Buhari Ya Yi Watsi Da Jama’ata – Gwamnan Neja

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya tuhumci gwamnatin tarayya da yin watsi da su wajen yunkurin da sukeyi na ceto daliban makarantar GSC Kagara da lyan bindiga suka sace.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne yayin karban bakuncin mai tsawatarwa a majalisar Dattawa Sanata Orji Uzor Kalu, a gidan gwamnatin jihar dake Minna ranar Alhamis.

Ya ce gaba daya gwamnatin Buhari ta rabu da shi yayi fama da matsalar shi kadai. Ya ce duk da cewa gwamnatin tarayya ta turo wakilai yi masa jaje tare da tura jami’an yan sanda 300 jihar, Bello ya ce gwamnatinsa bata samu komai na kudi daga wajen gwamnatin tarayya ba.

“Ina taimakon yake? A yanzu babu wani taimako daga wajen gwamnatin tarayya tun lokacin da wannan abun ya faru. Duk da cewa an turo tawaga don jajanta mana, amma an bar mu da matsalarmu,”.

“Zamu yi amfani da duk wata dama da dukiya da muke da shi wajen tabbatar da cewa mun ceto yaran nan. Bamu da takamamman ranan dawowansu amma ina da tabbacin hakan zai faru nan ba da dadewa ba.”

Labarai Makamanta