Buhari Zai Ciyo Bashin Biliyan 82 Na Sayen Ragar Gidan Sauro

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Shugaban ƙasa Buhari zata ciyo bashin bilyan 82 don sayen ragar kariya da cizon sauro a shekarar 2022.

Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar gaban majalisar dokokin tarayya kwanakin baya. Sai dai anasu bangaren ‘Yan majalisar sun ce gaskiya ba zasu yarda da wannan abu ba, dole sai an sake dubawa.

Majalisar dattawar Najeriya ta yi Alla-wadai da shirin da ma’aikatar kiwon lafiyan Najeriya ke yi na karban bashin $200 million (N82,070,388,916.76) a kasafin kudin shekarar 2022.

Ma’aikatar za ta yi amfani da wannan bashi ne wajen sayawa yan Najeriya ragar kariya daga cizon sauro, Sakaraten din-din-din na ma’aikatar ya bayyanawa kwamitin a taron bayani kan kudin da ma’aikatar ta bukata cikin kasafin kudin 2022.

Labarai Makamanta