Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto

Shugaban Kasa Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga iyayen ɗalibar kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto wanda ajali ya iske ta bayan an zarge ta da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.

Buhari ya ce doka ba ta ba wani damar yanke hukunci kai tsaye ba. komai na da hurumin sa.

Idan an yi laifi sai kuma a bari waɗanda hukunci ke hannunsu su yanke shi ba kowa ya yi gaban kansa ba.

A sakon da ya fitar wanda kakakin shugaban ya saka wa hannu Garba Shehu, Buhari ya yabawa wa gaggawar ɗaukar mataki da gwamnatin Sokoto ta ɗauka a lokacin da abin ya auku.

” Babu wanda yake da damar yanke hukunci ko ɗaukar doka a hannun sa a kasar nan. Tashin hankali ba zai haifar da ɗa nai ido ba.

Labarai Makamanta