Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudi A Yau Juma’a


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wannan Juma’ar ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kudirin kasafin kudin kasar na baɗi, wanda aka kiyasta zai kai naira tiriliyan goma sha tara.

Kasafin kuɗin dai yana da giɓin da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin kasafin kudin.

Ƴan majalisun dokokin kasa wato da majalisar dattawa da ta wakilai za su yi zama ne na haɗin gwiwa don bai wa Shugaba Buharin damar gabatar musu da kudirin kasafin na baɗi, wanda shi ne kasafin kuɗi na ƙarshe da zai gabatar a matsayinsa na shugaban Najeriya.

An dai ƙiyasta cewa a kasafin kuɗin na fiye da tiriliyan 19, za a samu giɓi na fiye da naira tiriliyan goma sha biyu, wanda sai gwamnati ta hada rance da sayar da waɗansu kadarorin kafin ta cike shi.Wasu labaran da za ku so karantawa

Kazalika akwai batun tallafin mai, wanda shi ma ƙarin dawainiya ne ga kasafin haka kuma zai iya janyo zazzafar  muhawara, kasancewar wasu goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba da tallafin, yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya kamata a dakatar, saboda a nasu ra’ayin masu hada-hadar man sun fi talaka cin gajiyar tallafin.

Sai dai ƴan majalisar da dama na da ra’ayin cewa akwai bukatar a jira a ga gangariyar abin da kasafin kudin ya kunsa.

Honarabul  Jafar Sulaiman Ribadu, ɗan majalisar wakilai ne daga jihar Adamawa wanda ke cewa zai so su karbi kudirin kasafin kudin badin da zuciya daya inda ya ce yana fata duk wani ɗan Najeriya zai mori kasafin kuɗin 2023.

Kasafin wannan shekara mai karewa ya kai naira tiriliyon goma sha bakwai da doriya wanda hakan ke nufin na badi ya ɗara shi da naira tiriliyan biyu da ɗoriya.

Sai dai Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya tabbatar da cewa an samu cikas wurin aiwatar da kasafin kuɗin bana a wasu ɓangarorin saboda rashin samun isassun kuɗin da za a aiwatar da shi.

Sai dai ya ce ana sa ran kafin ƙarshen shekara za a samu shigowar wasu kuɗin da za a ci gaba da ayyuka.

A Najeriyar dai za a iya cewa zumuɗi da ɗokin sauraron kasafin kuɗin shekara-shekarar ya ragu a tsakanin al`ummar kasar da dama, sakamakon yanke ƙaunar da wasu ke yi suna zargin cewa sau da yawa faɗa ne kawai ba cikawa!

Labarai Makamanta