Buhari Ya Yi Tankade Da Rairaya A Kasafin Kudin Shekarar Bana

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da wasu karin ayyuka 6,576 da Majalisar Dokokin ƙasar ta ƙara a kasafin kudin 2022.

Shugaban ya ce sanya ayyukan da kuɗinsu ya haura Naira biliyan 36 ya saɓa wa dokar cin gashin kai da kowanne ɓangaren zartarwa ke da shi.

Shugaban wanda ya bayyana hakan yayin sanya wa kasafin hannu a fadarsa da ke Abuja, ya ce zai sake mayar wa ƴan majalisar don su duba gyare-gyaren da ya yi.

Sai dai shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya kafe a kan cewa babu kuskure a abun da suka yi, yana cewa dama ba lallai ne a ce a ko da yaushe ra’ayin ɓangarorin biyu ya zo ɗaya ba.

Labarai Makamanta