranar 30 Ga Janairu, Nasarawa a ranar 4 Ga Fabrairu, Katsina a 6 ga Fabrairu, sai Imo a ranar 14 Ga Fabrairu.
Haka kuma Buhari zai halarci kamfen ɗin TInubu na ƙarshe a ranar 18 Ga Fabrairu a Legas.
Tun da Buhari ya halarci ƙaddamar da kamfen ɗin TInubu a ranar 15 Ga Nuwamba, 2022 a Jos bai ƙara fita kamfen ɗin TInubu ba.
Hakan ya sa an riƙa nuna damuwa cewa Buhari bai damu da Tinubu ya ci zaɓe ko ya faɗi zaɓe ba.
“Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu/Shettima na murna ganin Shugaba Muhammadu Buhari zai ƙara mata ƙwarin-guiwar fitowa ya taya ta kamfen a jihohi 10. Wannan kuma zai ƙara wa kamfen ɗin karsashi sisai.
“Mu na kira ga ɗaukacin magoya bayan APC su riƙa fitowa ƙwai da kwarkwata wurin yaƙin neman zaɓe.
Yayin da wasu ke jinjina wa irin namijin ƙoƙarin da Tinubu ya yi domin ganin Buhari ya yi nasara a zaɓen 2015, ana kallon cewa a yanzu shi Buhari bai nuna masa irin haka ba.
You must log in to post a comment.