Buhari Zai Halarci Taro Kasar Habasha Yau Alhamis

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari a ranar yau Alhamis zai ziyarci Addis Ababa, babbar birnin kasar Ethiopia domin halartan taron gangamin gamayyar kasashen Afrika na 35.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya fitar a yammacin Laraba.

Bayan taron, shugaba Buhari zai zauna da wasu shugabannin kasashe kan ganin yadda za’a bunkasa huldar kasuwanci, karfafa tsaro, da sauransu.

Adesina yace Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan Noma, Mohammed Abubakar; da Ministar tallafi da jin kai, Sadiya Farouq.

Sauran sun hada da mai bada shawara kan harkokin tsaro Maj. Gen. Babagana Monguno da Shugaban hukumar NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.

Labarai Makamanta