Buhari Ya Zama Kadangaren Bakin Tulu Ga ‘Yan Arewa – Matasan Arewa

An bayyana salon mulkin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin wani tarnaki wanda ya zama wa ‘yan Arewa Ƙadangaren bakin tulu, a tsige shi ya zama matsala a barshi kuma Arewa ta cigaba da fuskantar tasku.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin Shugabannin Ƙungiyar Matasan Arewacin Najeriya Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna.

Shugaban Matasan yana mayar da martani ne dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta yi ga Majalisa na ta tsige Buhari sakamakon gazawarshi wajen samar da tsaro a Najeriya.

“Tabbas batun da kungiyar Dattawan suka yi ƙarkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta bakin sakataren kungiyar Dr. Hakeem Baba Ahmed gaskiya ne, Buhari ya gaza ta kowane fanni, amma batun a tsige shi a yanzu mu a matakin matasa ba ma goyon bayan haka, abin da muke magana shine Buhari ya farka ya dage wajen cika alkawarrun da ya yi kafin karewar lokaci”.

“Mu abin da muke buƙata shine bayan kammala wa’adin mulkin Buhari ya zamana wanda zai gaje shi Ɗan Arewa ne, domin fitar da Arewa daga cikin halin kuncin da take ciki”.

Dangane da batun harin da ‘yan bindiga suka kai fadar shugaban kasa kuwa Kwamared Kamal Funtuwa ya bayyana cewar bai yi mamakin faruwar hakan ba ta la’akari da yadda aka samu kai hare hare a wasu cibiyoyin tsaro waɗanda suka haɗa da babban Barikin Soji dake gari Jaji Jihar Kaduna, da kwashe daliban kwalejin koyon dabarun noma da gandun daji dake Kaduna wanda ke makwabtaka da sansanin sojin sama dake Kaduna, wannan bai zama abin mamaki ba hari fadar Shugaban ƙasa, sannan a hannun guda wani cigaba ne da zai ankarar da gwamnati fahimtar halin rashin tsaro da ‘yan Najeriya ke ciki.

Labarai Makamanta