Buhari Zai Halarci Taro Kasar Saudiyya Yau Litinin

Rahotanni daga fadar Shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Saudiyya yau Litinin domin halartar wani taron zuba jari a birnin Riyadh.

Fadar shugaban cikin wata sanarwa ta ce Buhari zai halarci babban taron na kwana uku wanda zai ƙunshi manyan ƴan kasuwa daga Najeriya da manyan masa’antu da masana makamashi domin tattauna batutuwa da suka shafi makomar saka jari a duniya.

Bayan kammala taron shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gudanar da aikin Umrah kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a, a cewar sanarwar.

Shugaban zai tafi tare da rakiyar jami’an gwamnatinsa da suka haɗa da ministan sadarwa Dr. Isa Ibrahim Pantami da ƙaramin ministan harkokin waje Ambasada Zubairu Dada da ministan man fetur Timipre Sylva da kuma mai ba shugaban shawara kan harakokin tsaro Janar Babagana Monguno.

Sauran ƴan kasuwa daga Najeriya da za su halarci taron sun haɗa da Alhaji Mohammed Indimi da Alhaji Aliko Dangote daTope Shonubi da Wale Tinubu da Alhaji Abdulsamad Rabiu da Hassan Usman da Omoboyode Olusanya da Abubakar Suleiman da Herbert Wigwe da kuma Leo Stan Ekeh.

Labarai Makamanta