Buhari Ya Yi Tir Da Sace Ɗaliban Jihar Neja

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma’aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata da wasu ‘yan Bindiga suka yi.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba da yammaci.

A cewar shugaban, ya samu labarin faruwar lamarin kai harin ‘yan ta’adda da ya auku cikin dare, wanda har ya zuwa yanzu ba a gano adadin ma’aikata da daliban da aka sace ba.

Shugaban ya kuma kara da cewa ya tura jami’an ‘yan sanda da sojoji don tabbatar da an ceto wadanda aka sacen. Hakazalika ya tura wasu daga cikin tawagar ministocinsa zuwa jihar ta Neja don tabbatar da cewa an ceto wadanda aka sacen, tare da ganawa da jami’an jihar, shugabannin al’umma, iyayen yaran da abin ya shafa da kuma iyalan ma’aikatan makarantar.

Shugaban yace: “Ina jajantawa iyalai da iyayen wadanda lamarin ya faru dasu. “Na bada umarnin tura sojoji da ‘yan sanda don ceto daliban da ma’aikatan makarantar da aka sace.” ya kara da cewa.

A ci gaba da jawabinsa, shugaba Muhammadu Buhari ya tausasa zukatan iyalan wadanda aka sacen da cewa, “Addu’o’inmu suna tare da dangin wadanda harin ya rutsa da su.” A karshe ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta dauki mataki akan lamarin, sannan zata ci gaba da kokari don gwagwarmayar yaki da ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta