Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban Ć™asa Muhammadu Buhari ya yi tir gami da Allah wadai da kisan da ‘yan Bindiga suka yi wa matafiya a jihar Sokoto ta hanyar cinna wa motarsu wuta.
Da yake maida martani akan Iftila’in da ya faru, shugaba Buhari a ranar Laraba ya bayyana harin a matsayin hari na rashin imani da keta wanda ko da wasa gwamnati ba za ta amince da hakan ba.
Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan harkokin yaÉ—a labarai Femi Adesina ya fitar yau Laraba, inda ya yi rantsuwar É—aukar matakan da suka dace akai.
“I extend deep condolences to the families of the victims as I assure that the security agencies will continue to give their all to bring to an end the operations of these despicable
“Ina mika ta’aziyyata ga iyalan waÉ—anda Iftila’in ya faÉ—a musu, sannan ina basu tabbacin jami’an tsaro za su yi dukkanin mai yiwuwa wajen gamawa da wanda suka yi wannan ta’asa
You must log in to post a comment.