Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Daliban Jami’a A Kaduna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi tir da Allah wadai da kisan uku daga cikin ɗaliban da aka sace a Jami’ar Greenfield a Jihar Kaduna.

“Tunanina yana tare da iyalansu a wannan lokacin na jimami. Allah Ya jiƙansu, ”in ji Shugaban cikin sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.

Shugaban ya la’anci yawaitar kashe –kashe da sace-sacen mutane a Kaduna, wanda ya kira “munanan hare-haren ta’addanci.”

Shugaban ya kuma bayyana takaici yana mai cewa “abin baƙin ciki ne yadda wasu shugabannin siyasa da na addini ke ƙara rura wuta da ƙara zafin ƙunci ga iyalan mamatan da ke zaman makoki.”

“Wannan bala’in na buƙatar nuna tausayi da kuma haɗin kai a matsayinmu na al’umma don tunkarar waɗannan ƙalubale da kuma barazana ga dimokuraɗiyyarmu da zaman lafiyar kasa,” in ji shugaban.

Shugaban ya ce ” Najeriya za ta yi amfani da duk ƙarfinta domin yaƙar ƴan fashi da masu satar mutane da kuma siyasar kashe-kashe.”

Labarai Makamanta