Buhari Zai Sayar Da Manyan Kadarorin Gwamnati 36

Gwamnatin Nijeriya na shirin sayar da kimanin manyan kadarorin gwamnati kusan 36 don samun kudin da za ta tunkari kasafin shekarar nan ta2021. Jaridar Premium Times wace ta sanar da mallakar takardun da gwamnati ta rubuta wannan kuduri nata ta ce ana shirin sayar da kadadorin ko kuma bayar da su aro domin cike gibin da za a iya samu a wurin aiwatar da kasafin kudin wannan shekara.

Kadarorin gwamnati da ake shirin cefanarwa ko kuma bayar d aro sun hada da bangaren lantarki kamar hukumar TCN da banagren sadarwa inda aka tsara cefanar da hukumar tace fina-fina ta Nigerian Film Corporation sai kuma wasu matatun man fetur da gwamnatin ba ta bayyana sunansu ba.

An mika wannan bukata ga zauren majalisa domin bada damar cefanar da kadarorin kuma babban buri shi ne .domin gwamnatin Nijeriya ta samu kudaden da za’a aiwatar da kasafin shekarar 2021 na tiriliyan N13.58 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu a karshen shekarar da ta gabata.

Labarai Makamanta