Buhari Zai Jagoranci Shugabannin Afirka Taron ECOWAS Yau A Abuja

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai jagoranci shugabannin Afirka taron ECOWAS yau Lahadi a Abuja.

Taron da za a yi na shugabannin ƙasashen shi ne na 60 kuma ana yin irin wannan taron a duk shekara.

Ana sa ran tattaunawa kan batun siyasa da tsaro da tattalin arziƙin ƙasashen.

Haka kuma ana sa ran tattaunawa kan halin da ƙasashen Mali da Guinea suke ciki.

Labarai Makamanta